Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ta shiga nazari kan Rodrygo, Monaco na son Trippier
Manchester City na duba yiwuwar sayo ɗan wasan Real Madrid mai shekara 24 daga Brazil, Rodrygo, wanda aka yi wa kuɗi £87m. (Fabrizio Romano)
Nottingham Forest na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Manchester City mai shekara 22, James McAtee. (Athletic - subscription required)
Chelsea da RB Leipzig sun tattauna kan ɗan wasan gaba a Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27 a lokacin ganawa kan Xavi Simons mai shekara 22. (Talksport), external
Monaco na son saye ɗan wasan Newcastle mai shekara 34 daga Ingila, Kieran Trippier. (Sky Sports)
West Ham na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Southampton mai shekara 21 daga Portugal, Mateus Fernandes, da aka yi wa kuɗi £30m. (Guardian)
Ɗan wasan gaba a Sweden Alexander Isak mai shekara 25, zai duba batun hakura da Newcastle ko cimma sabon kwantiragi idan Liverpool ta sanar da shi kai tsaye cewa babu batun yarjejeniya da shi a wannan kakar. (Givemesport)
Inter Milan da Roma daJuventus da Napoli sun bi sahun AC Milan a farautar Rasmus Hojlund, yayinda Manchester United ke son amicewa da cinikin £30m zuwa £40m kan ɗan wasan gaban mai shekara 22 daga Denmark. (The i - subscription required)
Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Jack Grealish tafiyarsa aro daga Manchester City zuwa Everton ta kunshi zaɓin sayansa kan £50m a sabuwar kaka. (Athletic - subscription required)
Chelsea ta gabatar da tayin £43m kan ɗan wasan Liverpool da Faransa mai shekara 26, Ibrahima Konate. (Defensa Central - in Spanish)
Brentford da Newcastle na tattaunawa kan saye ɗan wasan Stade Rennais na Faransa, Arnaud Kalimuendo mai shekara 23. (L'Equipe - in French)
Newcastle ta kuma kwaɗaitu da ɗan wasan Leicester City da Moroko, Bilal El Khannouss mai shekara 21, amma kuma akwai kalubale daga wurin Leeds. (Telegraph)
Everton na son ɗan wasan Leicester mai shekara 21 daga Ghana, Abdul Fatawu bayan rashin nasara a kokarin saye ɗan wasan Southampton mai shekara 19 da ke Ingila, Tyler Dibling. (Sky Sports)
Dominic Calvert-Lewin ya kori ajen ɗinsa wanda ke kokarin sama masa wata ƙungiyar. Ɗan wasan mai shekara 28 daga Ingila ya gana da Manchester United da Newcastle da Leeds. (Talksport)
Wolfsburg na son ɗan wasan Sunderland mai shekara 23 daga Northern Ireland, Trai Hume. (Sky Sports)
Chelsea na son saye ɗan wasan Bayer Leverkusen da Ecuador, Piero Hincapie mai shekara 23, saboda mumunan raunin da Levi Colwill ya ji. (Caughtoffside)
Ɗan wasan tsakiya a Jamus, Ilkay Gundogan mai shekara 34, na son cigaba da zama a Manchester City duk da tayin da yake samu daga Galatasaray. (Football Insider)