Me ya sa Kannywood suka rage sanya waƙoƙi a fina-finan Hausa?

Asalin hoton, Rahama Sadau TV
Daina ganin waƙoƙi da raye-raye a finafinan Hausa sun fara jan hankali masu kallo, inda wasu suke fargabar ko dai an daina saka waƙoƙin ne, lamarin da masana suke ganin ci gaba ne mai kyau ga masana'antar.
Tun farkon finafinan Kannywood, masana'antar ta yi fice wajen amfani da waƙa a matsayin wani muhimmin jigo na labari.
Ana dai amfani da waƙoƙin ne ko don nuna soyayya, ko nuna baƙin ciki, ko kuma don ƙarfafa wani saƙo, wanda bai rasa nasaba da kamanceceniyar da finafinan Hausa ke da shi da finafinan Indiya.
Sai dai a wani sabon yanayi, yawancin sabbin finafinai ko dai babu waƙa, ko kuma an yi amfani da waƙar ne kawai domin sharar fage.
Yanzu finafinan Kannywood da suka fi dace, masu dogon zango ne, kuma finafinai ne da ake daɗewa ana yi, ba kamar yadda ake yi finafinai masu gajerin zango na wasu awanni ba.
'Abin da ya sa aka daina saka waƙa'

Asalin hoton, Adam A. Zango Official
A game da abin da ya sa aka rage sanya waƙoƙi a finafinan, Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne ta Jamus, wanda ya yi fice wajen sharhi kan harkokin finafinai, musamman Kannywood, ya ce ƴan masana'antar ne suka fi dacewa su bayar da amsa.
Sai dai ya ce tun asali dama, "amma dai tun asali da aka fara waƙa, ba ta samu karɓuwa ba sosai, ba kowa ba ne ya karɓe ta. Wasu suna sakawa amma a bayan fage, ba tare da an fito ana rawa da waƙa ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "A ɓangaren nazari, muna ganin mutane da dama ba za su damu ba don an daina saka waƙa a fim domin dama akwai ƙorafi cewa rawa da waƙa ba al'adar Hausawa ba ce - duk da cewa wasu na ganin al'adun fim daban, al'adar mutane daban."
A nasa ɓangaren, Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru Ɗan Hajiya wanda mai shirya finafinai ne a Kannywood, ya ce yanayin lokaci ne da kuma sauye-sauyen da aka samu a harkar.
"Yanayin labaran finafinan ne suka canja, yanzu an koma masu dogon zango. Sai ya zama finafinai masu dogon zangon an fi buƙatar samar da labari mai kyau da zai ɗauki hankalin mutane ya ja su."
Ɗan Hajiya ya ƙara da cewa ba su cika mayar da hankali kan waƙa ba kamar yadda aka saba a finafinan masu gajeran zango, "waɗanda zuwa ɗaya za ka kalla na awa ɗaya ko ɗaya da rabi. Don haka ne aka ratsa waƙoƙi domin nishaɗantar da mai kallo mai. Wannan kuma kallo za a yi na watanni. Wannan shi ne babban dalilin rabuwa da waƙoƙi."
Shin ko ci gaba ne?
Sai dai wannan rage ganin waƙoƙin a finafinan ya haifar da muhawara a tsakanin masu bibiyar masana'antar, inda wasu suke ganin ci gaba ne mai kyau, wasu kuma suke ganin yana da kyau a riƙa abin da Hausawa suke kira da "taɓa kiɗi, taɓa karatu." wato a riƙ jefa waƙoƙin.
A game da wannan, Dokta Muhsin ya ce, "Ni dai a nawa ra'ayin, rage sanya waƙa a fim ci gaba ne saboda dama wasu lokuta ana saka waƙoƙin ba a wuraren da ba su dace ba. Za ka ga an saka a waƙa a wuraren da babu dalilin yin waƙar. Ko da ake yin waƙoƙin, akwai masu yin masu ma'ana, akwai waɗanda ba su da ma'ana. Su cigaba da waƙoƙinsu. Don haka su cigaba da waƙoƙinsu, mawaƙa ma su cigaba da waƙoƙinsu," in ji shi.
Ina makomar mawaƙa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game da makomar mawaƙan Hausa, Dokta Muhsin Ibrahim ya ce ba dole sai an yi waƙoƙi a cikin finafinai ne za a tabbatar da mafita ga mawaƙan na Hausa.
Ya ce, "A ɓangaren mawaƙa, ai yanzu suna yin waƙoƙinsu. Akwai shirin fitattun mawaƙa na Arewa24, za ka ga suna nuna waƙoƙin suna fita, sannan ga Youtube, sannan kuma ga Sportify. Kuma mawaƙan Hausa sun fara shiga manhajar, kuma suna samun kuɗi," in ji shi.
Ya ƙara da cewa baya ga waɗannan hanyoyin, "ana gayyatarsu bukukuwa, sannan suna yi wa ƴansiyasa waƙoƙi da sauransu. Don haka ba sai sun yi waƙa a fim ba ne za su samu tagomashi."
Shi ma Naziru Dan Hajiya ya ce an fara amfani da waƙoƙin wajen tallata finafina masu dogon zango, saboda a cewarsa akwai masu sha'awar waƙoƙi, "kuma ana amfani da su wajen tallata finafinan."
A game da ko za a dawo da sanya waƙoƙi a finafina nan gaba, Naziru ya ce, "Akwai wasu suna sanya waƙoƙi domin tallata finafinansu. Ke nan an fara da dawo da waƙoƙin, amma ba a cikin fim ɗin. Don haka za a yi amfani da waƙa domin tallata fim ɗin, ko da kuwa ba a saka a cikin fim ɗin ba."











