Kongo: Ƙasa mai ɗimbin arziƙi wadda talauci ya yi wa katutu
Kongo: Ƙasa mai ɗimbin arziƙi wadda talauci ya yi wa katutu
Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ƙasa ce mai ƙunshe da ɗimbin albarkatun ƙasa masu tsada a ƙarƙashinta, waɗanda ake amfani da su wajen haɗa wayoyin salula da kuma motoci masu amfani da lantarki.
Sai dai duk da irin wannan arziƙi da take da shi, ƙasar ta kasance cikin mafiya talauci kuma mafi fama da rikice-rikice a fadin duniya.



