Abubuwan da dokar tilasta gwajin lafiya kafin aure a Kano ta ƙunsa

Majalisar dokokin jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta amince da kudurin dokar tilasta yin gwaji kafin a yi aure a jihar.
Dan majalisar jihar ta Kano mai wakiltar Takai Dakta Musa Ali Kachako, shi ne ya gabatar da wannan ƙuduri a zauren majalisar wanda aka tafka muhawara a kai kafin a kai ga amincewa da shi.
Ya kuma shaida wa BBC cewa lallai ne jama'a sun yi maraba da wannan ƙudiri a bisa yadda suka riƙa samun martani da rahotanni daga jama'ar jihar.
''Wannan ƙuduri na yi masa kallo na tsanaki kafin in fitar da shi, kuma mun gudanar da dogon bincike a kansa saboda muhimmancinsa kafin a kai ga amincewa da shi,'' in ji dan majalisar.
Ya kuma kara da cewa, ƙuduri ne da yake so ya tsarkake, kana ya taimaka wa tsarin auratayya saboda irin cututtukan da suke yanzu a duniya.
Ya ce: ''Misali uku daga cikin manyan cututtukan da suka addabi duniya ba wai a jihar Kano ko Najeriya ko kuma Afirka kadai ba, cututtuka ne wadanda kuma suna da hanyar matakan da za a iya kare su.''
''Cututtuka ne masu yaduwa, cututtuka ne da daya ta hanyar jima'i ake samu, yayin da kuma daya ake gado ta hanyar jinni da sauransu,'' ya ce.
Hon Kachako ya kuma ce da farko ƙudurin ya yi kallo a matsayin jihar Kano, da yawanta, da muhimmancin al'ummarta, da kuma addini da al'ada. Don haka ƙudurin ya kalli abin da Musulunci ya tanadar, abin da al'ada ta tanadar, da kuma abin da zamantakewa ta tanadar.
Saboda haka ya ce idan an yi wannan doka za ta wajabta cewa a duk lokacin da za a yi aure sai an dauki wannan mataki na yin gwaje-gwaje sannan a samu takardar shaidar da ta tabbatar da cewa daga hannun ƙwararrun likitoci suke na bincike domin a yi auren ba tare da cutarwa ba.
''Mataki ne da idan an yi shi zai taimaka wa lafiyar al'umma, zai takaita yaduwar cututtuka a tsakanin al'umma, zai taimaka wa ƴaƴanmu su tashi cikin koshin lafiya, da yaduwar irin wadannan cututtuka, kamar cutar kanjamau, da cutar hanta da kuma cutar amosanin jini ko sikila,'' kamar yadda ya ce.
Nan da dan lokaci kankani ne dai ake sa ran 'yan majalisar za su gabatar da ƙudurin a gaban gwamnatin jihar Kanon domin ya zama doka.
Tuni dama wasu jihohin kamar Jigawa mai makwabtaka da jihar Kanon da kuma wasu wuraren a jihar ta Kanon suka yi nisa wajen irin wadannan gwaje-gwaje kafin a yi auren.











