Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan jami'an gwamnatin Tinubu da suka ajiye aiki da dalilan da suka bayar
Har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara kan yadda shugabannin hukumomin harkokin da suka shafi sarrafawa da tacewa da jigilar man fetur da gas na Najeriya suka ajiye aiki taƙaddama da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.
A ranar 17 ga watan Disamba ne shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk ya ajiye aikinsa a wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, inda ta ce tuni shugaba Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai maye gurbinsa.
Sanarwar ta ce shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da naɗin Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban hukumar ta NMDPRA.
Shi ma shugaban hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe ya sauka daga muƙaminsa, inda shi ma fadar shugaban ƙasar ta aike da sunan mutumin da zai gaje shi.
Murabun ɗinsu ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Aliko Dangote ya yi zargin cewa Farouk Ahmed na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliya biyar, har ma hukumar ICPC ta ce za ta ƙaddamar da bincike.
Sai dai ba waɗannan mutanen biyu ba ne suka fara ajiye aiki a zamanin wannan mulkin na Tinubu, bisa dalilan daba-daban da suka danganci taƙaddama da rashin lafiya.
Wannan ya sa BBC ta kalato wasu jiga-jiga gwamnatin na Tinubu da suka ajiye aiki da ma dalilan da suka bayar.
Ministan Tsaro
A ranar Litinin 1 ga watan Disamba ne Ministan tsaron Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙaminsa.
An samu labarin murabus ɗin ne a wata sanarwa da da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanguga ya fitar, inda ya ce Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar ya aika wa Shugaban Ƙasar Bola Tinubu.
Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.
Badaru ya bayyana cewa ya ajiye aikin ne domin ya mayar da hankalinsa kan kula da lafiyarsa.
Sai dai tsohon gwamnan na Jigawa ya ajiye aikin ne a daidai lokacin da ƙasar ta turnuƙe da hayaƙin satar ɗalibai a makaratun Kebbi da Neja, da kuma zargin yi wa kiristoci kisan kiyashi a ƙasar.
Ajuri Ngelale
A ranar Asabar 7 ga watan Satumban shekarar 2024 ne mai magana da yawun shugaban Najeriya Ajuri Ngelale ya ajiye aiki.
A lokacin Ajuri ya ce ya ajiye aikin ne saboda wasu abubuwa da suka danganci iyalinsa ciki har da wani rashin lafiya na wani a cikin danginsa ya ce yana buƙatar kulawarsa.
Ya kasance na farko-farkon waɗanda Tinubu ya naɗa muƙami a gwamnatinsa bayan ɗarewa karagar mulki.
Abdullahi Ganduje
A ranar Juma'a 27 ga watan Yunin 2025 ne Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa na shugaban jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar bayan kusan shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar.
Ganduje ya ajiye ne kwanaki bayan an samu hargitsi a taron jam'iyyar APC na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda wasu ƴan jam'iyyar suka bayyana rashin jin daɗinsu kan rashin bayyana sunan Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya takarar shugaban ƙasa ta shekara ta 2027.
Shi ma Ganduje ya bayyana kula da lafiya a matsayin dalilinsa na murabus ɗin, duk da cewa watanni bayan ajiye aikin ya ci gaba da gudanar da harkokinsa na siyasa da shugabancin hukumar filayen jirgin sama ta Najeriya.
Hakeem Baba-Ahmed
A watan Afrilun shekarar 2025 ne aka samu labarin tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus.
Daga bisani ne ya fito ya tabbatar da ajiye aikinsa, inda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda wasu dalilai na ƙashin kansa.
Ya yi godiya bisa damar da ya samu na aikin, amma ya ce lokaci ya yi da zai koma ga jama'arsa domin ci gaba da fafutukar kare muradun Arewa.
Ministan Kimiyya da Fasaha
A ranar 7 ga watan Oktoba ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Geoffrey Uche Nnaji, bayan ya miƙa buƙatar hakan.
Fadar shugaban Najeriya ne ta fitar da sanarwar ta hannun mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, inda ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin ministan.
A nasa murabus ɗin, minista ya sha caccaka ne bayan wata jarida a ƙasar ta zarge shi da amfani da takardun bogi, lamarin da ya musanta, wanda a cewarsa bita-da-ƙullun siyasa ne.
An dai zargi tsohon minista ne da amfani da digirin bogi daga Jami'ar Najeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin ƴan ƙasar matuƙa.
Betta Edu - Dakatarwa
A nata ɓangaren kuma, ita Betta Edu Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya dakatar da ita bayan ce-ce-ku-cen da aka riƙa yi kan zarginta da hannu a ɓacewar wasu kuɗaɗe daga ofishinta.
Ta kasance ministar jinƙai da yaƙi da talauci kafin aka dakatar da ita, sannan daga bisani aka maye gurbinta baki ɗaya.
Sai da matashiyar, wadda ta zama minista tana da shekara 37 a duniya ta musanta zarge-zargen da aka yi mata.
Ahmed Farouk
Sai kuma a ranar 17 ga watan Disamba ne shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk ya ajiye aikinsa a wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, inda ta ce tuni shugaba Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai maye gurbinsa.
Sanarwar ta ce shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da naɗin Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban hukumar ta NMDPRA.