Gwamnatin Kogi ta kai kamfanin Dangote ƙara

Yahaya Bello da Aliko Dangote

Asalin hoton, Others

Gwamnatin jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya ta shigar da ƙarar kamfanin Dangote kan batun wanda ke da mallakar kamfanin siminti da ke Obajana a jihar.

Babban mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai Mohammed Onogu, ya tabbatar wa da BBC batun, inda ya ce sun shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a gaban babbar kotun jihar da ke Lokoja.

Mista Onugu ya ce gwamnatin na fatan kotu za ta yi duba a tsanake kan yarjejeniyar da ke tsakanin kamfanin Dangote da jihar Kogi da aka cimma ranar 30 ga watan Yulin 2002 da kuma ran 14 ga Fabrairun 2003.

Sai dai har yanzu kamfanin Dangoten bai ce komai ba kan batun.

Wannan ƙara da gwamnatin Kogi ta shigar na nuna cewa sulhu da shiga tsakanin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a makon da ya gabata bai yi tasiri ba.

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kogi ta rufe kamfanin simintin bisa zargin cewa bai bi ƙa'ida ba wajen mallakar hannun jarinsa.

Sai dai a martanin da kamfanin Dangote ya yi tun a lokacin, ya ce ya zuba jari a kamfanin simintin na Obajana, kuma ya bi dukkan ƙa'idoji kafin ya fara harkar siminti a jihar.

A cikin ƙarar da gwamnatin jihar ta shigar, ta nemi kotun da ta soke yarjejeniyar bisa hujjar cewa ba ta cika sharuɗɗanta ba, waɗanda su ne ginshiƙin ingantaccen kwantiragi.

Gwamnatin jihar na kuma son kotu ta hana kamfanin Dangote cin gajiyar riba ko samun wata dama daga yarjejeniyar ta 2002 da 2003, saboda rashin bai wa gwamnatin Kogin wasu muhimman bayanai kan matsayarta a kan yarjejeniyar.

Kazalika tana so a soke dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla ɗin.

Wasu labaran da za ku so

Farkon rikicin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan fara wannan takun saƙa saimajalisar dokokin jihar Kogi ta ba da umarnin rufe kamfanin simintin Dangoten, bisa ikirarin cewa ta samu korafi daga wasu al'ummomin jihar da ke zargin cewa kamfanin Dangoten bai bi ƙa'ida wajen mallakar hannayen jarin kamfanin simintin Obajana ba.

Lamarin ya haddasa yamutsi a kamfanin, saboda wasu rahotanni sun nuna cewa an samu wasu da suka jikkata.

Alhaji Sada Ladan Baki, shi ne babban darakta a kamfanin Dangoten, ya shaida wa BBC cewa a wancan makon cewa, gayyatar su aka yi a kan su je su sanya jari a kamfanin simintin na Obajana, kuma sun sanya.

Ya ce, "Mu ba mu sayi kowane kamfani ba, an gayyace mu mu sanya jari ne a kamfanin simintin Obajana, kuma muka yi hakan.

"Sannan duk wasu ka’idoji da ya kamata mu cika mun cika, baya ga kiyaye duk wasu sharudda na zuba jari a kamfanin.

"Amma ba mu san me ya faru ba mahukunta a jihar Kogi suka dauki matakin rufe kamfanin wai saboda zargin cewa mun yi almundahana wajen mallakar hannun jarin kamfanin simintin.”

Su Dangote

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Ga alama sulhun da gwamnatin tarayya ta yi tsakanin bangarorin biyu bai yi tasiri ba

Alhaji Sada Ladan Baki, ya ce "Tun daga lokacin da Gwamna Yahaya Bello ya hau mulki kawo yanzu mun biya haraji da kudin wasu abubuwa da ya kai naira biliyan 16.”

Kuma wannan ne ya sa mahukunta a jihar suka ce sai kamfanin ya nuna shaida.

Gwamnatin jihar dai ta ce abin da take yi a cikin shekaru biyar da suka wuce shi ne kokarin ganawa da kamfanin Dangote, na kafa kwamitoci daban-daban da suka duba hanyar da aka bi ta shari’a wajen mallaka wa kamfanin Dangote ragowar kashi 10 cikin 100 na hannun jarin kamfanin simintin da ke hannun gwamnatin jihar Kogi amma hakan bai yi wu ba.

Ya ce a duk a lokacin da aka zauna sai kamfanin Dangote ya ce zai kawo takardunsa amma shiru har aka kai lokacin da majalisar dokokin jiha ta dauki matakin rufe kamfanin simintin.

A yanzu haka dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta shiga tsakani da nufin sasanta bangarorin biyu.