Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi da Imo da Bayelsa

...

A ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi da kuma wasu jihohin biyu.

Tuni aka kammala kaɗa ƙuria a rumfunan zaɓe da dama.

Sauran jihohin su ne Imo da Bayelsa.

Hukumar zaɓe ce za ta bayyana waɗanda suka yi nasarar a cikin ɗimbin ƴan takarar da suka fafata.

Wannan shafi ne da ke kawo muku sakamakon zaɓen yayin da yake fitowa daga Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Sakamakon zaɓen jihar Kogi

...

Asalin hoton, Twitter

Jam'iyyu 18 ne suka fafata a zaɓen gwamnan jihar ta Kogi, wadda ake tunanin ƙabilanci zai taka muhimmiyar rawa a cikinsa.

Manyan ƴan takara uku da ake ganin fafatawar ta fi zafi tsakaninsu su ne:

  • Sanata Dino Melaye na jam'iyyar PDP
  • Ododo Ahmed Usman na jam'iyyar APC
  • Murtala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP

Shafa saman taswira domin ganin sakamakon kowace ƙaramar hukuma:

Sakamakon zaɓen jihar Imo

...

Asalin hoton, HOPE UZODINMA/ SAMUEL ANYANWU / ATHAN NNEJI ACHONU/ FACEBOOK

Jam'iyyu 17 ne suka gabatar da ƴan takarar gwamnan jihar Imo a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023.

Manyan ƴan takara su ne:

  • Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC
  • Sanata Samuel Anyanwu na jam'iyyar PDP
  • Athan Nneji Achonu na jam'iyyar LP

Shafa saman taswira domin ganin sakamakon kowace ƙaramar hukuma:

Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bayelsa

.

Asalin hoton, facebook

Bayanan hoto, Ƴan takarar gwamnan Bayelsa na PDP da APC da kuma LP

Ƴan takarar 16 ne suka fafata a zaɓen gwamnan jihar ta Bayelsa na ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Manayan ƴan takara a zaɓen su ne:

  • Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP
  • Timipre Sylva na jam'iyyar APC
  • Udengs Eradiri na jam'iyyar LP

Shafa saman taswira domin ganin sakamakon kowace ƙaramar hukuma: