'Komawar irin su El-Rufai SDP ce ta sa za mu fita daga jam'iyyar'

Asalin hoton, FACEBOOK
Da alama dai jam'iyyar adawa ta SDP ta fara rasa wasu daga cikin manyan jam'iyyar tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya shiga jam'iyyar a makon da ya gabata.
Na baya-bayan nan da ke shirin ficewa daga jam'iyar ta SDP shi ne dan takarar gwamna a jam'iyyar na Kano, Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar a zaben da ya gabata na 2023, Injiniya Yusuf Buhari, da wasu shugabanin jam'iyyar ta SDP a Kano a ranar Talata zuwa jam'iyyar APC.
Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa wanda tsohon ma'ajin jam'iyyar APC na kasa ne, ya ce sun shirya ficewa daga jam'iyyar ne sakamakon yadda shugabancin jam'iyyar tasu ta SDP ya sauka daga kan manufa da tsarin da aka kafa jam'iyyar.
Haka kuma ya ce, wadanda jam'iyyar ta karba a yanzu ba su da kishin jama'a, sannan ba su damu da halin da kasar ke ciki ba, illa kawai bukatun kansu, suka sanya a gaba.
"Idan ka kula wai El-Rufa'in nan ba shi ne wanda ya je aka tantance shi ba a majalisa don bashi minista ba, wanda daga baya Allah bai yi ba. Da a ce ya samu ba zai fita ba, saboda haka matakin da ya dauka na dawowa cikin jam'iyyar SDP bacin rai ne, ba wai magana ba ce ta akida", in ji Hon Gwagwarwa.
Haka kuma ya ce 'sabanin yadda wasu ke ganin dawowar ta su El-rufa'i za ta sa jam'iyyar ta yi tasiri saboda fitatun yan siyasa da, za su ringa mitsa jam'iyyar, ya ce raina rawarsu aka yi, 'yanzu ni ba fittace ba ne, na rike Ma'ajin jam'iyyar APC na kasa, da sauran mukamai a matakin jiha da na tarayya, kai har da shugaban karamar hukuma na yi, ko ni kadai ban isa a ce na yi amo ba a jam'iyyar' in ji shi.
Ya musanta zargin da ake musu na cewar sun ci moriyar ganga ne za su yar da korenta shi ya sa za su bar jam'iyyar, yana mai cewar ko da ya yi takara a zaben da ya gabata da kafarsa ya tsaya, tare da sauran wadanda suka yi takarar daga jam'iyyar.
Hon Gwagwarwan ya ce sun zabi komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC ne sakamakon gamsuwa da kamun ludayin yadda shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu yake tafiyar da kasar, musamman dawo da kasar kan turba ta hanyar samar da manufofi da tsare tsaren da za su bunkasa siyasar Najeirya da kasar baki daya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar goma ga watan Marsi din da muke ciki na 2025 ne dai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, tare da komawa jam'iyyar SDP.
Hakan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan alamun da suka nuna cewa ya raba gari da jam'iyyar APC.
Masana harkokin siyasa dai na ganin ficewar El-Rufai daga APC za ta yi tasiri ganin cewa shi jigo ne a siyasar ƙasar.
A cewar irinsu farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja "wannan ficewa ta El-Rufai za ta yi tasirin gaske saboda shi hamshaƙin ɗan siyasa ne yana da ɗimbin goyon baya musamman a sassan arewacin Najeriya,".
Haka kuma ya ce girman tasirin barin jam'iyyar APC da El-Rufai ya yi ba zai misaltu ba kasancewarsa kwararren ɗan siyasa wanda ya taɓa riƙe manyan mukamai da suka haɗa da ministan birnin tarayya Abuja da kuma gwamnan Kaduna.
Sai dai masu sharhi na ganin ficewar yan jam'iyyar irinsu Bala Gwagwarwa ka iya haifar da Rauni ga tasirin jam'iyyar ta SDP, saboda da'awar da su Bala Gwagwarwan ke yin a cewar akwai yiwuwar samun karuwar wasu da ka iya ficewa daga SDP da zai shafi tasirin da ake tunanin zata iya yi.
Abin jira a gani shi ne yadda lamuran za su ci gaba da kasancewa a siyasar cikin gidan jam'iyyar ta SDP a dai dai lokacin da ake zuba ido a ga karin mutanen da za su bar ta, ko su shige ta.










