Real Madrid ta ɗauki Joselu daga Espanyol

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta ɗauki aron Joselu daga Espanyol zuwa ƙarshen kakar da za a fara, da yarjejeniyar za ta saye shi matuƙar ya taka rawar gani.
Joselu, mai shekara 33, shi ne na uku a yawan cin ƙwallaye a La Ligar da aka kammala.
Ya jefa ƙwallo 16 a raga, amma duk da haka ƙungiyarsa ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Tsohon ɗan wasan kulob ɗin Stoke City da Newcastle United, ya ci wa Sifaniya ƙwallo a Gasar Nations League da ƙasar ta lashe kofin ranar Lahadi a Netherlands.
Real ta ɗauki ɗan wasan ne, bayan Karim Benzema ya bar Santiago Bernabeu a ƙarshen kakar nan zuwa Al-Ittihad ta Saudiyya.
Kenan Real tana neman wanda zai maye gurbin gwarzon ɗan wasan wanda ya ci Ballon d'Or ta bana, inda ya zama na biyu a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye a tarihi, bayan Cristiano Ronaldo.
Ana kuma alaƙanta ɗan wasan na tawagar Ingila da Tottenham, Harry Kane a matakin wanda zai maye gurbin Benzema a Real Madrid.
Joselu ya koma Sifaniya don taka leda a 2010, inda ya fara tamaula daga ƙaramar ƙungiyar Real Madrid.
Ya fara taka leda a Almeria a 2011, kuma ya ci ƙwallo, bayan ya shiga wasan daga baya.
Tun bayan barin Real a 2012, ɗan wasan tawagar Sifaniya ya buga gasar Bundesliga da ta Premier League.
Ya ci ƙwallo 10 a wasannin da ya yi a Stoke City da Newcastle daga nan ya sake koma wa Sifaniya zuwa ƙungiyar Alaves.











