A Fada A Cika: Karar da aka kai ni kotu ce ta hana ni aiki sosai a karon farko - Yahaya Bello

Bayanan bidiyo, Yahaya Bello: Karar da aka kai ni kotu ce ta hana ni aiki sosai a karon farko

Danna hoton da ke sama domin kallon hira da Gwamna Yahaya Bello:

Gwamnan Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya ya ce kararrrakin da aka kai shi kotu lokacin da ya lashe zaben gwamna a karon farko su ne suka hana shi aiki sosai.

Ya bayyana haka ne a shirinmu na A Fada A Cika, wanda muke gudanar da hira ta musamman da manyan mutane.

Gwamna Bello ya ce "Nasarar da muka samu a karo na biyu ta fi ta shekara hudu da muka yi a baya... mun yi aiki sosai amma saboda an kai mu kotu, ana raba mana hankali. Shari'u ashirin da daya muka yi [ na bayan zabe] har zuwa Kotun Koli."

Sai dai gwamnan ya ce a wa'adinsa na biyu ya fi gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama'a saboda bai fuskanci kalubalern shari'a ba.