Kantunan da ba masu tsaro na ƙaruwa a Koriya ta Kudu saboda amanar mutane

- Marubuci, David Cann
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Seoul
- Lokacin karatu: Minti 5
Can da talatainin dare a wani yankin karkara na birnin Seoul na Koriya ta Arewa, na ji ina buƙatar samun ɗan wani abin da zan ci. Wannan ba matsala ba ne - saboda ina tsallaka titi daga gidana akwai kantuna uku da kan buɗe tsawon sa'a 24, tun daga dare ya zuwa wayewar gari.
Na shiga kantin sayar da askirim. A nan na ga jerin na'urorin sanyaya kaya maƙare da askirim iri-iri, amma babu jami'in tsaro ko wani mai kula da kantunan, kawai idan ka zaɓi abin da kake so sai ka biya da kanka. Abin da na yi kuwa kenan, na ɗauka na biya kafin in bar wurin.
A wannan ginin kuma akwai wasu kantunan sayar da kayan kwamfuta da abincin dabbobi da ma abincin Japanawa da ake kira sushi. Dukan su kuwa ban ga ko da mutum guda na saka ido da sunan tsaron su ba.
Ko a tsakiyar gari inda ake samun cin koson jama'a babu masu tsaron kantuna a mashaya.
"Idan dai mutum na son ya buɗe wurin sayar a kayan sha kamar barasa da lemunan kwalba a irin waɗannan, to dole sai na nemi masu kula da wurin 12 zuwa 15, amma mutum biyu ne kawai ke kula min da su", in ji Kim Sung-rae, mutumin da ke da kantin na Sool 24, wanda ake sayar da barasa har daga dare zuwa safe. Ya ce hakan kan ba shi damar da zai fuskanci wani kasuwaci na daban.
Ya taɓa tafiyar da wata mashaya a kusa da wurin, amma da ya ga kuɗin da ya ke samu ba su kai adadin da ya ke muradi ba, sai ya juya ga kantunan da ba su da mai kula da su - inda a yanzu kuɗin shigar da ya ke samu ya ƙaru.
Ƙarancin haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
Gomman shekaru da ƙasar Koriya ta Kudu ta ɗauka ba tare da 'yan ƙasar na ci gaba da haihuwa ba, ya sa kusan kowa na da arziki abin da ya sa kowa ke da ikon cin gashin kansa.
Ita ce ƙasar da ke da ƙarancin ƙaruwar jama'a, inda adadin 'ya'yan da mace kan haifa a duk rayuwarta - 0.72 ne a shekarar 2023 kafin ya ɗan ƙaru zuwa 0.75 a bara.
A bisa al'ada, ana buƙatar adadin haihuwar yara a ƙasa ya zama kashi 2.1 wanda rabon da Koriya ta Kudu ta samu hakan tun a 1982. Wannan kuma ya sa yawan masu aiki a ƙasar ya ragu, yayin da tun a shekarar 2000 albashi mafi ƙanƙanta a Koriya ta Kudu ke ƙaruwa.
"Ni ma babban dalilin da ya sa na zaɓi tafiyar da kanti maras mutum shi ne ƙaruwar yawain albashin. Akwai zaɓi biyu game da wannan ƙalubale: ko dai ka saka saƙago [robot] ko yi da kanka - sannan akwai wada ba sai ka sa kowa ba," in ji Mista Kim.
Ya zama dole masu kasuwanci kamar Mista Kim su biya dala 7 duk sa'a ɗaya ga ma'akata.
Saka saƙago[robot] na buƙatar kuɗi da yawa da kuma fili, don haka sai ya zaɓi buɗe kantunan da ke tafiyar da kansu.
![Wani mai aiki a ma'aikatar sayar da gahawa, na saka kofunan gahawa akan saƙago [robot] da ke raba shayoin na gahawa ga mutane](https://ichef.bbci.co.uk/ace/ws/640/cpsprodpb/2077/live/2f3010c0-1ab4-11f0-a455-cf1d5f751d2f.jpg.webp)
Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu kan ce matasa da ke tasowa a yanzu ba su son yin aiki irin na amfani da kwamfuta, a ganin su aiki ne mai wahala da haɗari ga kuma ɓata lokaci.
Sai kuma ayyukan da suka shafi na ƙarfi kamar na ƙere-ƙere da aikin gona da sauran waɗanda a yanzu ake ganin kamar ba a buƙatarsu.
"Matasa sun fi son zama cikin birabe, inda za su ƙirƙiri nasu sana'o'i, su samu jari na kansu sannan su nemi aikin da ke da albashi mai tsoka," in ji Cho Jun-hun.
Mista Cho dai ɗan majalisar dokoki ne a jam'iyya mai mulki ta ƙasar, kuma mamba ne a Kwamitin Cigaban ilimi na majalisar dokokin.
Cibiyar Bincike akan Tattalin Arzikin Koriya, mai zaman kanta, na hasashen cewa nan da shekaru 20 masu zuwa akwai yuwar kashi 43 cikin ɗari na gurabun aiki na fuskantar barazanar ɓacewa inda irin waɗannan ayukan da ba mutane ke yi ba na maye gurbinsu.
Hakan kuwa na nufin ƙara samun buɗi ne ga mutae irin Kwon Min-Jae, shugaban kamfanin Brownie, wanda ke amfani da saƙago a maimakon mutane wajen tafiyar da ayukansa. Ya soma tafiyar da kamfanin lokacin da annobar Korona ta zo ƙarshe a 2022.
"Mu kan tafiyar da kasuwancinmu ba tare da masu tsaron sana'ar ba kamar wankin tabarmi ko darduma da kantunan askirim da kafe da sauran irin waɗannan kantunan," ya shaidawa BBC.
"Muna da ma'aikata tsayayyu daga yankinmu da kullum kan zaiyarci kantunan nan. Babban abin da muka fi mayarwa hankali ba kantunan ba ne, albashi ne. Sun fi son su biya mu dala 100 ko dala 200 a wata domin mu kula musu da waɗannan kantuna".
Mista Kwon ya ce ya fara da shaguna biyu kawai, amma yanzu ya mallaki fiye da 100.
Ƙarancin sata
Ba a cika samun laifukan sata a Koriya ta Kudu ba, wannan ma ya taimaka wajen samar da kantunan da ba mutane a cikinsu.
''An sha samun lokutan da mutane suka manta ba su biya kuɗin kayan da suka saya ba, amma daga baya su kira ni don su biya kuɗin. Ban sani ba ko haka abin ya ke a wasu kantuna, amma dai a nan matasa ba su jin fargabar su bar walet ko wayoyinsu har su dawo wannan ba bain damuwa ne ba," in ji Mista Kim.
Ya ce wasu lokutan akan ɗan samu hasara nan da can sai dai ba ta kawo masa cikas ko faɗuwa ga sana'arsa.
"Ba na tsaya lissafin me aka sace min, ni ba na ma yin hasarar kuɗi, don haka ba babbar damuwa ce ba. Ribar da akan samu tafi hasarar yawa ta kowane hali, kuma idan na ce zan sa mai duba min faɗuwar za ta fi abin da ake samu matsayin riba".
Ci gaban kimiyya na ƙara buɗe hanyoyin sabbin ayuka kamar tuƙa mota zai zama wani tsohon yayi tun daga lokacin da mota mai tuƙa kanta ta cika kasuwanni.
Daga shekarar 2032 an yi hasashen cewa Koriya ta Kudu za ta buƙaci fiye da ƙarin ma'aikata 890,000 domin tafiyar da dogun muradin gina tattalin arzikin ƙasar da ƙarin kashi 2 cikin ɗari.
Wasu ƙungiyoyi kamar Ƙungiyar Ma'aikatan Koriya ta Mart, sun nuna damuwa game da makomar neman aiki a ƙasar, amma waɗansu kamar masu kantunan da ba su da matsara irin Mista Kim na da yaƙinin cewa za a iya samun ƙaruwar ci gaban tattalin arziki nan gaba.











