DR Congo da Rwanda sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya

CONGO RWANDA

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Rwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun sanya kan wata yarjejeniya da za ta sa ƙasashen su mutumta ƴancin junansu, da kuma fitar da tsarin zaman lafiya tsakaninsu nan da mako ɗaya.

Ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Washinton na Amurka, ƙarƙashin jagorancin sakataren harkokin wajen Amurkan Marco Rubio.

An tilastawa dubban fararen hula barin muhallinsu a watannin nan bayan ƙungiyar M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta ƙwace yankin gabashin Congo mai albarkatun ƙasa.

Bayan iko da yankin ya ƙwace mata, yanzu Kinshasha ta mayar da hankali ga Amurka domin neman mafita da ƙulla alaƙar kasuwanci.

Alaƙa ta yi tsami sosai tsakanin Congo da Rwanda, ta yadda wasu ke Kallon taron da ministocin harkokin wajen ƙasashen suka yi a matsayin wani abin a yaba, wanda zai iya kawo mafita.

Amma duk da tattaunawar tasu, ana ci gaba da gwabza yaƙi a yankin yankin Kivu da ke arewaci.

A farkon makon nan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da mayaƙan M23 sun ce a shirye suke su amince da shirin zaman lafiya da fatan kawo ƙarshen rikicin.

Hukumomi a Congo sun ce mutane dubu bakwai aka kashe tun bayan fara rikicin a watan Janairu.

Rikicin da aka shafe sheakaru da dama ana yi ya yi ƙamari a farkon shekarar nan inda mayaƙan M23 suka afkawa birnin Goma da Bukavu, birane mafi girma a gabashin Congo, lamarin da ya jefa tsoro a tsakanin mazauna yankin.

DR Congo ta zargi Rwanda da tallafawa mayaƙan M23 da makamai da kuma dakaru.

Duk da goyon bayan wannan zargi daga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, Rwanda ta musanta cewa tana tallafawa M23.