Munanan hare-hare shida da aka kai Nijar bayan juyin mulkin soji

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

A ranar Laraba ne ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adama ta Human Rights Watch, ta ce ƴanbindiga sun kashe sama da mutum 127, ciki har da mazauna ƙauyuka da Musulmai masu ibada a aƙalla hare-hare biyar a yammacin Tillabéri na Nijar.

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Laraba, Human Rights Watch ta zargi ƙungiyar IS-Sahel da kai hare-haren, ciki har da ƙone gomman gidaje da satar dukiya da dama.

Rahoton na ƙungiyar ya nuna cewa an samu ƙaruwar hare-haren kan fararen hula a Nijar tun daga watan Maris ɗin 2025, tana mai cewa hare-haren sun saɓa wa dokokin jinƙai na duniya kuma ana ganin laifukan yaƙi ne.

Human Rights Watch ta zargi hukumomin mulkin sojin Nijar da gaza kare fararen hula yadda ya kamata.

Haka ma ƙungiyar ta ce sojoji ba su mayar da martani kan gargaɗin da ake yi musu ba, inda ta zarge su da watsi da buƙatun mazauna ƙauyuka don samun kariya.

Kawo yanzu dai hukumomin Nijar ba su mayar da martani kan rahoton Human Rights Watch ba tukuna.

A wannan maƙala mun duba wasu munanan hare-hare shida da aka samu tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar a watan Yulin shekara ta 2023.

Harin yankin Tahoua

A farkon watan Oktoban 2023 wasu mayaƙa masu iƙirarin jihaɗi suka ƙaddamar da wani mummunan hari a yankin Tahoua tare da kashe aƙalla sojojin ƙasar 29.

Maharan sun yi amfani da abubuwan fashewa da motocin yaƙin, kamar yada ma'aikatar tsaron ƙasar ta bayyana a lokacin harin.

Ma'aikatar tsaron ta kuma dakarunta sun samu nasarar kashe gomman mayaƙan a lokacin harin wanda ya auku a kusa da kan iyakar ƙasar da Mali.

Harin Banibangou

A ranar 19 ga watan Yunin 2025 wasu mahara fiye da 200 a kan babura suka kai wani mummunan hari kan wani sansanin soji da ke Banibangou kusa da kan iyakar ƙasar da Mali.

Harin ya yi sanadin mutuwar sojojin ƙasar 34, kamar yadda ma'aikatar tsaron ƙasar ta bayyana a lokacin harin.

Maharan - waɗanda ma'aikatar tsaron ƙasar ta bayyana da ''sojojin haya'' - sun kuma jikkata sojoji 14 a garin na Banibangou - da ke kan iyakar ƙasashen Mali da Burkina Faso.

Yankin ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan ƙungiyoyin mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

Ma'aikatar tsaron ta ce dakarun ƙasar kashe gomman mayaƙan a lokacin harin.

Harin Manda

Haka ma a ranar 24 ga watan Yuni wasu mahara masu iƙirarin jihadi suka kai wani mummunan hari a garin Manda da ke yankin Tillebri a kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Bayanai sun ce maharan ɗauke da muggan makamai sun far wa garin tare da buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sannan suka rika cinna wa gidaje wuta.

A lokacin harin mayaƙan sun kashe aƙalla mutum 71 da ke sallah a cikin wani masallaci a yankin.

Harin Fombita

A ranar 21 ga watan Maris ɗin 2025, wasu mayaƙa masu masu alaka da ƙungiyar al Qaeda sun kai wani mummanan hari a ƙauyen Fombita tare da kashe fararen hula 44.

An kai harin ne a yankin Kokorou - da ya yi ƙaurin suna wajen zama sansanin mayaƙan jihadi a Nijar.

An kai harin ne a lokacin da mutanen ke tsaka da sallar azahar inda aka raunata mutum 13.

Harin Tera

Haka kuma a ranar 5 ga watan Disamban 2024, wasu mahara ɗauke da makamai a kan babura suka ƙaddamar da hari kan garin Tera mai nisa kilomita 175 daga Yamai, babban birnin ƙasar.

A lokacin harin fararen hula aƙalla 21 ne suka mutu, kamar yadda sojojin ƙasar suka bayyana.

Garin Tera na kusa da kan iyakar Nijar da Burkina Faso, yakin da ya yi ƙaurin suna wajen hare-haren masu iƙirarin jihadi.

Harin Eknewan

Haka ma a cikin watan Mayun 2025 wasu mahara suka ƙaddamar da harin kwanton- ɓauna kan wani jerin gwanon sojoji da ke tafiya a garin Eknewan a kusa da kan iyakar Mali.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji masu yawan gaske, kamar yadda rahotonni suka nuna a lokacin.

A lokacin harin sojoji da dama ne suka jikkata a mutu a harin da ake ganin ɗaya daga munanan hare-hare kan sojojin ƙasar.

Me ya sa aka kasa magance hare-haren mayaƙa?

A lokacin da sojojin suka karɓe mulkin ƙasar a 2023, ɗaya daga cikin dalilan da suka bayar shi ne gwamnatin farar hula ta gaza magance matsalar hare-haren masu tayar da ƙayar baya.

Wani abu da ya sa mutane ke mamakin yadda ake samun ƙaruwar munanan hare-haren masu iƙirarin jihadi a ƙarƙashin mulkin sojojin.

To sai dai Dakta Abba Sadiq, mazaunin birnin Paris da ke sharhi kan hare-haren ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi a yankin Sahel ya ce ta'addanci abu ne mai wuyar sha'anin kawo ƙarshensa.

Ya ce akwai abubuwa da dama game da ta'addanci da masu bincike suka ganowa, sannan "ba lallai da ƙarfin bidiga za a iya magance matsalar ba,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

  • Taulauci

Ya ce wani babban abin da ke ƙara ingiza wannan matsala shi ne talauci.

''Akwai matasa masu yawa da waɗannan ƴan ta'adda ke yaudarar su ta hanyar ba su kuɗi domin janyo hankalinsu wajen shiga irin waɗannan ƙungiyoyi'', in ji shi.

Ya ce muddin ba a kawar da talaucin da ke damun al'umma ba to za a daɗe ba a shawo kan ayyukan masu tayar da ƙayar baya a ƙasashen Sahel ba.

  • Rashin abubuwan more rayuwa

Masanin tsaron ya ƙara da cewa rashin aikin yi da abubuwan more rayuwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara tunzura matasa shiga wannan ayyukan ƙungiyoyin masu kai hare-hare.

"A lokuta da dama maharan kan yi amfani da rashin kyawun tituna wajen ƙaddamar da hare-harensu a yankunan karkara ta yadda sojoji ba za su iya kai ɗauki a kan lokaci ba, saboda rashin kyawun tituna".

  • Amfani da ƙarfin soji kaɗai

Dakta Sadiq ya ce wani abu da ya ƙara ingiza matsalar shi ne yadda gwamnatin mulkin sojin ta dogara da ƙarfin soji kaɗai wajen magance matsalar tsaro.

''Ita matsalar ta'addanci ba kodayaushe ne ƙarfin soji da bindiga zai yi maganinsa ba, akwai lokutan da kake buƙatar wasu hanyoyin da ba na soji ba, kamar sulhu ko tattaunawa'', in ji shi.

Me ya kamata a yi don magance matsalar?

Dakta Abba Sadiq ya ce abin da ya kamata a yi shi ne gwamnatin mulkin sojin Nijar ta samar wa matasan ƙasar ayyukan yi, domin kauce wa yaudarar da ƙungiyoyin ke yi musu.

''Gwamanti ta ɓullo da wasu tsare-tsaren sama wa matasa ayyukan yi ta yadda za su dogara da kansu su kuma yaƙi talauci tsakaninsu'', in ji shi.

Masanin tsaro ya kuma ce wani da ya kamata gwamnatin mulkin sojin ta yi shi ne ta samu haɗin kan ƙasashe makwabta domin yaƙi da masu iƙirarin jihadin.

''A lokuta da dama maharan kan ƙaddamar da hare-harensu ne kan iyakokin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Benin da kuma Najeriya a wasu lokuta, don haka yana da kyau gwamnati ta haɗa kai da duka waɗannan ƙasashe domin lalubo hanyoyin magance matsalar'', in ji Dakta Abba Sadiq.

Haka kuma masanin tsaron ya ce wani abu da ya kamata a yi shi ne al'umma su bayar da tasu gundumawar, wajen bai wa gwamnati bayanan sirri.

''Matsalar tsaro ba ta gwamnati kaɗai ba ce, matsala ce da ta shafi kowa, don haka ya kamata jama'a, kowa ya bayar da haɗin kai wajen bai wa jami'an tsaro bayanan sirri kan ayyukan ƴanbindigar'', in ji shi.