Kongo ta yi watsi da tattaunawa da M23 duk da ƙaruwar matsin lamba

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Anne Soy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Africa correspondent, BBC News, Nairobi
- Lokacin karatu: Minti 3
Duk da irin ƙaruwar matsin lamba daga ƙasashen waje, Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta ci gaba da zama kan matsayarta ta ƙin tattaunawa da ƙungiyar ƴan tawayen M23 kai-tsaye, waɗanda suka danna zuwa gabashin ƙasar a baya-bayan nan.
A makon da ya gabata, gwamnatin Birtaniya ta ƙara yin kira ga ƙungiyar da ta shiga cikin "tattauanwar gabaki-ɗaya" don taimakawa wajen laluɓo hanyar warware rikicin.
Sai dai a wata tattauanwa da BBC, Firaiministar Kongo Judith Suminwa Tuluka ta ce gwamnatinta na son tattaunawa da makwabtansu Rwanda, wadda ta zarga da mara wa M23.
Aƙalla mutum 8,500 aka kashe tun bayan ɓarkewar faɗa a watan Janairu, a cewar hukumomin Kongo.
An tilasta wa dubun-dubatar mutane barin gidajensu yayin da rikicin ya ƙara kamari, wadda masana daga Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma wasu ke kallon Rwanda a matsayin wadda take da muhimmin rawa a ciki.
"Maganar gaskiya ita ce Rwanda na da laifi a shiga yankin Jamhuriyar Kongo," in ji Suminwa Tuluka, inda ta bayyana rahoton MDD a bara wanda ya ce sojojin Rwanda 3,000 zuwa 4,000 sun tsallaka zuwa yankin ƙasar Kongo - kuma muna faɗa tare da M23.
Tattaunawar zaman lafiya da Angola ke jagoranta bai cimma wata matsaya ba a watan Disamba bayan da Rwanda ta nemi cewa gwamnatin Kongo ta tattauna kai-tsaye da M23.

Asalin hoton, EPA
Ta yi maraba da takunkuman da Amurka ta kakaba wa ministan gwamnatin Rwanda James Kabarebe, inda ta ce hakan zai taimaka wajen "matsa wa masu kai farmaki".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai Rwanda ta yi watsi da su, inda ta kwatanta takunkuman da cewa ba za su taimaka wajen warware rikicin ba.
A nata ɓangaren, hukumar Tarayyar Turai ta dakatar da "tattaunawa kan tsaro" da kuma jingine yarjejeniya da suka cimma da Rwanda kan kayayyaki a bara.
Firaiminstar Kongon ta yi na'am da matakin hukumar ta Tarayyar Turai, inda ta ce "satar albarkatun ƙasa - na ɗaya daga cikin abin da ya haddasa rikicin".
Kongo ta zargi Rwanda da satar albarkatun ƙasarta a gabashin ƙasar, abin da Rwanda ta musanta.
A makon da ya gabata Birtaniya ta ce za ta ɗauki matakin dakatar da agajin da take bai wa Rwanda amma ban da kuɗin tallafawa matalauta da kuma ƙungiyoyi marasa galihu, har sai ta janye dakarunta da shiga tattaunawar zaman lafiya da kuma amincewa da tsagaita wuta.
Rwanda ta kwatanta matakin da horo, inda ta ce ba shi da ma'ana a yi sa ran ta sadaukar da tsaron ƙasarta.
Firaiministar Kongon ta ce Rwanda ta yi kunnen shegu game da kiraye-kirayen janye dakarunta.
"Don haka, waye yake kawo cikas a tattaunawar samo mafita? ba gwamnatin Kongo ba ce," in ji ta.
A baya Rwanda ta amince da batun tura sojojinta zuwa Kongo don "ba da kariya da kuma farmaki" yayin faɗan da ake gwabzawa, inda suke iƙirarin kare yankunan ƙasarsu.
Ta kuma sha zargin gwamnatin Kongo da aiki da kuma bai wa ƙungiyar mayaƙa ta Democratic Forces for the Liberation of Rwanda (FDLR) mafaka, waɗanda mambobinsu suka kunshi mayaƙa daga kisan kare dangi na 1994.
Da aka tambaye ta game da hakan, Suminwa Tuluka ta musanta cewa sojojin Kongo na aiki da ƴan tawayen FDLR, sai dai ta ce ƙasarta za ta duba yiwuwar kakkaɓe ƴan tawayen.
Idan aka zo ga batun abin da zai warware matsalar idan aka yi watsi da buƙatar tattaunawa kai-tsaye da M23, firaiministar ta ce tare da tattaunawa da Rwanda, abu mai sauki ne zai kawo tsagaita wuta.
"Tabbatar da ficewar sojojin Rwanda daga Kongo sannan M23 su daina kashe al'ummar Kongo," in ji ta.











