Zaben 2023: Abu biyar da Buhari ya gaya wa gwamnonin APC kan zaben fitar da gwani na shugaban kasa

Asalin hoton, Presidency
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci dukkan gwamnonin jihohin ƙasar na APC da su tabbatar da cewa sun nuna kyawawan ɗabi'u da manufofin jam'iyyar a lokacin zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da za a gudanar a makon gobe.
Shugaban ƙasar ya faɗi hakan ne a yayin wata ganawa da ya yi da gwamnonin 22, da kuma shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu a ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai, Femi Adesina, ya fitar bayan ganawar Buhari ya yi magana ne a kan muhimman abubuwa biyar:
Haɗin kan ƴan jam'iyya
Shugaba Buhari ya yi magana a kan zaɓukan da ke tafe na 2023 da kuma nuna muhimmancin haɗin kan ƴaƴan jam'iyyar APC a wannan lokaci na zaɓukan fitar da gwani.
"Tsare-tsaren zaɓukan 2023 sun kankama gadan-gadan, kuma na fahimci cewa jam'iyyun siyasar da suka fi nasara a faɗin duniya a ko yaushe suna dogara ne kan haɗin kan cikin gida da shugabanci na gari don samun manyan nasarori.
"Jam'iyyarmu ta APC ba za ta bambanta da sauran da suka yi nasara ba, har yanzu muna ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren samar da ƙasa mai albarka," in ji shi.
Shekarar ƙarshe ta mulki

Asalin hoton, Presidency
Shugaban ya yi magana a kan shekararsa ta ƙarshe a matsayin shugaban Najeriya.
"A yayin da na shiga shekarata ta ƙarshe a karo na biyu a matsayin shugaban ƙasar Najeriya, na fahimci muhimmancin buƙatar da ke akwai ta na samar da shugabanci mai ƙarfi a ƙarƙashin wannan sauyin mulkin, don tabbatar da cewa an yi komai cikin tsari.
"Irin wannan shugabanci shi ake buƙata don jam'iyyar ta cigaba da zama mai ƙarfi kuma dunƙulalliya.
"Sannan shi ake buƙata don bunƙasa ribar dimokuraɗiyya wajen tabbatar da cewa jam'iyyar ta ci gaba da samun iko da ƙasar, da samun yawan ƴan majalisun dokoki da kuma yawan jihohi," a cewar Buhari.
Zaɓen fitar da gwani

Asalin hoton, Presidency
Abu na uku da shugaban ya yi magana a kai shi ne zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC da ke tafe.
Ya ce: "Nan da ƴan kwanaki, jam'iyyar za ta yi zaɓen fitar da gwani inda za a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar.
"Wannan wani abu ne mai muhimmanci kuma sakamakon zaɓen zai tabbatar wa duniya irin ingancin APC wajen tabbatar da tsare-tsaren dimokuraɗiyya, da ala'ada da kuma shugabanci.
Kira ga gwamnoni

Asalin hoton, Presidency
Shugaban ya yi kira ga gwamnoni su sanya bukatun jam'iyyar a gaba, da yunkurinmu na kawo sauyi a dakkan yanayinmu, da kuma abin da yan kasarmu da kasashen duniya suke sa rai su gani daga wajenmu.
Dole ne manufarmu ta kasance samun nasara ga jam'iyyarmu, kuma dole dan takarar da za mu zaba ya zama ya zama wanda zai bai wa talakawan Najeriya fatan samun nasara da karfin gwiwa tun ma gabanin zabe.
Ci gaba da tuntuɓa
Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa za a ci gaba da tuntuba don tabbatar da cewa duka 'yan takara da masu ruwa da tsaki suna da ta cewa har zuwa lokacin babban taro, yana jaddada cewa za a ringa magance damuwar da za ta ringa tasowa saboda wasu dalilai, ta yadda APC za ta kara zama mai karfi.
Da yake magana a madadin gwamnonin, gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ya ce dole ne jam'iyyar ta ɗora a kan nasarorin da ta samu lokacin zaben shugabanninta da aka yi a baya bayannan da kuma zabukan fitar da gwani da aka gudanar kawo yanzu, abin da ya sa aka samu yan takara da za su bi sawun kishin kasa da shugaban kasa ya nuna.











