Me ya sa ake ƙoƙarin tsige shugaban Koriya ta Kudu?

Jam'iyyun hamayya a Koriya ta Kudu sun gabatar da ƙudirin tsige shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol bayan da ya yi yunƙurin kafa dokar soji a ƙasar.
Mista Yoon ya janye ƙudurin ne bayan 'yan majalisar dokokin sun kaɗa ƙuri'ar daƙile matakin.
Ƙungiyoyin ƙwadago, har da ma jam'iyyar Mr Yoon, duk sun yi kira gare shi da ya yi murabus.
Shi dai Mista Yeol ya bai wa al'ummar ƙasar mamaki ne ranar Talata, sa'ilin da ya ayyana dokar mulkin soji a ƙasar ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, lamarin da shi ne irin sa na farko a cikin kimanin shekaru 50.
Matakin Yoon Suk Yeol, wanda ya sanar a kafar talabijin ya ce ya ɗauke shi ne domin daƙile yunƙurin masu adawa da ƙasar da kuma kawar da barazana daga Koriya ta Arewa.
To amma nan da nan sai aka gano cewa ba ya yi hakan ne saboda wata barazana ba sai dai kawai domin cimma wata manufarsa ta siyasa.
Wannan ne ya sanya dubban mutane suka taru a gaban majalisar dokokin ƙasar domin nuna adawa da matakin, inda nan take ƴan majalisa na adawa suka gaggauta amincewa da wani ƙuduri na soke matakin shugaban ƙasar.
Jim kadan bayan haka, shugaba Yoon ya fito ya nuna amincewa da matakin majalisar, sannan ya dage dokar ta soji.
Yanzu ƴan majalisar za su kaɗa ƙuri'a kan ko za su tsige shi kan wannan mataki da ya ɗauka, wanda ƴan adawa suka bayyana a matsayin "ɗabi'ar masu tayar da ƙayar baya".
Yadda abin ya faru
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaba Yoo ya yi abin ne tamkar wanda yake fuskantar barazanar kifar da gwamnatinsa, kamar yadda masharhanta suka bayyana.
A jawabinsa na ranar Talata, ya zargi ƴan adawar siyasa da yi masa zagon ƙasa gabanin ya ayyana dokar sojin, inda ya ce “a murƙushe maƙiya ƙasa waɗanda ke kawo rikici”.
Ayyana dokar ta sanya sojoji zama jagororin ƙasar na wani ɗan lokaci – inda aka tura sojoji sanya da hular kwano da kuma ƴansanda a harabar Majalisar Dokokin ƙasar, yayin da jiragen helikwafta ke shawagi a sararin sama.
Kafafen yaɗa labaru na cikin gida sun wallafa bidiyon da ya nuna jami’an tsaro ɗauke da bindiga na ƙoƙarin kutsawa cikin majalisar yayin da ma’aikata ke ƙoƙarin korarsu ta hanyar amfani da tokar kashe gobara.
Kimanin ƙarfe 11 na daren ƙasar kuma sojoji sun sanar da dokar haramta duk wata zanga-zanga a Majalisar dokoki tare da sanya duk kafafen yaɗa labaru ƙarƙashin kulawar gwamnati.
To amma nan take ƴan siyasa na Koriya ta Kudu suka bayyana matakin shugaban ƙasar a matsayin haramtacce kuma abin da ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Shugaban jam’iyya mai mulki ta masu ra’ayin riƙau ‘People’s Power Party ya bayyana matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka a matsayin “gurguwar shawara”.
A nata ɓangaren jam’iyyar adawa mai sassaucin ra’ayi Democratic Party ta buƙaci ƴan majalisarta su taru a majalisa tare da kaɗa ƙuri’ar janye dokar.
Haka nan ta buƙaci al’ummar ƙasar su fito domin zanga-zangar adawa da dokar.
Dubban mutane sun amsa kiran, inda suka yi dandazo a wajen majalisar suna furta kalaman “Babu dokar mulkin soja!”, kuma “a kawar da kama-karya”.
Mece ce dokar mulkin soji?
‘Martial law’ wata dokar wucin-gadi ce ta sojoji a lokacin da ake cikin halin ha’ula’i, ana ƙaƙaba ta ne a lokacin da farar hula suka gaza sauke nauyinsu na jagorantar ƙasa.
Lokaci na ƙarshe da aka ayyana irin wannan doka a Koriya ta Kudu shi ne a shekarar 1979, lokacin da aka kashe tare da yi wa daɗaɗɗen shugaban mulkin kama-karya na ƙasar, Park Chung-hee juyin mulki.
Kuma ba a taɓa amfani da irin wannan doka a ƙasar ba tun bayan da ta koma bin tsari na jamhuriya a 1987.
To amma a ranar Litinin shugaba Yoon ya ayyana dokar inda ya ce ya yi hakan ne domin ceto ƙasar daga “maƙiyanta”.
Yoon ya kasance shugaba wanda ya ɗauki tsauraran matakai a kan Koriya ta Arewa fiye da sauran shugabannin ƙasar da suka gabace shi.
Ya zargi masu adawa da shi da kasancewa masu tausaya wa Koriya ta Arewa, ba tare da ya bayar da wata hujja kan wanna zargi nasa ba.
A ƙarƙashin dokar mulkin soji, sojoji na samun ƙarin ƙarfin aiwatar da abubuwan da suke so kuma akan jingine amfani da kundin tsarin mulkin ƙasa da duk wani ƴanci na al’umma.
To sai dai duk da sanarwar da sojoji suka bayar na dakatar da ayyukan siyasa da mayar da kula da kafafaen yaɗa labaru ƙarƙashin hukumomi, ƴan siyasa da masu zanga-zanga sun bijire.
Haka nan babu wata alamar da ke nuna cewa gwamnati ta ƙwace iko da kafafen yaɗa labaru, inda gidajen jarida ke ci gaba da ayyukansu yadda suka saba.











