‘Hurumin gwamna ne ayyana yin hawan sallah ko akasin haka a jihar Kano’

Asalin hoton, OTHER
Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ce hurumin gwamnan jihar ne ya ayyana ko za a yi hawan sallah ko a’a kasancewarsa lamba daya a kula da harkokin tsaron jihar.
Gwamnatin ta kara da cewa abin takaici ne wasu su rika yin shishshigi a kan ikon da gwamna yake da shi don cimma wata manufa.
Kwamishinan shari’a na jihar ta Kano, Haruna Isa Dederi, yace a baya-bayan nan abubuwa da dama sun faru daga wasu da ya kira makiya Kano musamman tun daga lokacin da aka sanya hannu a kan sabuwar dokar masarautun jihar abin da ya kai ga shigar da kararraki a kotuna daban-daban.
Kwamishinan ya ce,”A cikin aikin gwamnati akwai bukatar hadin kai musamman idan aka tsinci kai a wani yanayi, to amma abin takaici shi ne akwai wasu jami’ai a jihar Kanon da basu shirya bayar da hadin kai wajen ciyar da jihar gaba ba.”
Haruna Isa Dederi, ya ce, gwamnan jihar Kano shi ne na daya wajen kula da harkar tsaro, don haka a kowanne irin mataki idan ya shafi batun tsaro a jihar shi ya kamata ya ce ga abin da za a yi, bayan shi kuwa sai majalisar tsaro ta jiha, su ne ya kamata su bayar da umarni na a hana wani bikin sallah amma ba daga bakin wani kwamishinan ‘yan sanda ba.
Kwamishinan shari’ar ya ce,” Mu muna ganin cewa kamar yadda ake cewa ai umarni ne daga sama, to zamu yi amfani da wannan dama mu yi kira ga koma wanene a saman, don mun tabbata cewa ba hannu ba kuma ruwan shugaban kasa, don haka duk masu sa hannu ko saka baki, ya kamata su daina domin Kano da al’ummar Kano su samu zaman lafiya.”
A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al'ada a faɗin jihar.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma
Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami'anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.
'Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al'ummar jihar.
A ranar 23 ga watan Mayun 2024 ne dai, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗa Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sauke Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma rushe ƙarin masarautun da gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2019.










