Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya

Kafofin sada zumunta

Ma`abota rubutu da wallafe-wallafe da ke goyon bayan jam`iyya ko `yan siyasa a Najeriya, wadanda aka fi sani da `yan "soshiyal midiya" na kara karfi a siyasar kasar.

A halin da ake ciki sun kai matsayin da ana damawa da su a kusan kowanne matakin gwamnati da rukunin `yan siyasa.

‘Yan soshiyal midiya a Najeriya na da karfin gaske kasancewar suna taka muhimmiyar rawa wajen daukaka jam`iyya ko dan siyasa.

Kuma su ma abubuwan da suke yi na kusanta su ga `yan siyasa, suna kuma samun rufin asiri daga harkar.

To sai dai kuma ana zargin wasu daga cikinsu da zama `yan kore ko karnukan farauta, wadanda ake amfani da su wajen kazafi ko aibunta abokan hamayyar siyasa.

Wannan dama da `yan soshiyal midiya ke samu ta ciccibawa da tura `yan siyasa zuwa kololuwar daukaka ko akasi ta sa ana kaffa-kaffa da su.

 Dr Kabiru Danladi Lawanti, masanin aikin jarida a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaida wa BBC cewa ana tsoron ‘yan soshiyal midiya saboda mutane ne wadanda suna da karfin gaske musamman idan suka fara yada abubuwa wadanda ake gani kamar nakasu ne daga dan siyasa, to wannan sai ya hana dan siyasar tasiri.

Ya ce haka kuma idan suna kaunar mutum suka fara yada manufofinsu masu kyau, ko ba a sonsa, sai kaga daga baya an zo ana sonsa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A halin yanzu dai `yan soshiyal midiya sun kasance tamkar sojojin baka ne, wadanda ke kokarin shan gaban `yan jarida ba don rashin kwarewa na yi musu cikas ba.

 Kuma ana dai zargin mafi yawan `yan soshiyal midiyan da zama `yan kanzagin `yan siyasa, saboda rashin akida.

Dr Ashir Tukur Inuwa, malami a sashen nazari da koyar da aikin jarida na jami`ar Bayero ta Kano, ya ce yawancin ‘yan soshiyal midiya basu da kwarewa ko horo na aikin jarida, da ka su kan tari abin shi ya sa ake yawan samun labaran karya da na batanci.

To amma Mallam Rabi`u Biyora, bai musanta ba, amma ya ce ba a taru aka zama daya ba.

Ya ce "Maganar cewa ana amfani da ‘yan soshiyal midiya a matsayin karnukan farauta da zage-zage da cin mutunci duk ana yin wadannan abubuwan, to amma ba duka aka taru aka zama Daya ba.”

Mallam Rabi`u Biyora, ya ce "Duk kaunar da nake yi wa siyasa ko wani dan siyasa bai isa ya sa na zagi ko aibata wani ba.”

 Wata kididdiga da aka yi a bara, ta nuna cewa ana da akalla kungiyoyin `yan soshiyal midiya fiye da dubu ashirin da bakwai a Najeriya.

Kuma a yanzu ma sai abin da ya karu kasancewar an fara shiga kakar zabe a Najeriya.