Yadda ake samun karuwar masu fama da kansar huhu a duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Theres Lüthi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
- Lokacin karatu: Minti 8
Adadin masu fama da kansar huhu a tsakanin mutanen da ba su taba zukar taba sigari ba na karuwa. Cutar ta bambanta da kansar daji da ake samu sakamakon shan taba, to mene ne abin da ke janyo ta?
Martha ta fara jin cewa wani abu na damunta lokacin da yanayin tarinta ya sauya kuma majinar da ke fita idan ta yi tarin na kara yin kauri da yauki.
Likitocinta sun ce tana fama da wata cuta da ba a cika gani ba wadda kuma take haifar da radadi a huhunta. "Kada ki damu, tabbas haka ne," aka shaida mata.
Bayan da aka dauki hoton huhunta an ga wata inuwa a jikin huhun. "Abin da ya kara haifar mata da mugun ciwo," in ji Martha.
"Da farko an fara yi mata gwajin duka jikinta ta hanyar amfani da na'urar daukan hoto ta CT Scan, sai kuma aka yi mata gwajin da ake amfani da dogon bututu domin haska hanyar da iska ke fita a jikinta.
Bayan cire ciwon, kusan wata hudu bayan da ta kai rahoton alamomin da take ji ga likitanta, an gano tana dauke da kansar huhu mataki na IIIA. Shekarar Martha 59 a duniya.
"Na kadu sosai," in ji Martha. Duk da cewa tana kunna sigari a lokutan shagali, ba ta taba kallon kanta a matsayin mai zukar taba ba.
Kansar huhu ita ce nau'in kansa da aka fi fama da ita a duniya kuma ta fi janyo mace-macen da ke da nasaba da cutar daji.
A 2022, kimanin mutum miliyan 2.5 aka gano suna dauke da cutar kuma sama da mutum miliyan 1.8 ne suka mutu sanadiyyar kansar huhun.
Duk da cewa masu shan taba sigari sun fi kamuwa da kansar huhu a fadin duniya, yawan shan taba na raguwa tsawon shekaru da dama.
Yayin da yawan masu shan tabar ke kara raguwa a kasashe da dama, yawan masu kansar huhu tsakanin wadanda ba sa shan taba kuma yana karuwa.
An fi ganin masu kansar huhu a tsakanin kashi 10 da kashi 20 cikin 100 na mutanen da ba su taba shan taba ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Kansar huhu a mutanen da ba su taba shan taba sigari ba ta bambanta da wadanda ke fama da cutar kuma suka kasance masu ta'amali da tabar," in ji Andreas Wicki, wani likitan kansa a asibitin koyarwa na jami'a da ke Zurich a Switzerland.
Ya yi bayanin cewa "idan muka ga masu shekaru 30 zuwa 35 da cutar kansar huhu, galibi wadanda ba su taba shan taba bane,".
Wani bambancin shi ne a irin hanyar da aka gano kansar. Zuwa shekarun 1950 da 1960, nau'in kansar huhu da aka fi gani ita ce wadda take fitowa daga kwayoyin da ke wajen huhu da ake kira squamous cell carcinoma.
Kansar huhu tsakanin mutanen da ba sa shan taba tana somawa ne daga kwayoyin da ke fitar da majina - wadda a yanzu ita ce nau'in da aka fi gani na cutar kansar huhu a tsakanin masu shan taba da wadanda ba sa sha.
Kamar sauran nau'ikan kansar huhu, ita wannan ba a cika gano ta da wuri ba. "Idan aka samu inda cutar ta kama ya boye a wani waje cikin huhu, ba za a iya gani ba," in ji Mista Wicki.
Alama ta farko da ta hada da yawan tari da ciwon kirji da fitar da sauti yayin numfashi, galibi ba sa bayyana har sai inda cutar ta taba ya girma ko kuma ya yadu.
Alaka mai karfi tsakanin shan taba da kansar huhu na iya sa wadanda ba sa shan taba su iya danganta alamomin ga wasu abubuwan na daban, in ji Wicki. "Akasarin kansar huhu a tsakanin wadanda ba sa shan taba an fi gano ta a mataki na 3 ko 4."

Asalin hoton, Getty Images
Kansar huhu a tsakanin mutanen da ba su shan taba abu ne da aka fi gani tsakanin mata. Matan da ba su taba shan taba ba sun fi mazan da suma ba sa sha saurin hadarin kamuwa da kansar huhu.
Kwayoyin halittar masu kansar huhu da ba su taba shan taba ba suna da adadin kwayoyin da ke rikida wadanda ka iya zama sanadin kansar, in ji Wicki.
Wadannan sauye-sauyen na kara girman ciwon,. Dalilan da ke sa aka fi ganin irin wannan rikida ta kwayoyin halittar a tsakanin mata musamman yan Asiya, abu ne da har yanzu babu ciokakken bayani a kai.
Akwai wasu hujjoji da ke cewa sinadaran hormones na iya taka rawa, da wasu nau'i na kwayoyin halittar gado da ke shafar sinadarin estrogen da aka fi gani a kudancin Asiya.
Sakamakon gano rikidar da kwayoyin halitta ke yi da ka iya janyo kansar huhu a tsakanin marasa shan taba, masu hada magunguna sun fara yunkurin samar da maganin da zai rika toshe ayyukan wadannan kwayoyin.
A shekarun baya-bayan nan, an kara kaimi don magance wannan matsala an kuma samar da sabbin magunguna da ake iya samu a kasuwa.
Hakan ya sa aka samu ci gaba wajen iya hasashen kamuwa da cutar. Mista Wicki ya ce " a yanzu akwai marasa lafiyar da ake kula da lafiyarsu tsawon sama da shekara 10.,
Wannan wani mataki ne na ci gaba idan muka duba cewa yiwuwar mutum ya tsira yana kasa da wata 12 da suka gabata kusan shekaru 20 baya."
Da yawan masu kansar huhu da ake gani tsakanin wadanda ba sa shan taba, masana na ganin ya zama dole a samar da dabarun kariya ga masu fama da matsalar.
Misali, bincike ya nuna sinadarin radon da masu shakar hayakin taba sigari duk da ba sa sha na kara hadarin kamuwa da kansar huhu tsakanin wadanda ba sa sha.
Sannan yawan shakar hayaki daga girke-girke ko kona katako ko gawayi a wuraren da babu isasshen wajen fitar iska na iya kara hadarin kamuwa da cutar.
Saboda mata sun fi zama a gida, sun fi fuskantar hadarin shakar irin wannan hayaki mai illa. Sai dai gurbatacciyar iska a wajen da iska ke gaurayawa ta fi zama muhimmin dalili na samun kansar huhu.

Asalin hoton, Getty Images
Gurbatacciyar iska ita ce hanya ta biyu mafi janyo kansar huhu bayan shan taba. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mutanen da ke zaune a wuraren da ke fama da gurbatacciyar iska sun fi fuskantar barazanar mutuwa sakamakon kansar huhu a kan sauran mutane.
Yadda gurbatacciyar iska ke iya janyo kansar huhu a tsakanin wadanda ba sa zukar taba ya zama wani abu na masu bincike suka mayar da hankali a kai a cibiyar Francis Crick da ke Landan.
"Idan muka yi tunanin sinadaran da ke yawo a muhalli, muna tunanin galibi suna janyo rikidewar kwayoyin halittar gado," in ji William Hill, wani mai bincike a cibiyar nazari ta Francis Crick.
Hayakin taba misali yana illata kwayoyin halittar gado abin da ke janyo kansar huhu. " Sai dai bincikenmu a 2023 ya bayyana cewa sinadarin iska ta PM2.5 bai cika janyo rikidewar kwayoyin halittar gado ba amma yana kara kuzarin kwayoyin halittar da ke rikida wadanda suke cikin huhunmuu, wanda ke sa su zama matakin farko na kansar huhu."
Alakar da ke tsakanin gurbatacciyar iska da kuma kansar huhu ba abu ne sabo ba. A tarihi wani littafi da ya samar da alaka tsakanin shan taba da kansar huhu a 1950, marubutan sun ce samun gurbatacciyar iska sakamakon kona wasu abubuwa na iya zama dalili.
Sai dai zuwa yanzu, tsare-tsare sun mayar da hankali kan yadda za a yaki shan taba sigari. Amma bayan shekara 75, ana yin duba kan batun gurbatacciyar iska.
Matakin gurbacewar iska a Turai da Amurka ya ragu a shekarun baya-bayan nan. Amma ba a fara ganin tasirin wadan nan sauye-sauye kan kansar huhu ba.
"Watakila ya kan dau shekaru 15 zuwa 20 kafin a fara ganin tasirin sauye-sauyen a yawan kansar huhun amma ba mu da tabbaci," in ji Christine Berg, wata tsohuwar likitar kansa a cibiyar nazarin cutar kansa ta kasa da ke Maryland a Amurka. Sauyin yanayi shi ma na iya yin tasiri a gaba.

Asalin hoton, Alamy
A gaba, adadin mace-mace sanadin kansar huhu sakamakon shakar gurbatacciyar iska na iya karuwa a kasashe kamar Indiya inda matakin gurbatacciyar iska ya kai kololuwa, a cewar WHO.
A Birtaniya, mutum 1,100 sun kamu da wani nau'in cutar kansa pulmonary adenocarcinoma sabod shakar gurbatacciyar iska a 2022, a cewar wani nazari da hukumar IARC ta gudanar.
"Amma ba duka wannan ya shafi mutanen da ba su taba shan taba ba," in ji Harriet Rumgay, wadda ta ba da gudunmawa a nazarin.
Wadanda ba su taba shan taba sigari ba na iya rayuwa da kansar huhu sakamakon ci gaba da aka samu wajen magani.
An gano cewa Martha tana dauke da nau'in rikidar kwayoyin halitta na ECFR kuma tana shan maganin da ke rage rikidar tun bayan da aka gano tana dauke da cutar shekaru uku da suka gabata.
Maganin na da illa kamar yawan gajiya da ciwon gabbai da matsalolin fata. Ba abu ne mai sauki ka samu daidaito tsakanin hadari da kuma alfanun shan maganin ba da kuma kula da lafiyarka, in ji ta.
Sai dai maganin yana da tasiri. "Ana samun sauyi a yadda ake alakanta cutar da mace-mace kuma hakan abu ne mai kyau."











