Makahon ango da ke shaukin ganin amaryarsa

Ango da Amarya

Asalin hoton, SAIFULLAH MUKHTAR

"Babban abin radadi a gare ni shi ne ba ni da ido da zan kalli matar da na aura a baya bayan-nan, sannan ko da 'yan uwana da mahaifinmu ya haifa a baya na, su ma ban san yadda kamar su take ba duk da cewa muna tare a kullum.”

Saifullah Mukhtar ya gamu da larurar makanta shekara 17 da suka gabata a lokacin da yake dan shekara 16 bayan ya samu matsala a idanunsa yayin da yake zuwa makarantar sakandare a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Cutar makantar dai, ba ta hana Saifullah damar kammala karatunsa na Jami'a ba a Jami'ar Bayero, kuma bayan nan ne ya samu aiki a hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya.

“Da farko, kamar duk wani da iftila'i ya faru da shi, na dauka cewa karshen rayuwata ne ya zo, mun yi duk mai yiwuwa domin samun lafiya amma komai ya ci tura,” in ji shi.

“Sai lokacin da ni da iyayena muka je wurin wani likitan ido a India, sannan yake fada wa mahaifana cewa ba zan sake gani ba, a lokacin ne muka hakura, sannan na yanke shawarar amfani da rayuwata yadda ya kamata ta hanyar daukar karatu da muhimmanci.”

“Na kammala karatun Digiri a Jami'ar Bayero, kuma ban bata lokaci ba na wuce domin yin Digiri na biyu, inda a baya bayan nan na samu aiki a hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya. Wani abin farin ciki ma shi ne na doke har da mutane masu gani da suka nemi aikin a jarrabawar da muka yi.

“Shawarata ga masu lalurar rashin gani irina ita ce, kar su yanke kauna ga rayuwa, na san cewa akwai radadi idan aka ce mutum ba ya gani amma mutane da dama na cikin matsanancin hali da ya fi wannan, je asibiti za ka ga mutane masu lalura ta laka ko kuma mahaukata.”

'Yan Najeriya miliyan 50 na fama da lalurar ido'

Ango

Asalin hoton, SAIFULLAH MUKHTAR

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kungiyar Likitocin idanu ta Najeriya ta gudanar da taronta na shekara-shekara a Abuja, ranar Laraba 13 ga watan Yuli, 2022, inda shugaban kungiyar, Dr Obinna Awiaka ya ce kusan 'yan Najeriya miliyan 50 na fama da lalurar ido.

Ya kara da cewa akwai makafi da suka kai miliyan 300 a duniya, inda Najeriya ke da mutum miliyan bakwai daga cikin alkaluman.

“A Duniya, kusan kashi 40 na mutane na fama da matsala ta idanu yayin da Najeriya ke da mutum miliyan 50,” a cewar likitan.

Dr Sadiq Hassan, shugaban sashin kula da masu lalura a idanu a asibitin Malam Aminu Kano, ya fada wa BBC cewa 'yan Najeriya miliyan 50 na fama da lalura ta idanu saboda karuwar mutane masu zuwa duba idanunsu a asibitin.

Likitan ya ce babban abin da ke janyo matsalar rashin gani ba a Najeriya kadai ba har ma a duniya shi ne yanar ido.

Mene ne maganin yanar ido?

Dr Sadiq ya ce hanyoyi da mutane za su bi wajen kare kansu daga kamuwa da yanar ido su ne kula da lafiya a ko da yaushe. Sannan a kuma kula da wasu kananan cutuka da za su iya ta'azzara matsalar.

“Alal misali , cutar yanar idon kan iya tsananta kan mutane da ke da cutar sikari, adon haka muddin mutum ya kula da irin wadannan cutuka, to zai iya kare kansa daga kamuwa da yanar ido.”

Likitan ya kara da cewa wasu na kamuwa da yanar ido ne saboda yawan shekarun su kamar daga shekara 50 ya yi sama yayin da ake haifar wasu kuma da ita.

Daga karshe, Dr Sadiq ya ce hanyar magance cutar a yanzu ita ce yi wa mai lalurar aiki a idanu saboda masana kimiyya na ci gaba da yin bincike don samo magani da masu lalurar zasu yi amfani da shi.