Abubuwan da kotun zaɓen Najeriya ta cimma a farkon zaman shari'o'i kan Tinubu

Asalin hoton, Court of Appeal/Twitter
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zaman da ta fara, zuwa ranar Talata, don ci gaba da zaman share fage a kan ƙorafe-ƙorafe game da nasarar Bola Ahmed Tinubu.
Alƙalan kotun, sun tsara sauraron ƙorafe-ƙorafe daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar a gobe Talata, da kuma korafin jam'iyyar APM da 'yar takararta.
Sai kuma washe gari jam'iyyar Labour da ɗan takararta, Peter Obi su gabatar da nasu ƙorafe-ƙorafe a ranar Laraba.
Haka zalika, kotun ta musamman za ta saurari ƙorafin jam'iyyar APP da ɗan takararta Simon Nnadi a ranar, game da zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.
Bayan kaddamar da zaman kotun ranar Litinin, alkalan kotun biyar sun fara yanke hukunci a kan korafin farko, wato na jam’iyyar AA da dan takararta na shugaban kasa Solomon David Okanigbuan, wadanda suka sanar da kotun game da aniyarsu ta janye korafin.
Alƙalin da ya jagoranci zaman, Mai shari'a Haruna Simon Tsammani ya ce korar ƙorafin na AA, ya dace da tanade-tanaden kundin dokar zaɓe na 2022.
Tun da farko, lauyoyi guda biyu ne, Oba Maduabuchi da Malachy Nwaekpe suka je gaban kotu, kowannensu na iƙirarin bayyana a madadin jam'iyyar AA.

Asalin hoton, BBC PIDGIN
Jam'iyyar dai ta shiga zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu ne cikin ɓaraka, inda ɗan takararta, Solomon David Okonigbuan ya shigar da ƙorafi a kan hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar APC mai mulki da ɗan takararta, Bola Ahmed Tinubu da kuma Hamza Al Mustapha, yana ƙalubalantar cire sunansa a takardar zaɓe.
Haka zalika, Action Alliance (AA) ta kuma tsayar da Hamza Al Mustapha a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasarta, kuma shi ne hukumar zaɓe ta wallafa sunansa a takardar zaɓe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin zaman farko a ranar Litinin, kotun sauraron kararrakin zaben karkashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani ta bai wa kowanne bangare tabbacin yin adalci a zaman da za ta yi.
Sauran rukunin alkalan akwai Mai shari'a Stephen Adah da Mai shari'a Misitura Bolaji-Yusuf da Mai shari'a Boloukuoromo Moses Ugo da kuma Mai shari'a Abbah Mohammed.
Kotun ta fara zaman sauraron ƙararraki a kan nasarar Bola Ahmed Tinubu ne mako uku daidai kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Masu ƙorafi huɗu ciki har da manyan 'yan adawan ƙasar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar Labour, kowannensu yana iƙirarin shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 25 ga watan Fabrairun 2023.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen bisa hujjar cewa jam'iyyarsa ta APC ce ta samu ƙuri'u mafi rinjaye da aka kaɗa.
Ya dai samu adadin ƙuri'a 8,794,726, inda ya kayar da 'yan takara 17, cikinsu har da babban abokin fafatawarsa daga jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda ya samu ƙuri'a 6,984,520 da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour da ƙuri'a 6,101,533.
Sai dai, ɓangaren zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Tinubu, yana da'awar cewa an yi zaɓen gaskiya da adalci don haka yana neman a kori ƙorafe-ƙorafen.
Dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ya halarci zaman share fage na kotun sauraron kararrakin zaben a Abuja.
Shi ma Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, kuma shugaban rusasshen kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu ya halarci kotun a ranar Litinin.
An jibge dumbin jami’an ‘yan sanda a hanyoyin shiga da kuma wajen harabar kotun.











