Jikan sarauniyar Ingila da matarsa sun kai ziyara masallaci

Asalin hoton, Getty Images
Duke da Duchess na Sussex, wato jikan sarauniyar Ingila da matarsa sun ci wani abincin gargajiya na Afrika Ta Kudu sannan sun ziyarci wani masallaci mai tsohon tarihi a kwana na biyu na rangadin kwana 10 da suke yi a nahiyar Afirka.
Jikokin sarauniyar sun ziyarci Masallacin Auwal mai shekara 225 a Bo-Kaap da ke Cape Town a Ranar Al'adu ta Afirka Ta Kudu - wata rana da aka ware don raya al'adun kasar.
Tun da fari dai ma'auratan sun ziyarci wata kungiyar agaji da take aiki tukuru kan batun lafiyar kwakwalwa don taimaka wa matasa.
Rangadin shi ne tafiyarsu ta farko a hukumance da suka yi da dansu Archie.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters
A yayin da suke tafiya zuwa masallacin, Yarima Harry da Meghan sun hadu da wasu malaman addini na yankin da suka hada da Sheikh Ismail Londt da kuma shugaban addini na yankin mai suna Mohamed Groenwald.
Meghan ta sanya dankwali a lokacin da za ta shiga masallacin, wanda aka gina shi a shekarar 1794 a gundumar Bo-Kaap, wacce ta bambanta saboda gidaje masu launi da ta kunsa.
Gabanin ziyarar, an dauki hoton ma'auratan suna cin abinci a gidan wasu iyalai a yankin.
Shaamiela Samodienmai shekara 63, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Dama mun saba dafa abinci mai yawa na walima ko na mutan gidan. Don haka a zuwan nasu ma ba wani abu daban muka yi ba.
"Sun ci wani abincin gargajiya na Afirka Ta Kudu mai zaki da ake kira koeksisters da kuma wani da ake yi da tuffa."
Bayan wannan ziyara kuma ma'auratan sun ziyarci bakin tekun Cape Town don ganin wani shiri da ake na taimakawa matasa kan lafiyar kwalkwalwa.
Ma'auratan sun kuma gana da masu koyawa mutane zamiya a tekun Monwabisi don jin cikakken bayani kan shirin mai suna Waves for Change.
Harry da Meghan sun kuma ji karin bayani a kan wani shirin na tallafi mai suna Lunchbox Fund, wanda mutane suke bayar da gudunmowa bayan da haihuwar dansu Archie.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters
Kungiyar Waves for Change sun bai wa ma'auratan wata dabara ta inganta lafiyar jiki da ta zuciya irin wanda suke tallafawa matasa marasa galihu kan lafiyar kwakwalwa.
Kungiyar wacce ke tallafawa yara 1,200 tana da ofishi ne a wani waje da ake sauke kaya daga jirgin ruwa a kuda da gabar tekun.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA
Sun karkare ranar da ganawa da wasu matasa da shugabannin al'umma a gidan jakadan Birtaniya na kasar.











