Boris Johnson: Firaministan Birtaniya da ya keta dokoki

Asalin hoton, Getty Images
Boris Johnson ya dade yana saba wa dokoki na al'ada da aka san siyasa da su, to amma abu ne mai wahala a yarda cewa ruwa ya ci shi a yanzu, ya tafi.
Boris, wanda za a iya kira da ''sakaina iya ruwa'', ya kasance firaministan Birtaniya wanda ya sha artabu da kuma samun kansa a cikin matsaloli.
Matsalolin da idan da a ce wani dan siyasar ne da tuni sai dai buzunsa, to amma shi kam tsohon firaministan, kusan a ko da yaushe yana sha, domin a je a zo sai ya girgije ya sake farfadowa, ya tsaya kyam, kamar ba a yi wannan tata-burza da shi ba.
A wannan zamani da ake fama da 'yan siyasa marasa karsashi da gundurar jama'a, Boris Johnson ya kasance wani na-daban, ta yadda ba ma maganar yanayi da kalamansa ba, hatta daga shigarsa da irin gyaran gashinsa ko daga nesa ka tsinkaye shi za ka gane shi.
Wannan ya ba shi damar kaiwa ga masu zaben da wasu 'yan siyasar ba su iya kaiwa garesu ba.
Yana dan jam'iyyar masu ra'ayin rikau ya ci zabe sau biyu a matsayin magajin garin birnin London, birnin da ake ganin ya karkata ne ga masu ra'ayin gaba-dai-gaba-dai.
Kuma ya kasance jigo wajen fitar da Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.
Gagarumar nasarar da ya samu a zaben 2019, ta sa kusan dukkanin 'yan jam'iyyarsu ta Kwanzabatib (masu ra'ayin rikau) suka sallama masa da cewa mutum ne mai sa'a a siyasa.
To amma kuma kwatsam sai ga annobar korona ta durfafo.

Asalin hoton, Getty Images
Annobar, aba ce da za ta iya zama babban kalubale da barazana ga duk wani shugaba, amma a karshe ba wai wani tsari ko mataki da firaministan da gwamnatinsa suka dauka ba ne ya yi sanadiyyar faduwarsa ba.
Maimakon haka dabi'a ce da halin Mista Johnson suka yi sanadin ganin bayansa.
Liyafar da shi da ma'aikatansa suka gwangwaje a fadarsa, a lokacin da aka yi dokar hana haduwar mutane da yawa a wuri guda ( Downing Street), ta sa aka rika suka da zarginsa cewa bai cancanci shugabancin ba.
Wannan shi ne karo na farko da ya fuskanci irin wannan zargi a shekaru 35 na rayuwarsa ta aiki.
'Sarkin duniya'
Alexander Boris de Pfeffel Johnson yaro ne mai cike da buri, inda ya yi fice da cewa yana son ya zama ''sarkin duk duniya''.
Boris wanda iyayensa 'yan Ingila ne asali suka haife shi a New York , ya kasance daya daga cikin 'yan uwa shida masu matukar gogayya.
Ya yi wani bangare na rayuwarsa a gonar mahaifansa da ke Exmoor National Park, a kudu maso yammacin Ingila.
A farko-farkon shekarun 1970, iyayensa da 'yan uwan nasa gaba daya sun joma Brussels, inda mahaifinsa, Stanley Johnson, ya samu aikin Hukumar Tarayyar Turai.
Boris ya halarci makaranta (European School) a Brussels, babban birnin Belgium inda ya hadu da matar da ta kasance matsara daga baya Marina Wheeler.
A 1973, lokacin da auren iyayensa ya mutu, sai ya koma makarantar kwana a Ingila, inda kuma daga baya ya samu tallafin karatu zuwa makarantar da ba ta gwamnati ba, mafi daukaka a Ingila, Eton.

Asalin hoton, Getty Images
Tun a lokacin aka fara ganin alamun fitattun halayen Mista Johnson in ji mutumin da ya rubuta littafin tarihinsa, Andrew Gimson.
Shugaban makarantar Eton, Sir Eric Anderson ya bayyana shi a lokacin da cewa ''yaro ne mai sa karsashi wanda za ka so kasancewa da shi, amma kuma mai wuyar sha'ani''.
Malaminsa na tarihi Martin Hammond ya yi bayani a kansa mafi jan hankali a 1982 a wata wasika da ya rubuta wa babansa, kamar yadda Gimson ya ruwaito.
"Wani lokaci Boris yana harzuka idan aka soke shi a kan wani abu da ya yi da ake ganin gazawa ce ta abin da ya rataya a wuyansa," Mista Hammond ya rubuta a game da Johnson mai shekara 17 a lokacin.
Kungiyar mashaya ta Oxford
Daga Eton, Mista Johnson ya wuce zuwa Jami'ar Oxford University, ya karanta tarihi.
A can ya zama shugaban kungiyar daliban tarihin- wadda kungiya ce fitacciya da ta yi suna wajen muhawara tun daga shekarar 1823 - haka kuma ya kasance dan kungiyar nan da ta yi kaurin suna ta mashaya (Bullingdon drinking club).
Ya auri wata 'yar uwarsa daliba kuma mai tallata kayan kawa, Allegra Mostyn-Owen, a wani biki da aka yi facaka.
Kamar yadda Andrew Gimson, ya bayyana, Mista Johnson ya kokarta ya zo wurin bikin amma da tufafin da ba su dace ba, sannan kuma zobensa na auren ya bata bat cikin sa'a daya da karbarsa. Auren nasu bai kai shekara uku ba ya mutu.
Mista Johnson ya kammala Jami'ar Oxford, inda daga nan kuma sai ya fara aiki da jaridar Times.
Ya rasa aikinsa bayan da ya yi karya a kan yawan wasu kudade- abin da a gaba ya bayyana da cewa daga cikin dukkanin kura-kuren da ya yi yana ganin wannan shi ne babba.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan matsala ta kasance, tarnaki na dan lokaci a gareshi, to amma daga baya nan da nan editan jaridar Daily Telegraph, Sir Max Hastings ya dauke shi aiki.
A matsayinsa na wakilin jaridar a Brussels Mista Johnson ya rika, muzanta dokokin da Hukumar Tarayyar Turai ke yi, ko da yake yawancin abokan aikinsa da ke wakiltar wasu gidajen jaridun na ganin yana zuzuta labaransa, a wani lokacin ma suna ganin ba gaskiya ba ne.
A 1999, Mista Johnson ya zama editan mujallar masu ra'ayin rikau ta Spectator, kuma shekara biyu bayan nan ya fada siyasa inda ya ce zaben kujerar majalisar dokoki ta mazabar Henley, a Oxfordshire, a jamiyyar masu ra'ayin rikau ta Kwanzabatib.
Zuwa wannan lokaci ya auri abokiyarsa tun sun yara, Marina Wheeler, daga Brussels, wadda a lokacin ta zama cikakkiyar lauya.
Sun haifi 'yarsu ta farko, Lara Lettice, a 1993, da kuma wasu karin 'ya'yan uku - Milo Arthur da Cassia Peaches da Theodore Apollo.
Mista Johnson ya yarda da irin kalubalen da samu kanasa a ciki na kasancewa dan jarida kuma dan siyasa, inda ya ce:
"Ina gani na yi nasarar sukuwa a kan dokuna biyu tare a lokaci daya zuwa wani lokaci, to amma akwai lokacin da tazarar da ke tsakanin dokunan ta yi fadi da yawa sosai."
Ya kasance cikin ministocin jeka-na-yi-ka, wato na bangaren 'yan hamayya a lokacin jagoran jam'iyyar Kwanzabatib Michael Howard, amma kuma aka cire shi bayan da ya ki fadar gaskiya cewa yana neman wata mata.

Asalin hoton, Getty Images
To amma bayan shekara daya ya sake samun wannan matsayi a jam'iyyar tasu a karkashin jagorancin David Cameron. Mutanen biyu sun kasance tare a makarantarsu, Eton da kuma Oxford.
Mista Johnson ya bayyana kasancewarsa karkashin sabon jagoran nasu, wanda ya ce ya girma da cewa ''abin tashin hankali a gareshi''.
Mista Johnson ya sauka daga matsayinsa na editan mujallar Spectator. Daga nan kuma ya zama wani sananne a talabijin, inda yake aikin taya gabatar da wani shirin barkwanci na BBC, mai suna Have I Got News For You.
Ya samu damar hawa sama a matakin siyasa a 2007, a lokacin da ya nemi yi wa jam'iyyar Kwanzabatib takarar kujerar magajin garin London.
Mutane da dama sun yi mamakin yadda ya ci zaben inda ya samu kuri'a sama da miliyan daya, kuma aka sake zabensa bayan shekara hudu, da yawan kuri'un da ba su kai na da ba, amma kuma dai masu rinjaye.

Asalin hoton, Getty Images
A matsayinsa na magajin garin London ya bullo da wani tsari na bayar da hayar keke, kekunan da mazauna birnin a lokacin suke wa lakabi da kekunan Boris.
Sannan kuma shi ne ya jagoranci shirye-shiryen gasar wasannin Olympics da aka yi a London a 2012.
Daya daga cikin hotunansa da suka janyo masa ce-ce-ku-ce, shi ne inda aka ganshi dauke da tutar Birtaniya, yana sulun igiya a sama.
Haka kuma ya fara aikin gina wata gada a kogin Thames, wanda wannan aiki ne mai tsadar gaske mai takaddama, wanda a karshe ya yi watsi da shi.
Bayan wa'adinsa a matsayin magajin garin London , an zabe shi a matsayin dan majalisar dokokin Birtaniya mai wakiltar mazabar Uxbridge da South Ruislip.
Bayan ya yi shekara daya kusan ba a jin duriyarsa a majalisar dokokin, ya sake daukar hankali a jaridu, lokacin da sanar da cewa zai jagoranci kamfe na fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai a zaben raba-gardama.
Wannan ba karamar mahangurba ba ce ga David Cameron, wanda ke fatan Mista Johnson zai taimaka masa da irin baiwar sa'a da yake da ya shawo kan masu zabe daga ko'ina a fadin kasar domin Birtaniya ta ci gaba da zama a Tarayyar Turai.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan rashin nasara da ya yi a yunkurinsa na zama jagoran jam'iyyar Kwanzabatib bayan Mista Cameron ya sauka, har ya fara tunanin kawo karshen siyasarsa.
To amma kwatsam bayan Theresa May ta zama firaminista, sai ta nada shi a matsayin ministan harkokin waje, abin da ya ba wa masu lura da al'amura mamaki.
Daga nan fa masu hamayya da shi suka bude babin bankado abubuwan da ya yi na kwaba a baya.
Wadannan anbubuwa kuwa sun hada da wani rubutu da ya yi a wata jarida a 2007, inda a ciki yake bayyana tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, da cewa ta yi kama da ''muguwar ma'aikaciyar lafiya a asibitin mahaukata''.
Haka kuma an matsa masa sai da ya bayar da hakuri ga kasar Papua New Guinea a kan yadda ya bayyana kasar cewa ana cin naman mutane da kisan kai haka kawai.
A can baya ma, ta kai sai da ya bayar da hakuri a kan yin amfani da kalamai na nuna wariyar launin fata a kan tsoffin kasashen karkashin mulkin mallaka na Birtaniya.

Asalin hoton, Boris Johnson
A lokacin da yake ministan harkokin wajen Birtaniya Mista Johnson ya mara baya ga daukar wasu tsauraran matakai a kan Rasha, tare da korar wasu jami'an diflomasiyya 23 bayan sanya wa tsohon jami'in leken asiri na rashar Sergei Skripal, guba.
Haka kuma ya sha suka lokacin da a bisa kuskure ya ce Nazanin Zaghari-Ratcliffe, ma'aikaciyar agajin da aka daure a Iran shekara shida bayan an kama ta da zargin laifin leken asiri, cewa ta yi aiki a matsayin 'yar jarida.
A 2018, ya fice daga gwamnatinta a kan korafin cewa yarjejeniyar da Theresa May take yi ta ficewar Birtaniya daga Turai ta yi sauki matuka.
Ya koma aikinsa na da, wanda yake samun kudi sosai na rubuta makala a jaridar Daily Telegraph, kuma nan da nan ya sake samun kansa a takaddama bayan da ya bayyana mata Musulmi masu sanya nikabi da cewa sun yi kama akwatunan wasika.
Ya ci gaba da zama mai kakkausar sukar Theresa May, a majalisa, kuma lokacin da aka neme shi da ya yi ritaya daga majalisar, sai kuma ya fito neman shugabancin jam'iyyar tasu ma gaba daya.
A wannan karon kuma ya yi nasara.

Asalin hoton, Getty Images
Watanninsa na farko a wannan matsayi sun gamu da kalubale, ya sha fama kan yadda jam'iyyarsa za ta yi mulki da dan rinjayen da bai taka kara ya karya ba a majalisar dokokin Birtaniyat.
Ya yi fito-na-fito da 'yan majalisar da ke neman dakatar da dabarunsa na ficewar Birtaniya daga Turai, 'yan majalisar da suka hada har da wasu fitattu daga cikin jam'iyyarsa.
A wani mataki da ya janyo gagarumar takkada a kasar, Mista Johnson ya yi kokarin dakatar da majalisar dokoki domin tabbatar da ficewar Birtaniya daga Turai ranar 31 ga watan Oktoba na 2019, da yarjejeniya ko ba yarjejeniya.
Wannan ya kai har sai da Kotun Kolin kasar ta yanke hukuncin haramta matakin nasa.
A 2019 ya yi kasada inda ya nemi a sake zaben kasa baki daya, bisa yakin zaben cewa zai tabbatar Birtaniya ta fice daga Turai.
Ya kuwa yi nasara da hakan, inda ya sake dawowa kan mulki da gagarumin rinjayen da jam'iyyarsu ta Kwanzabatib ba ta taba samu ba tun zamanin Margaret Thatcher a shekarun 1980.
Yarjejeniyarsa ta ficewar Birtaniya daga Turai ta yi nasara, inda a ranar 31 ga watan Janairu Birtaniyar ta fice daga Tarayyar ta EU.
Annoba
A farkon shekara ta 2020, abubuwa sun kasance kamar yarjejeniyar kasuwanci da Tarayyar Turai ita ce za ta kasance babban kalubale ga gwamnatinsa - Kuma fitar da Birtaniya daga Turai za ta kasance babban abin tarihi da gwamnatinsa ta yi.
To amma cikin 'yan makonni, kamar dai sauran shugabannin duniya ya samu kansa tsundum a matsalar annobar korona.
Ta bayyana a fili cewa gwamnatinsa ba ta shirya wa annobar ba, inda ma'aikatan lafiya suka kasance ba su da kayan kariya kuma cutar ta rika hallaka ta'annati a gidajen kula da tsofaffi.

Asalin hoton, PA Media
A watan Afrilu na 2020, shi kansa Mista Johnson ya kamu da koronar, inda ya shafe kwana uku a sashen kulawar gaggawa a asibiti a London.
A kasa da mako uku kuma budurwarsa Carrie Symonds, ta yi haihuwarta ta farko, inda aka sanya wa 'yar suna Wilfred. Sun daura aurensu a cikin sirri a watan Mayu na shekarar ta 2020.
Ba kasafai Mista Johnson yake son yin magana a kan abin da ya shafi rayuwarsa ba amma dai an san cewa yana da 'ya'ya bakwai, da suka hada da na biyu da ya haifa da Carrie.
Hudu kuma tare da Marina Wheeler sai wani da Helen Macintyre. A dan wannan lokaci na wata 20, Birtaniya ta yi fama da annobar korona, inda aka samu mace-mace fiye da sauran kasashen Turai.
To amma kuma ta kasance ja-gaba wajen kirkirar allurar riga-kafin cutar da kuma rarraba ta.
Haka kuma Johnson zai bugi kirji cewa ya kula da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata a yayin annobar. To amma kuma nan da nan sai wasu matsalolin suka fara tasowa.

Asalin hoton, Reuters
Bayan da aka tilasta fitar da tsohon mai ba shi shawara daga gwamnati, Dominic Cummings, tsohon hadimin ya fasa kwai.
Ya bayyana wa wani kwamiti na musamman na majalisar dokokin kasar a watan Mayu na 2021 cewa dubban mutane sun mutu ba gaira ba dalili saboda Mista Johnson bai dauki matakin da ya dace ba cikin gaggawa alokacin bullar korona, da kuma kin yarda da shawarar masana.
Mista Cummings ya ce tsohon shugaban nasa bai dace ba da mukamin firaminista.
Mista Johnson ya fuskanci zarge-zarge da dama na keta dokoki da rashin nuna kamala ga ofishinsa, wanda dukkaninsu ya yi ta tsallakewa.
To amma mafi muni da ya bayyana shi ne na watan Nuwambar 2021, lokacin da aka bayar da rahoton cewa shi da ma'aikatansa sun yi liyafa a fadar gwamnati (Downing Street) a lokacin da aka haramta haduwar jama'a a cikin gida, ya bayyana a jaridar Daily Mirror.
Sai kuma kwatsam ga wata gararumar ta bayyana bayan sama da mako daya, a lokacin da wani hoton bidiyo ya bayyana daga shekarar ta 2021, wanda ke nuna ma'aikatan fadar gwamnatin na shewa da burede a kan yin liyafar Kirsimeti.

Asalin hoton, Getty Images
Allegra Stratton, wadda ta yi wani barkwanci a cikin bidiyon, cewa ba liyafa ba ce, taro ne kawai na a ci a sha, ta yi murabus a matsayin mai bayar da shawara ga gwamnati, tana zubar da hawaye inda ta ke cewa ta yi nadama da kalaman nata.
Bullar hoton ya bata wa Mista Johnson rai kamar yadda ya gaya wa 'yan majalisa kuma ya ce ya bayar da umarnin a gudanar da bincike.
A karshe dai mutumin da ke da hannu a lamari ya, Simon Case, ya sauka daga mukaminsa a bisa dole.
Haka shi ma Mista Johnson din a dolen dole bayan ya sha musantawa a karshe ya yarda cewa ya halarci wannan liyafa, amma kuma ya ce wai shi ya dauka taro ne na aiki.
Gwamnatinsa ta kara tsunduma cikin rikici, bayan da jaridar Telegraph ta bayyana cewa ma'aikatan fadar gwamnatin sun yi liyafar dare kwana daya kafin jana'izar mijin sarauniya (Duke of Edinburg).
Boris, ya nemi gafara daga Sarauniya a kan abin da ma'aikatan nasa suka yi, a wannan lokaci da Sarauniyar take cikin matakan kariyar korona inda take zaune ita kadai a wurin jana'izar mijinta.

Asalin hoton, Reuters
A wani rahoto mai cike da badakar liyafa da aka rika yi, har kusan 16 a fadar gwamnatin tun 2020, babbar jami'i a fadar Sue Gray ta ce wasu daga cikin tarukan da aka yi na liyafa, bai kamata a ce an yi su ba.
Ta kara da cewa hakan na nuni da gazawa a bangaren gwamnati. Ministocin sun goyi da bayan Mista Johnson, amma kuma 'yan majalisa na jam'iyyarsa ta Kwanzabatib aka bari da aikin kare dabi'ar shugaban nasu a mazabunsu.
A yanzu dai jam'iyyar hamayya ta Labour ta samu gagarumin ci-gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a a karon farko tun bayan da Boris Johnson ya zama firaminista. Sai kuma ga sakamakon binciken 'yan sandan London a kan liyafar da aka yi ta yi a lokacin kullen korona a fadar gwamnatin.
An yi jimillar tara 126 ga mutum 83 a binciken 'yan sandan, kan tarukan liyafa 12 a lokacin korona. Kuma daga cikin wadanda aka aika wa samnarwar yi musu tarar har da firaministan da matarsa Carrie.
Sai kuma ga cikakken rahoton Sue Gray wanda aka fitar, da ke bayar da cikakken bayani kan liyafar shan barasar da aka yi a fadar gwamnatin a lokacin da aka umarci sauran jama'ar kasa su zauna a gida.
Rahoton da kuma wasu hotuna da aka yi satar fitar da su ga 'yan jarida, sun sa mutane sun ka karin abubuwa na ban kunya da firaministan ya aikata, inda aka ga hotunansa yana shan barasa a liyafa da ma'aikatan fadarsa.
Matsin lamba da suke sha daga mazabunsu, ya sha 'yan majalisar dokokin kasar suka kira a yi kuri'ar yanke kauna a kan firaministan. Amma kuma ya yi nasarar tsallakewa.
Sai dai kafin a je ko'ina, sai kuma ya tsunduma cikin wani rikicin na nada mataimakin mai tsawatarwa na majalisa, Chris Pincher, wanda ake bincike a kansa sakamakon tarin zargi na cin zarafi na lalata.
A ranar Laraba 6 ga watan Yuli, Mista Johnson ya nemi gafara a kan nada Chris Pincher, bayan an gaya masa kan rashin da'ar da ake zarginsa da yi.
Firaministan ya amince cewa an gaya masa korafin a 2019, kuma ya ce ya yi babban kuskure da yaki daukar mataki a kai.
Wannan abu ne ya bude kofar murabus ga jami'an gwamnatinsa da suka hada da Ministan Kudi Rishi Sunak da kuma na Lafiya Sajid Javid.
Bayan kwana daya da wannan da kuma karin gomman murabus da jami'an gwamnatin ke ta yi, a karshe Mista Johnson ya ga ba shi da zabi da ya rage illa ya jefar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.
Ya mika wuya, tare da bayar da kai bori ya hau, inda ya karbi kaddara, ya sauka daga mukaminsa na jagoran jam'iyya.
Bayan da Mista Johnson ya yi shekara kusan 40 yana jan zarensa, a karshe dai ruwa ya kare wa dan kada, tusa ta kare wa bodari.
To amma waye zai yanke hukuncin cewa Boris Johnson ba zai sake dawowa ba?











