Man City na zawarcin Donnarumma, Galatasaray na son Ederson

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na tattaunawa da Paris St-Germain kan cinikin golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, kuma ana ganin wasu bukatunsa ba za su kawo cikas ba. (RMC Sport - in French)

Galatasaray ta nemi golan Manchester City dan kasar Brazil Ederson, mai shekara 3, wanda zai ba Donnarumma damar komawa filin wasa na Etihad. (Fabrizio Romano)

Southampton ta ki watsi da tayin farko da West Ham ta yi, wanda ya zarce fam miliyan 30, kan dan wasan tsakiyar Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21. (Athletic - subscription required)

Real Madrid na ci gaba da sanya ido kan dan wasan Crystal Palace dan kasar Ingila Adam Wharton, mai shekara 21 (Mail - subscription required)

Aston Villa na fatan sake siyan Marco Asensio daga Paris St-Germain sakamakon nasarar da dan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 29 ya yi a matsayin aro a bara. (Telegraph - subscription required)

Liverpool ba ta da niyyar siyar da dan wasan baya na Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, a wannan kasuwar musayar 'yan wasan, duk da kokarin da take yi na daukar 'yan wasan baya biyu don karfafa tawagarta.(Mail - subscription required)

Bournemouth ta cimma yarjejeniya da Bayer Leverkusen kan dan wasan gaban Morocco Amine Adli mai shekaru 25. (Footmercato - in French)

Bayer Leverkusen ita ce kungiyar ta baya-bayan nan da ta nuna sha'awarta kan Facundo Buonanotte na Brighton, inda Seagulls a shirye ta ke ta siyar da dan wasan na Argentina mai kai hari, mai shekara 20 a kan fam miliyan 39.(Kicker - in German)

Borussia Dortmund ta fice daga cinikin Fabio Silva bayan Wolves ta kara farashin dan wasan gaba na kasar Portugal mai shekara 23.(Teamtalk)

Dan wasan gaban Chelsea dan kasar Faransa, Christopher Nkunku, yana sha'awar komawa Bayern Munich, inda aka akwai yuwuwar cinikin dan wasan mai shekaru 27. (Florian Plettenberg)