Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bikin tunawa da sarkin da ya kafa masarauta cikin hotunan Afirka
Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.
A ranar Asabar mutane suka taru a birnin Bulawayo na Zimbabwe domin bikin tunawa da Sarki Mzilikazi, wanda ya kafa masarautar Ndebele.
Wani mutum riƙe da lema, yayin da yake tafiya cikin ruwa a Dakar babban birnin Senegal.
Ƙwararren mai zanen Zimbabwe wanda ya lashe lambar yabo, Gresham Tapiwa Nyaude ya tsaya kusa da ɗaya daga cikin zanen da ya yi a wajen baje kolin fasahar zane, a Afirka ta kudu ranar Juma'a.
DJ Zinhle ta Afirka ta Kudu yayin da ta halarci makon baje kolin kayan ado a birnin New York a ranar Talata...
Josias Musasa daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya yi nasara a kan Otari Tanzilovi na Georgia a faɗan da suka yi a Amurka ranar Talata.
Achta Toko Njoya ta Kamaru tana murna da ƴan wasan tawagarta bayan ta zura ƙwallo a wasan da suka yi da Australia a gasar cin kofin duniya ta mata ƴan ƙasa da shekara 20 a Columbia, ranar Juma'a.
Ƴan wasan ƙwaikwayon Senegal, Anna Diakhere Thiandoum da Ibrahima Mbaye lokacin da suka halarci bikin baje kolin fina-finai a Deauville, a ranar Lahadi.
Yankan dabino a garin Badrashin na ƙasar Masar.
Ruwa ya malale gidaje a birnin Maiduguri da ke arewacin Najeriya bayan ambaliyar da ta fasa madatsar ruwa ta Alau.
Mutane 170 ambaliyar ruwa ta kashe a sassan ƙasar cikin makonnin nan, kuma ta tilastawa dubbai barin muhallin su.