Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An zaɓi Ranil Wickremesinghe a matsayin sabon firaministan Sri Lanka
'Yan majalisar dokokin Sri Lanka sun zaɓi firaminista Ranil Wickremesinghe a matsayin sabon shugaban kasar, duk da rashin amincewar jama'a.
Mista Wickremesinghe na fuskantar aikin jagorantar kasar daga durkushewar tattalin arziki da kuma maido da zaman lafiya bayan shafe tsawon watanni ana zanga-zanga.
Ya doke babban abokin hamayyarsa Dullus Alahapperuma wanda ya samu ƙuri’u 82 a kacal.
A makon da ya gabata ne tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar.
Yanzu haka yana neman mafaka a Maldives da Singapore bayan dubban masu zanga-zanga sun mamaye gidansa da wasu gine-ginen gwamnati, suna masu kira da ya yi murabus.
Sun kuma yi kira da Mista Wickremesinghe ya yi murabus bayan nada shi firaminista a watan Mayu.
Masu zanga-zangar sun kona gidansa na kashin kansa sannan kuma sun mamaye ofishin firaministansa da ke Colombo a zanga-zangar adawa da shugabancinsa.
Sri Lanka ta yi fama da talauci sosai, kuma tana fuskantar matsanancin karancin abinci, da man fetur da sauran kayan masarufi.
Bayan zabensa, Mista Wickremesinghe ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa "al'ummar kasar na cikin wani mawuyacin hali" inda ya kara da cewa akwai "manyan kalubale a gaba".
Yana da burin maido da kwanciyar hankali a siyasance ta yadda kasar za ta iya dawo da tattaunawa da asusun lamuni na duniya IMF domin samun tallafin ƙwatar kai.
Sabon shugaban kasar, mai shekaru 73, ya kuma yi kira ga abokan hamayyarsa na siyasa da su yi aiki tare da gwamnatinsa domin amfanin kasar.
Mista Wickremesinghe ya shafe shekaru 45 yana siyasa a kasar Sri Lanka, ya taba tsayawa takarar shugabancin kasar sau biyu, sannan ya zama firaminista sau shida.
Jam'iyyar Sri Lanka mai mulkin kasar Podujana Peramnua (SLPP) ta ce mafi yawan mambobinsu sun goyi bayan Mista Wickremesinghe ne saboda kwarewar tattalin arzikinsa.
Sakatare Janar Sagara Kariyawasam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Muna jin cewa Ranil Wickremesinghe shi ne mutum daya tilo da ke da gogewa, sani da kuma karfin samar da hanyoyin magance matsalar tattalin arziki."
Sai dai kuma zaben na Mista Wickremesinghe na iya haifar da karin tarzoma da zanga-zangar gama gari.
A ranar Larabar da ta gabata, gabanin sakamakon zaben, an kafa shingaye a kewayen majalisar inda sojoji suka yi ta jerin gwano a zagayen majalisar a shirye-shiryen tarar abun da ka je ya zo.
Makonni biyun da suka gabata an ga yadda masu zanga-zangar suka yi ta yin kira ga Mista Wickremesinghe da ya sauka daga mukaminsa, saboda suna kallonsa a matsayin wani bangare na jiga-jigan siyasa da suka karkatar da akalar kudaden Sri Lanka.
Amma ya bijire wa wadannan kiraye-kirayen kuma a makon da ya gabata ya karbi mukamin mukaddashin shugaban kasa bayan Mista Rajapaksa ya gudu.
Nasarar da ya yi na nufin zai cika sauran wa'adin shugabancin kasar har zuwa watan Nuwamban 2024.
Wanda ya kalubalance shi shine Mista Alahapperuma, dan majalisa mai adawa a jam'iyya mai mulki wanda ya samu goyon bayan babbar jam'iyyar adawa.
Ya yi alkawarin kawo sabuwar gwamnatin jam'iyya mai mulki a Sri Lanka wadda za ta "kawo karshen al'adun siyasa na yaudara". Sai dai ya kasa samun goyon bayan mafi rinjaye.