Wane ne zaɓaɓɓen gwamnan Kogi Usman-Ododo?

Asalin hoton, Ododo Ahmed Usman
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Ododo ya samu ƙuri’a 446,237, inda ya doke mai biye masa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda ya samu ƙuri’u 259,052.
Dino Melaye na PDP ne ya zo na uku, inda ya samu ƙuri’u 46,362.
Hakan na nuna cewa Ahmed Ododo ya doke dukkanin ƴan takara 18 da suka fafata a zaɓen gwamnan jihar ta Kogi wanda aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Shi dai Usman-Ododo ba kowa ne ya san shi ba gabanin nasarar da ya samu a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC.
A lokacin zaɓen fitar da gwani, Ododo ya doke ƴan takara kama Shu’abu Audu, Stephen Ochen, Sanusi Ohiare da kuma Smart Adeyemi.
Jihar Kogi na daga cikin jihohi uku da aka gudanar da zaɓe a cikinsu ranar Asabar.
An haifi Ahmed Usman Ododo ne a ranar 7 ga watan Fabarairun 1982.
Usman-Ododo wanda ɗan ƙabilar Ebira ne da ya fito daga garin Okene, ya yi digirinsa na farko a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a Jami’ar Legas.
Kafin zama ɗan takarar gwamna a jam'iyyar APC, ya kasance babban mai binciken kuɗi na ƙananan hukumomi na jihar, tsawon shekara bakwai da rabi, kuma an yi imanin cewa ya taka rawar gani a gwamnatin gwamna Yahaya Bello mai barin gado.















