An yi jana'izar mutum takwas da rufin masallacin Zazzau ya ruftawa

Asalin hoton, Ammar Rajab
An samu mutuwar mutane lokacin da Babban Masallacin Zazzau da ke ƙofar fada, bayan ruftawar ginin mai tsohon tarihi na Masarautar Zazzau.
Jama'ar gari da ƙwararrun ma'aikatan agaji sun gudanar da aikin ceto bayan aukuwar lamarin a Juma'ar nan.
Da daddare ne misalin ƙarfe 8:30, aka yi jana'izar mutanen da suka mutu a ƙofar fada cikin ruwan sama tsamo-tsamo.
Mai magana da yawun Masarautar Zazzau, Mallam Abdullahi Aliyu Ƙwarbai ya tabbatarwa BBC cewa mutum takwas aka yi jana'izarsu, yayin da wasu mutum 21 kuma suka jikkata.
"Cikin waɗanda suka mutu har da wani mai larurar rashin gani da wani yaro da ke yi masa jagora," in ji Ƙwarbai.
Ya tabbatar da cewa Sarkin Zazzau, Mai martaba, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ba ya cikin masallacin lokacin da ginin ya rufta.
Bayanai sun ce rufin masallacin, wanda na ƙasa ne ya rufta a lokacin Sallar La'asar. Mallam Abdullahi Ƙwarbai ya ce ana raka'a ta biyu ne, rufin ginin ya faɗa a kan masallata.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna mutane ɗauke da shebura, bayan ruftawar ginin suna yashe ƙasa a tsakiyar masallacin.
An kuma ga wani da ke nuna yadda wani sashen rufin na tsakiyar masallacin ya ɓurma, har ana iya hango sararin samaniya.

Asalin hoton, Ƙasar Zazzau Jiya Da Yau/Facebook
Tashar talbijin ta TrustTV ta ruwaito Sarki Ahmed Bamalli yana cewa mutanen da abin ya ritsa da su, sun gamu da iftila'in ne ana gudanar da Sallar La'asar da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Ya ce, “Tun farko, mun lura da wata tsagewa a jikin ganuwar masallacin jiya Alhamis, kuma muna shirin ɗauko injiniyoyi don su gudanar da gyare-gyare, amma wannan al'amari maras daɗi ya zo ya faru.”
Mallam Abdullahi Ƙwarbai ya ce a ziyarar da ayarinsu wanda Sarkin Zazzau ya naɗa don bin kadin mutanen da suka jikkata, zuwa asibitin Wusasa, sun taras an kai adadin mutum 24, cikinsu har da waɗanda suka rasu mutum huɗu.
Sarki Nuhu Bamalli ya miƙa saƙon ta'aziyya ga 'yan'uwa da dangin mutanen da suka rasu. Ya kuma bayar da umarnin cewa a ci gaba da sallah a wajen masallacin ya zuwa lokacin da za a gudanar da gyare-gyaren.
Masallacin, tsohon gini ne da aka yi shi cikin fasali irin na gine-ginen Hausawa da yawan ginshiƙai da ke tashi daga jikin ganuwa har zuwa rufin ginin, sannan su tanƙwara su sauka a ɗaya ɓangaren.

Asalin hoton, AMMAR RAJAB
Cikin masu aikin ceton har da ƙungiyar ba da agaji na Red Cross.
Ga ƙarin hotuna na irin ɓarnar da ruftawar ginin ya haddasa.

Asalin hoton, AMMAR RAJAB

Asalin hoton, AMMAR RAJAB

Asalin hoton, AMMAR RAJAB

Asalin hoton, AMMAR RAJAB











