Biden ya kamu da kansar mafitsara

Joe Biden

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya kamu da cutar Kansar mafitsara kamar yadda ofishinsa ya fitar da sanarwa.

Tsohon shugaban da iyalansa na nazari kan matakin dauka na maganin cutar tare da kwararrun likitoci.

A sanarwar da ofishin Mr Biden ya fitar ya ce ya je asibiti domin yi masa gwaje-gwaje sakamakon matsalar da ya ke samu wajen yin fitsari, anan ne likitoci suka gano akwai wani kullutu a marainarsa.

Bayan karin gwaji aka tabbatar ya kamu da mummunar nau'in cutar kansar mafitsara da ta fara yaɗuwa zuwa kashinsa.

Likitocin sun ce duk da munin nau'in kansar amma sauyin da ake samu na jikin mai dauke da ita ba zai hana yin maganinta da saurin karbar sauyin ga jikin dan adam ba.

Rahotanni sun ce iyalan Mr Biden na duba nau'in maganin da za a yi ma sa tare da shawarar likitocinsa.

Tuni jiga-jigan jam'iyyar Democrat a sassan Amurka suka fara wallafa sakonnin karfafa gwiwa.

Shugaba Trump ya ce bai ji dadin labarin halin da Biden ke ciki ba, ya na kuma yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.

Shima tsohon shugaban Amurka kuma na hannun daman Mr Biden Barrack Obama ya wallafa a shafinsa na X cewa shi da maidakinsa Mixchelle na tare da iyalan Biden a irin wannan lokaci.

Babu wanda ya yi namijin kokari domin gannin an samar da maganin cutar kansa kamar Biden, ya kuma yi imanin zai cinye wannan jarabawa, kuma su na yi masa addu'ar samun sauki, in ji Obama.

Mr Biden mai shekara 82 a duniya ya sauka daga mukaminsa a watan Junairu, kuma shi ne shugabn Amurka da ya fi sauran shekaru a tarihi.

Bisa radin kan shi ya ce ba zai tsaya takarar shugaban kasa a wa'adin mulki na biyu ba.

Bayan kalubalen da ya dinga fuskanta a muhawarar da suka fafata da shugaba Donald Trump wanda shi ma ya nuna shakku kan cancancar jagorancinsa.