Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa

Asalin hoton, facebook/Sani Mai Katanga Photography
Da safiyar Asabar aka tashi da wani yanayi da ba a taɓa gani ba a birnin Kano, kwana ɗaya bayan miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.
Sarkin Kano da aka sauke, Aminu Ado Bayero ya koma birnin na Kano cikin dare inda ya yi sansani a gidan sarkin Kano da ke Unguwar Nassarawa.
Hakan ya faru ne jim kaɗan bayan sarki Muhammadu Sanusi II ya shiga gidan sarauta da tsakar dare tare da rakiyar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hakan dai ya sanya an shiga hali na zaman ɗarɗar duk da dai babu wata rigima ko hatsaniya da ta tashi.
Da safiyar Asabar ɗin kwamishinan ƴansanda a jihar Kano, Usaini Gumel ya kira taron manema labaru inda ya bayyana cewa jami'an tsaro za su tabbatar da hukuncin kotu kan batun masarautun Kano.
Mene ne abin da hukuncin kotun ya ƙunsa?
A ranar 23 ga watan Mayu ne Sarkin Dawaki Babba na Kano, Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Kano yana roƙon kotu ta biya masa wasu buƙatu da ya gabatar game da dokar masarautar Kano ta 2024, wadda majalisar dokokin jihar ta amince da ita.
Bayan sauraron neman mai shigar da ƙara shi kaɗai (ex-exparte), kotun ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a A. M. Liman ta bayar da umurni na wacigadi da suka haɗa da:
- Jingine aiwatar da Dokar masarautar Kano ta 2024 wadda ta shafi masarautu da naɗe-naɗen sarauta da aka yi ƙarƙashin dokar masarutun jihar Kano ta 2019.
- Kotu ta dakatar da wanda ake kara na biyar, wato kwamishinan ƴansandan jihar Kano da wanda ake kara na takwas, wato Hukumar tsaron farin kaya ta DSS - aiwatarwa ko tabbatar da dokar masarautar Kano ta 2024.
- A maimakon aiwatar da Dokar masarautar Kano ta 2024, kotu ta bayar da umurni na wucin gadi cewa komai ya tsaya a inda yake har sai lokacin da kotu ta saurari ƙarar wanda ya yi kara.
- Sannan daga ƙarshe Kotun ta bayyana cewa matsalolin Kudin Tsarin Mulki da na Hurumi sun fito ƙarara a cikin Ƙarar, saboda haka ta umarci ɓangarorin Shari'ar cewa su yi mata jawabi a kan waɗannan matsalolin a lokacin sauraron Ƙarar.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da:
1- Gwamnatin Jihar Kano
2- Majalisar Dokokin jihar Kano
3- Shugaban majalisar dokokin jihar Kano
4- Kwamishinan shari'a na jihar Kano
5- Kwamishinan ƴansanda na jihar Kano
6- Sufetan ƴansandan Najeriya
7- Hukumar tsaro ta Civil Defence
8- Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS)











