Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yanke wa jagoran ƙungiyar Ansaru a Najeriya hukuncin ɗaurin shekara 15
A ranar Alhamis ɗin nan wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke wa Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Ansaru guda biyu da aka gurfanar a gaban kuliya, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15.
Alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite ta nemi jami'an DSS su tsare Mahmud Usman a wurinsu kafin a kammala yanke masa hukunci kan ragowar tuhume-tuhume 31 da ake yi masa shi da Abubakar Abba wanda shugaban ma'aikatansa ne.
Ana dai tuhumar kwamandojin biyu ne da laifuka 32 masu alaƙa da ayyukan ta'addanci a 2022, bayan kai hari a barikin soji na Wawa Cantonement a Kainji da ke jihar Neja.
Tuhume-tuhume
- Daga cikin tuhume-tuhumen 32 da ake yi wa kwamandojin ƙungiyar, akwai zargin samun horon sanin dabarun ƙirƙira da amfani da abubuwan fashewa daga ƙungiyoyin ta'adda.
- Ana kuma tuhumar su da samun horo kan dabarun yaƙi daga wata ƙungiyar ƴan ta'adda a ƙasar Mali.
- Hukumar DSS ta zargi kwamandojin biyu da kitsa harin da aka kai gidan yarin Kuje a 2022 wanda ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni fiye da 600.
- Har wayau, ana tuhumar mutanen biyu da aikata wasu laifuka da suka haɗa da yin garkuwa da Alhaji Musa Umar Uba da Magajin Garin Daura a 2019 da sauran ayyukan fashi da makami.
Yadda aka kama su
A ranar 16 ga watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta ce jami'an tsaronta sun samu nasarar kama wasu gawurtattun ƴanta'adda, ƴan tsagin ƙungiyar Ansaru da take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022, har wasu fursunoni suka tsare.
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa da ke Abuja inda ya ce ƴanta'addan biyu na cikin waɗanda suke nema ruwa a jallo.
"A yau ina farin ciki sanar da ku cewa mun samu gagaruwamr nasara a yaƙin da muke yi da ta'addanci ta hanyar amfani da bayanan sirri, inda muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru masu alaƙa da Al-Qaeda a Najeriya." In ji wata sanarwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa sun samu nasarar ce a wasu samame da suka yi a tsakanin watan Mayu da Yulin bana, inda ya ce "muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru waɗanda suka kitsa kai wasu manyan hare-hare a Najeriya a shekarun baya."
Su wane ne kwamandojin Ansaru?
Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara'a ko Abbas ko Mukhtar, ya kasance Amir na ƙungiyar Ansaru, da kuma Mahmud al-Nigeri wanda aka fi sani da Mallam Mamuda, wanda shi ne shugaban ma'aikatan Abu Bara'a kuma mataimakinsa, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribaɗu ta bayyana.
Mamuda ya samu horo ne a ƙasar Libya a tsakanin 2013 zuwa 2015 a ƙarƙashin wasu ƴanbindiga daga ƙasashen Masar da Tunisia da Aljeriya da suka ƙware wajen amfani makamai da nakiyoyi.
Daga cikin manyan hare-haren da suka kitsa, kamar yadda Nuhu Ribadu ya bayyana akwai harin gidan yarin Kuje da aka yi a shekarar 2022 da hari a wajen haƙar ma'adinin uranium na Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa.
A ranar 1 ga watan Janairun 2012 ne ƙungiyar ta Ansaru ta ɓalle daga ƙungiyar Boko Haram kuma bayan nan ne gwamnatin Najeriya da ta Amurka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya suka haramta ƙungiyar.