Bayanai dangane da kansar ƙasan mafitsara da ta kama Shugaba Biden

Asalin hoton, Getty Images
Tun dai bayan samun labarin kamuwar tsohon shugaban Amurka, Joe Biden da cutar kansar ƙarƙashin mafitsara, jama'a ke ta neman sanin haƙiƙanin cutar.
Bayan gwaji aka tabbatar ya kamu da mummunan nau'in cutar kansar ta ƙasan mafitsara da ta fara yaɗuwa zuwa kashinsa.
To sai dai likitocin sun ce duk da munin nau'in kansar sauyin da ake samu na jikin mai ɗauke da ita ba zai hana yin maganinta da saurin karɓar sauyin ga jikin ɗan adam ba.
Mece ce kansar mafitsara?
Shafin Inshorar Lafiya na Burtaniya, NHS, ya bayyana kansar mafitsara wani ɗan ƙullutu da girmansa bai wuce na goro ba, ke fitowa ƙarƙashin jakar fitsari. inda yake mamaye hanyar mafitsarar - wadda ke ɗaukar fitsari daga cikin jakar ajiye fitsari zuwa waje.
Saɓanin sauran nau'in cutar kansa da ake iya dakatar da ƙwayoyin da suke haddasa cutar yaɗuwa, kansar mafitsara tana girma ne a hankali, inda za ta iya ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da nuna alamu ba.
Masana sun bayyana cewa galibi waɗanda suka fi shiga haɗarin kamuwa da cutar kansar mafitsara maza ne.
Akan kuma samu namiji ɗaya cikin tara da ke kamuwa da cutar, amma kuma mutum ɗaya kaɗai cikin 39 kan mutu da cutar.
Kusan kashi 80 bisa ɗari na mazan da suka kai shekara 80 na da ƙwayoyin halittar kansar a mafitsararsu.
Bayan kasancewa maza, akwai wasu dalilai da kan haifar da cutar ta kansar mafitsara.
Akwai dalilai kamar na shekaru, da yanayin abinci, da ƙiba da tarihin cutar daga cikin dangi, da kuma yadda mutum yake tafiyar da rayuwarsa.
Alamomin kansar mafitsara
Cutar na da alamomi masu dama amma fitattu daga cikinsu sun haɗar da:
- Jin fitsari a kai- a kai - musamman cikin dare.
- Jin zafi gabanin fara fitsari.
- Rashin ƙarfin fitar fitsari tare da ɗaukar tsawon lokaci yana fita.
- Cakuɗuwar jini da maniyyi a cikin fitsari.
Waɗannan alamomi na kamanceceniya da wasu da cutuka da dama ke haifar da su, to amma yana da matuƙar muhimmanci a tuntuɓi likita idan aka ga irin waɗannan alamomi.
Hanyar gano cutar da wuri
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana kimiya a Birtaniya sun ce sun gano cewa ɗaukar hoton cikin jikin mutum da ake kira MRI, ya fi saurin nuna kansar mafitsarar maza fiye da gwajin jini.
Binciken ya tabbatar da cewa hanyar gano cutar kansa ta amfani da ɗaukar hoton jikin mutum ya fi gano alamomin cutar kansa.
Na'urar daukar hoto ta MRI kan ɗauki hoton alamomin cutar kansa da gwajin jini na PSA ke kasa ɗauka.
A halin yanzu babu wata cikakkiyar hanyar gano cutar, saboda ana kallon hanyar gwajin jini ta PSA a matsayin wadda ba za a iya dogara da ita ba, duk kuwa da cewa ana amfani da ita wajen gano cutar tsakanin mazan da suka haura shekara 50.
Masu sabon binciken sun bayar da shawarar yin amfani da hanyar daukar hoton jiki ta MRI domin gano cutar.
Sabon binciken da aka wallafa a shafin jaridar BMJ da ke bincike tare da lalubo mafita kan batutuwan da suka shafi al'umma ya nuna maza sama da 300,000 ne tsakanin shekara 50 zuwa 75 aka yi gwajin gano cutar ta hanyar amfani da MRI a asibitin koyarwa da ke Landon.
Daga cikin mutum 303 da aka yi wa gwajin, an gano cewa mutum 48 na ɗauke da cutar, inda mutum 25 daga cikinsu, suka fara karɓar magani.
Fiye da rabin mazan da aka gano suna ɗauke da cutar ta hanyar gwajin MRI, hanyar gwajin jini ta PSA ba ta gano suna ɗauke da cutar ba.
Shugaban binciken Farfesa Caroline Moore, ya ce ''sakamakon bincikenmu ya gano cewa hanyar gwaji ta MRI na da inganci wajen gano ƙwayar cutar da wuri''.
Ko ana maganin kansar mafitsara?
Akwai hanyoyi da dama da likita zai iya bayar da shawara a kai.
Idan kansar ba ta ci ci jiki sosai ba kuma ba ta nuna wasu alamu ko kuma ba ta yaɗuwa da gaggawa, to ana iya sanya idanu a jira har a ga abin da zai faru.
Akwai yanayin da ake iya warkar da kansar ƙasan mafitsara ta hanyoyi kamar tiyata da gashi da kuma wani lokacin akan daƙile bazuwar cutar ta hanyar sinadarai masu aike saƙo ga ilahirin jikin ɗan adam.
Bugu da ƙari, akwai yiwuwar a iya lalata ƙwayoyin kansar ta hanyar amfani da tsananin sanyi (cryotherapy) ko sauti tsanani (ultrasound)











