Yadda ƴan ƙasashen Gabashin Asiya ke sauya addininsu

Asalin hoton, Getty
- Marubuci, Lebo Diseko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion Correspondent, BBC World Service
An haifi ''Joon'' a cikin iyalin addinin Kirista a Koriya ta Kudu. Sai dai kamar sauran mutane da yawa a ƙasarsa, a yanzu addininsa ya sauya daga kan wanda yake lokacin yana karami.
Yanzu ya yi imanin cewa babu Allah.
"Ban san me yake can waje ba. Zai iya kasancewa akwai Allah, ko kuma babu shi," kamar yadda ya faɗa kan wayar tarho daga Seoul.
Har yanzu iyayen Joon suna cikin addinin Kirista, kuma ya ce ba za su ji ''daɗi ba'' idan suka samu labarin cewa ya sauya addini. Ba ya son ɓata musu rai, don haka yake amfani da wani suna na daban.
Al'amarin Joon ya nuna sakamakon wani bincike da wata cibiya a Amruka ta gudanar, wanda ya nuna cewa ƙasashen Gabashin Asiya su ke da yawan mutane da ke bari ko kuma sauya addini a faɗin duniya.
An tambayi mutum sama da mutum 10,000 kan addininsu, kuma yawanci sun ce yanzu addininsu ya sauya daga kan wanda suka tashi suka samu.

Asalin hoton, Getty Images
Hong Kong da Kudancin Koriya ne ke sahun gaba na mutane masu sauya addini, inda kashi 53 na mutane da aka tambaya a ƙasashen suka bayyana cewa sun sauya addininsu, ciki har da waɗanda suke ajiye batun addini kwata-kwata.
A Taiwan, kashi 42 na mutane sun sauya addini, yayin da Japan kuma suka kai kashi 32.
Idan aka kwatanta wannan da wani bincike a Turai a shekara ta 2017, an samu cewa waɗanda ke sauya addini ba su haura kashi 40 ba. A Amurka kuwa, wajen da aka tattara bayanai a bara, an gano cewa kashi 28 na manya ba su ci gaba da kasancewa a addinin da aka haifesu.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ga Joon, sauya addininsa ya saka ya bar gidan iyayensa, inda ya samu sabbin dabaru. Lokacin girmansa, iyayensa na tashi a kowane safiya da misalin karfe 6, inda suke karanta littafin Baibul.
Kowane safiya ''na kasancewa kamar lokaci na ibada,'' in ji shi.
Ya bar gida yana shekara 19, inda ya fara halartar ɗaya daga cikin babbar majami'a a Seoul - mai ɗubban mabiya. Cocin yana amfani da Baibul yadda yake, musamman yin watsi da batun sauyi.
"Ina ganin addinin Kirista ya bambanta fari da baki, mai kyau da mara kyau. Sai dai bayan duba yadda al'umma take, da kuma haɗuwa da mutane daga wurare daban-daban, na fara tunanin cewa akwai abubuwan sarkakiya a duniya".
Joon ya ce kusan rabin abokansa ba sa kan addinin da aka haifesu, musamman waɗanda aka haifa a addinin Kirista.
Kuma ba addinin Kirista ne kaɗai ke rasa mabiya ba. Kashi 20 na mutanen da suka tashi cikin addinin Buddha , a yanzu sun bar addinin.
A Hong Kong da Japan kuma sun kai kashi 17.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai mutane a yankin waɗanda ke son shiga sabon addini. A Kudancin Koriya, alal misali, kashi 12 na 'yan addinin Kirista, sabbin mutane ne da suka shiga addinin, inda waɗanda suka shiga addinin Buddha kuma ke a kashi biyar. Sabbin mutane da suka shiga addinin Kirista da Buddha a Hong Kong, sun kai kashi tara da kuma huɗu.
Sai dai, yawan mutane cikin waɗanda suka sauya addini sun kasance ba su da addini kwata-kwata, kuma alkaluman mutanen ya fi yawa a ƙasashen Gabashin Asiya idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.
Kashi 37 na mutane a Kudancin Koriya sun ce sun fuskanci haka, idan aka kwatanta da kashi 30 a Norway ko kuma kashi 20 a Amurka.
Amma duk da yadda kamar rashin addini ke kara yawa tsakanin al’ummar, da yawa daga cikin al’ummar yankin sun ce sukan gudanar da ibada ko wasu harkoki na bauta.
A cikin dukkanin kasashen da aka zanta da mutanen, fiye da rabin mutanen sun ce sun gudanar da wani aiki na bauta a cikin shekara daya da ta gabata domin girmama magabantansu.
Kuma mafi yawan mutanen da aka tattauna da su din sun ce sun yarda cewa akwai ababen bauta ko kuma wasu abubuwa da ba za a iya gani ba.
Duk wadannan abubuwa ba su zo wa Dr Se-Woong Koo da mamaki ba, wanda shi din kwararre ne a fannin nazarin addinai.
Lokacin da yake magana da BBC daga birnin Seoul, ganin mutane na amfani da wasu bangarori na addini abu ne da ya samo asali a tarihin yankin.
Ya ce “Idan aka duba tarihi, a Gabashin Asiya ba a cika samun wadanda ke mayar da hankali sosai kan addini guda daya ba.
Idan kana bin addinin Taoist, hakan ba yana nufin ba za ka iya yin addinin Budda ba duk a lokaci daya. Babu wata iyaka da ta raba wadannan addinai, ba kamar yadda ake gani ba a kasashen Yamma.”

Asalin hoton, Getty Images
A cikin karni na 19 kawai addini, kamar yadda aka san shi a yanzu, ya shigo gabashin Asiya, sanadiyyar cudanya da mutanen kasashen Yamma.
Sannan kuma yin addinai ko bin al’ada fiye da daya abu ne da ya kasa barin yankin, in ji Dr Koo.
Ya ga irin hakan har a cikin iyalansa. Dr Koo ya ce mahaifiyarsa ta sauya addinai a lokuta da dama.
“A makon da ya gabata ta yi rajista a cocin katolika da ke unguwarmu, kuma ina kyautata zaton cewa za ta je cocin a ranar Lahadi.”
Amma kuma ta fada masa cewa za ta “je wani taron addu’o’i“ a wata cocin Evangelica.
Dr Koo ya tambaye ta “mama, me ya faru da cocin ta katolika? Sai ta ce masa abin da take bukata a lokacin shi ne adduar samun lafiya, ba wani abu ba”.
Mahaifiyarsa na son ta je cocin katolika ne saboda tun asalinta ita yar cocin ce. To amma a wasu likutan idan tana bukatar wani abin takan gwada wasu addinan.











