Matsanancin laulayi mai jefa masu juna biyu cikin haɗari

Wata mace mai juna biyu a zaune

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Ƙwararru na cewa waɗanan matsalolin laulayi na daban ne da kan zama ƙalubale musamman idan an zo gwajinsu inda alamomin kan yi kama da waɗanda ake samu ga duk mai juna biyu
    • Marubuci, Jelilat Olawale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Ina ta adu'a ga wannan juna biyu amma fa a ƙasan marata ina jin damuwar da nake jin na matsu in haife shi".

Lokacin da Christabel Ngwube wadda 'yar ƙasar Kanada ce 'yar shekara 30 ta samu juna biyu, murna har kunne tana ta yi wa jinjirin fata da adu'a, mma fa daga baya lamarin ya sauya zuwa damuwa.

A cikin 'yan makonni da samun juna biyun lamarin sai ya juya daga na farin ciki zuwa fama da lafiyar jikinta.

Sannu a hankali Christabel ta soma fama da lauyayi inda ta ke jin jiri wani sa'in ta kan yi amai ba ƙaƙƙautawa. Duk da ƙamshin abinci ta ji sai ta yi rashin lafiya. Nan take ta soma fargabar duk da ɗan ruwa kaɗan ta kurɓa sai ya takaro mata yin amai mai yawa.

Alamomin da take ji sun wuce irin waɗanda mai juna biyu ke fama da su idan ta faraka da safe - irin waɗannan akan fara jin su daga makonni 14, lokacin da ƙwayoyon halitta kamar chorionic gonadotropin (hCG) da estrogen suka ƙaru a jiki.

Bayan an yi mata gwaji ne aka gano tana fama da irin wannan shu'umin laulayi na hyperemesis gravidarum (HG) rashin lafiya mai tsananin da mai juna biyu kan yi fama da ita har tsawo makonin goyon ciki 39 ɗin nan da ake yi, akan rasa wadataccen ruwa da kuma ƙarancin abinci a jiki.

Hoton Gimbiya Catherine Middleton, ta Wales tana fara'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Catherine Gimbiyar Wales ma ta taɓa fama da irin wannan laulayin

Wannan irin laulayi da ake kira HG da jimawa ya ke jan hankalin jama'a, ciki kuwa har da Catherine Gimbiyar Wales, da ta bayar da labarin yadda ta yi fama da shi a dukan juna biyu har uku da ta taɓa samu.

An yi ƙiyasin cewa a ƙasar Burtaniya a duk cikin masu juna biyu 100 yana shafar aƙalla daga mace ɗaya zuwa uku kamar yadda Cibiyar Kiyyon Lafiya ta Ƙasa (NHS) ta bayyana.

Har ila yau, masana sun yi imanin cewa ba a cika fito da bayanin matsalar a sarari ba, abin da ya sa aka kasa gane tasirin da ta ke shi a duniya.

"Na yi fama da yunwa da rashin lafiya ina ji ina gani ba zan iya cin abinci ba," in Christable. "Kusan ko ruwa ma ba ni iya sha saboda ina jin tsoron kada in yi amai"

Ta ce damuwar da ta shafi tunani da lafiyar ƙwaƙwalwarta, har ma a ke ganin kamar kowa ya fita lamarinta.

Hoton wata mata mai juna biyu

Asalin hoton, Christabel

Bayanan hoto, HG kan kai har tsawo makonin goyon ciki 39 ɗin nan da ake yi, ya kan haddasa rasa wadataccen ruwan jiki da kuma ƙarancin abinci a jiki.

Ƙalubalen gwajin laulayin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A sassan duniya da dama, ƙarancin samun cibiyoyin kiyyon lafiya na nufin ana iya samun lokuta da yawa akan kasa yin gwajin wannan laulayi kasancewar ba a san shi ba. Wasu matan na fama tsangwama mai alaƙa da al'ada, inda ake ganin mace ta nuna damuwa game da laulayin a matsayin kasawa ko kuma raki.

Tafiyar dubban milamilai daga Abuja a Najeriya wata mata da ta samu juna biyu a karon farko Nenye ita ma ta ke kan fama da wannan laulauyin mai tsanani da aka gano.

A yanzu tana yawan amai da ganin jiri ga rashin wadataccen ruwan jiki, da yawan zuwa asibiti saboda yin ƙorafi. Hakan dai ya sa tilas aka dinga yi mata ƙarin ruwan jiki.

"Ban taɓa jin labarin wannan laulayi da ake kira hyperemesis gravidarum sai fa a yanzu, " in ji Nenye.

Kamar dai sauran iyaye da suka yi haihuwar farko, ita ma ba ta san kome game da laulayi ba da ma abubuwan da ke faruwa da ita ba, duk kuwa da cewa lafiyarta na ci gaba da taɓaɓarewa amma dai ta mayar da hankali wajen ganin likitoci.

"Likitan ya soma da nuna cewa wai 'masassarar safiya ce kawai'," kamar yadda ta tuna yadda ya faɗa mata.

Amma ita Nenye ta san yadda ta ke ji a jikinta bya saɓa na al'ada. Har cikin ya kai wata biyar ba ta daina yin matsanancin amai ba. Ta ce sai fa da ta fara yin aman jini sannan ne tawagar likitoci su ɗauki mataki

Masana dai sun yi bayanin cewa gano irin wannan cuta da kan shige cikin lalulayin mai goyon ciki wani babban ƙalubale ne, domin idan aka je gwaji sai ta yi kama da irin laulayi mai sauƙi da aka saba da shi, kamar yadda Dakta Nkiruka Uche-Nwidagu likitan sashen masu haihuwa na Cibiyar da ke yaƙi da cututuka ta Ebonyi.

Dakta Adeniyi Akiseku, ƙwararren likitan haihuwa kuma mai bayar da horo akan kiyon lafiya a Cibiyar Binciken Halittu ta PBR a Landan, ya ce laulayin HG yana iya shafar lafiyar jinjirin da ke ciki.

"Idan ba a kula da matsalar uwar a kan lokaci ba, shi ma jinjirin na iya kamuwa, domin zai iya rasa abincin mai gina jiki da zai haddasa rashin girman jiki da nauyin jinjirin, da fama da matsalar ciyon ciki wani sa'in ma da yin ɓarin sa."

Hoton wata mata sanye da bakar riga

Asalin hoton, Nenye

Bayanan hoto, Nenye ta dinga jin damuwa har zuwa lokacin da ta haihu a dalilin tasirin laulayin HG

Ko ana gadon laulayin HG?

Har yanzu dai binciken da ake kan gudanarwa bai kai ga tabbatar da cewa ko akwai alaƙa tsakanin irin wannan laulayi na HG matsalolin mace kan samu a yayin naƙuda ba. Har wayau Dakta Marlena Fejzo, wani mai bincike a Jami'ar Kudancin Kalifoniya, ya ce akwai hujja mai ƙarfi cewa wannan laulauyin yana da nasaba da gado na halitta.

Dakta Fejzo ya ƙara da cewa matan da ke fama da wannan laulayi na hyperemesis gravidarum (HG) suna samu wasu irin ƙwayoyin halitta da yawa nau'in GDF15 a lokacin da suka ɗauke da juna biyu - wannan nau'in ƙwayar halittar kan taimaka wajen rage kumburin jiki da sarrafa sinadaran ginin jiki da taimakawa halittun jiki girma.

"Mun gano cewa wannan sauyi na matakin ƙwayoyin halittar jiki na haddasa bijirewar garkuwar jiki ta ƙaru, abin da ke sa aukuwar hakan.

Matakan magani

Mace mai juna biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba a gano alaƙa tsakanin laulayin HG da matsaloli da ake samu a yayin naƙuda ba

Akwai magungunnan da ake ba ai juna biyu ciki har wanda ake bayarwa daga sati na 12, da kan taimaka wajen raguwar laulayin. Daga ciki akwai na zazzaɓi (anti-emetic) ƙwayoyin steriod da ke rage kumburi, ko duka biyun.

Haka kuma, idan aka kasa tsayar da amai, to akwai buƙatar zuwa asibiti a ba mace na son kulawar gaggawa saboda tana iya rasa ruwan jiki, da akan yi ƙarin sa ta jijiya.

Ƙwararru a fannin lafiya sun sahidawa BBC cewa akwai buƙatar ba maras lafiyar kulawa domin taimaka mata rage tsananinsa.

A cewar Dakta Akiseku, ba su kulawa game da lafiyar ƙwaƙwalwa da tunaninsu yana da muhimmanci, saboda dogon tasirin da HG kan yi a tunani har zuwa bayan mace ta haihu, kuma hakan kan haifar da damuwa da baƙin ciki.

Nenye ta ce ta jure hakan tsawon watanni tana fama da damuwa har zuwa lokacin da ta haifu ma ba ta rabu da jin tasirin da laulayin na HG ya haddasa mata ba.

Galibi ma akan nemi yin ƙarin wasu magungunna da matakai daga - ciki har da bayar da shawarwari - watakila taiakawa mace da hanyoyin da za ta ci gaba da ɗauka domin samun sauƙin damuwar.

Dakta Uche-Nwidagu ya nanata cewa akwai buƙatar yawaita faɗakarwa domin sau da dama ba a san cewa mata na fama da wannan matsala a ɓoye ba.

Ɗaukar mataki akan lokaci na da muhimmanci wajen magance yanayin da kuma kare faɗawa haɗari ga lafiyar uwa da jaririnta - ba rage tsananin ciyo kawai ba har da ceton rai.