Jam'iyya mai mulki ta ce shugaban Koriya ta Kudu zai yi murabus

Asalin hoton, Reuters
Jam'iyya mai mulki a Koriya ta Kudu ta ce shugaban ƙasar, Yoon Suk Yeol zai yi murabus daga shugabancin ƙasar, bayan kalamansa na ayyana matakin soji a ƙasa sun tayar da ƙura ckin makon da ya gabata.
Yoon Suk Yeol ya tsallake rijiya da baya daga yunƙurin tsige shi da majalisar dokokin ƙasar ta yi a ranar Asabar, bayan ƙoƙarin da ya yi na amfani da dokar soja a ƙasar a farkon makon nan.
Tun da farko masu gabatar da ƙara sun kama tsohon ministan tsaron ƙasar, Kim Yong-hyun, a kan rawar da ya taka wajen wannan yunƙuri na kafa dokar soji.
A ranar Asabar da daddare jam'iyyar Shugaba Yoon ta yi masa halarci, na ganin ba ta tsige shi ba.
To amma ga alama ba haka kawai lamarin zai zo ya wuce ba, – dole ne shugaban ya sauka daga muƙaminsa da wuri kuma daga nan ba zai sake shiga wata harka ko dai ta ƙasar ko kuma ta ƙasar da wata ƙasa, ko ma ta duniya ba.
Tun bayan yunƙurin tsige shi ɗin ya kasance kamar shugaba na je-ka-na-yi-ka a kan wannan kujera – da yadda ma kuma hakan zai yiwu a kundin tsarin mulkin ƙasar ta Koriya ta Kudu.
Jam'iyyar Mista Yoon na ƙoƙarin ganin ta taƙaita illar siyasa da mummunan yunƙurin shugaban na sanya dokar soji.
To amma fa kuma akwai batutuwa ko abin da matakin zai iya haifarwa a ɓangaren doka da ya kamata a yi duba a kai.
Kama ministan tsaro da aka yi da safiyar Lahadin nan kan rawar da aka yi zargi ya taka a wancan yunƙuri na sanya dokar soja, hakan bai wadatar da 'yan hamayya ba.
Suna nan suna ta ƙoƙarin ganin har shi kanshi shugaban ya shiga hannu – an kama shi.











