Ƙalubale biyar da ke gaban sabuwar Firaministar Birtaniya

Liz Truss

A ranar Talata ne aka rantsar da Liz Truss a matsayin sabuwar Firaiministar Birtaniya.

Tun a ranar Litinin ne aka sanar da ita a matsayin wacce ta lashe zaɓen takarar shugabancin jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Conservatives.

Hakan ya sa ta zamanto mace ta uku da ta zama Firaiministar Birtaniya - kuma wacce ta maye gurbin Boris Johnson - wanda ya yi murabus babu girma ba arziki.

Sai dai duk da wannan ci gaba da nasara da Liz Truss ta samu, masu sharhi na cewa akwai manyan ƙalubale a gabanta.

Editan BBC Hausa, Aliyu Abdullahi Tanko, ya fayyace manyan ƙalubale biyar da ya ce sabuwar firaiministar za ta fuskanta tun a ranar farko na fara mulki.

Ƙalubale biyar

1. Ƙalubale na farko shi ne batun tsadar rayuwa da ake fama da shi kusan a ko ina a faɗin duniya - inda a yanzu a Birtaniya farashin gas da na lantarki suka fi ƙarfin talaka, dole sai gwamnati ta shigo.

2. Abu na biyu shi ne batun tattalin arziki, inda na Birtaniya ya yi matuƙar yin ƙasa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A karon farko tun shekarar 1985 idan aka kwatanta dala da fam na Ingila, shi fam ɗin ya sauko kaɗan. Hakan kuma babban ƙalubale ne.

3. Ƙalubale na uku shi ne batun ficewar Birtaniya daga Turai wato Brexit.

Har yanzu akwai wasu abubuwa da ba a warware ba musamman na kan iyaka tsakanin arewacin Ireland da ke cikin Birtaniya da kuma Jamhuriyar Ireland da ke cikin Tarayyar Turai.

"Su kuma wadannan yankuna Ɗanjuma ne da Ɗanjummai, wato ƴan uwan juna ne," kamar yadda Aliyu Tanko ya ce.

4.Ƙalubale na huɗu shi ne na yadda a wannan shekarar aka dinga yaje-yajen aiki na direbobi da ma'aikatan jiragen ƙasa.

Kowa ya san cewar batun jiragen ƙasa shi ne ƙarfin tattalin arzikin Birtaniya.

Yaje-yajen aikin sun yi tasiri kuma dole sai sabuwar firaiministar ta zauna da waɗannan ƙungiyoyin da ke da ƙarfi sosai, waɗanda da sun ce za su yi yajin aiki sai komai ya nemi ya wargaje a ƙasar.

5. Abu na ƙarshe da za ta fuskanta daga rana ta farko shi ne rarrabuwar kawuna da ake fuskanta a jam'iyyarta ta Conservative.

Saboda tun kafin saukar Boris Johnson akwai matsala ta cewar an samu gidaje daban-daban na siyasa a jam'iyyar, ita ma kanta ta ja wasu.

Ko za ta iya shawo kan matsalolin?

Idan dai za a yi la'akari da wanda ta yi takara da shi wato Rishi Sunak a matsayin mizani, to wataƙila wannan ba wani abu ba ne mai ƙarfi.

Kasancewar shi Rishi Sunak asalinsa Ba'indiya ne, to ana ganin Birtaniya a daidai wannan lokacin ba ta yi ƙwarin da za a ce a zaɓi baƙo ya zama firaiminista ba.

Kuma da yake an san ƴan Conservative da suka yi zaɓen yawanci mutane ne da suke zaune a karkara kuma wadanda ba sa mu'amala da ƴan wasu ƙasashe da sauran su balle har a ba shi damar yin nasara.

Sai dai abin da ake tunanin za ta iya yi da sauri da zai iya sa mutane su fara jin amincewa da shugabancinta, ita ce maganar tsadar gas.

Da ta fara wani abu akai to kusan kowa zai fara samun sauƙi saboda an kusa a shiga lokacin hunturu kuma mutane abin da suke kuka akai ke nan.

"Yana cikin abin da ake ganin za ta fara mayar da hankali a kai daga ranar da aka rantsar da ita, a yau ɗin nan sai ta yi magana a kai idan ba haka ba akwai matsala," a cewar Editan BBC Hausa.