Me ya sa matasa ke yawan kamuwa da cutar daji?

Luisa Toscano, wata uwa mai shekara 38 daga Brazil, ta ce ta yi mamaki da aka shaida mata tana fama da cutar daji

Asalin hoton, Luisa Toscano

Bayanan hoto, Luisa Toscano, wata uwa mai shekara 38 daga Brazil, ta ce ta yi mamaki da aka shaida mata tana fama da cutar daji
    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin da Luisa Toscano ta gano cewa tana da kansar mama, ta yi mamaki.

"Kwata-kwata ban yi tsammanin haka ba," in ji matar, wadda ta kasance yar Brazil kuma mahaifiya ga ƴaƴa biyu.

"Ina matashiya, da ƙoshin lafiya - bai kamata hakan ta faru da ni ba. Ban taɓa tunanin zan yi fama da cutar daji ba a rayuwata.

An gano Luisa tana ɗauke da kansar mama da ta kai mataki na uku a Maris ɗin 2024, abin da ke nufin, cutar ta kai wani babban mataki.

Ta shafe kusan wata biyar ana yi mata gashi, sannan aka yi mata tiyata don cire ɓangaren mamanta da ke da ciwon. Luisa ta kammala waɗannan matakan a watan Agusta amma dole tana buƙatar ta ci gaba da shan magunguna domin kare dawowar ciwon.

Ta ce abin godiyar shi ne ba a cire min mamana gaba ɗaya ba. Abin da na yi wahalar jurewa shi ne yadda gashina ya zube. Abin ya faru cikin ƙanƙanin lokaci. Idan na kalli madubi, sai na ji tsoro, kuma hakan ya shafi 'ya'yana suma.

Labarin Luisa yana bayyana yadda cutar daji ke yaɗuwa a duniya, ana gano cutar a jikin matasa da a danginsu babu wanda yake da ita.

An fi ganin cutar daji a tsakanin manya saboda dalilai da suka shafi muhalli da shekaru.

Don haka ne ya sa likitoci da daɗewa suka alaƙanta cutar daji a jikin matasa ga dalilai na gado.

Sai dai babu wata dangantaka da gado a wasu masu cutar da dama kamar Luisa.

Ƙaruwar masu cutar daji

Hoto da ke nuna wata mata ɗauke da kansar mama.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cewar wani rahoto, kansar mama ta yaɗu sosai

Wani bincike da aka wallafa a mujallar BMJ Oncology ya gano cewa gano cutar daji a jikin 'yan ƙasa da shekara 50 a duniya ya ƙaru da kashi 79 cikin 100 tsakanin 1990 da 2019, inda kuma aka samu karin mace-mace sanadiyyar cutar ta daji da kashi 28 cikin 100.

Binciken ya yi nazari kan nau'ikan cutar daji 29 a sassan ƙasashe 204.

Kazalika, wani rahoto da aka wallafa a mujallar 'The Lancet' ya gano cewa adadin masu fama da nau'ika 17 na cutar daji ya ƙaru a Amurka, musamman tsakanin waɗanda aka haifa tsakanin 1965 da 1996.

Wani sabon rahoto na 'American Cancer Society' ya bayyana cewa yawan masu kansar mama tsakanin farar fata 'yan ƙasa da shekara 50 ya ƙaru da kashi 1.4 cikin 100 a shekara, idan aka kwatanta da ƙasa da kashi ɗaya cikin 100 na waɗanda shekarunsu suka haura 50 tsakanin 2012 da 2021.

Sauran nau'ikan cutar daji kamar waɗanda suka shafi hanji sun ƙaru a tsakanin matasa, in ji rahoton mujallar 'BMJ Oncology'.

Abubuwan da ka iya janyo cutar

Luisa Toscano with her two children, after the completion of her treatment. They are all smiling.

Asalin hoton, Luisa Toscano

Bayanan hoto, Luisa ta ce goyon bayan da take samu daga iyalinta ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin da take da kansar mama
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu bincike na fafutukar gano dalilai yayin da binciken 'The Lancet' ke gargaɗin cewa yaɗuwar cutar na iya haifar da koma baya ga ci gaban da aka samu na tsawon shekaru a yaƙi da cutar.

Zuwa yanzu, dalilai na abinci kamar yawan cin jan nama da shan sinadarin sodium da ƙarancin 'ya'yan itatuwa da madara - tare da shan barasa da taba, suna daga cikin abubuwan da ake zargin suna haifar da cutar, a cewar rahotannin 'BMJ Oncology' da kuma ' The Lancet'.

Sannan ana danganta ƙibar da ta wuce kima da ƙara haifar da haɗarin kamuwa da cutar, in ji WHO.

Rahoton 'The Lancet' ya ce 10 cikin nau'in kansa 17 da ke ƙaruwa a tsakanin matasa a Amurka sun danganci ƙibar wuce kima har da cutar dajin da ta shafi ƙoda da mahaifa da hanta da mafitsara.

Masana kimiyya na duba wasu abubuwan da ka iya haddasa cutar. Wasu sun ce yawan kallon haske na na'ura da kuma fitulun kan hanya na iya sauya sinadaran da ke kula da jikin ɗan'adam abin da ke ƙara haɗarin kamuwa da kansar mama da ta mafitsara da ta hanji.

A Yunin 2023, likitan fiɗa Frank Frizelle a New Zewaland ya nemi a yi bincike kan ko ɓurɓushin roba na taka rawa a kansar hanji.

Sauran masu bincike sun ce abincin da aka yawaita sarrafa shi suma suna iya haifar da matsala.

Yawan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta - da kashi 45 cikin 100 a duniya tun 2000 - musamman a tsakanin yara, shi ma na iya zama dalilin janyo matsalar, in ji wasu masu bincike.

Wata tawagar ƙwararrun Italiya sun shaida cewa hakan na da alaƙa da kansar huhu da wasu nau'ikan cutar ta daji.

Sannan ƙara tsayi na iya taka rawa wajen ƙara yawan masu cutar daji, in ji farfesa Malcolm Dunlop, a jami'ar Edinburgh da ke Scotland.

Dakta Dunlop, ɗaya daga cikin manyan ƙwararru kan cutar daji, na ganin cutar na samo sali ne daga abubuwa da dama a maimakon dalili ɗaya, amma gano su yana da wahala.

A cewar cibiyar kula da cutar daji ta Amurka, kashi 80 cikin 100 na mutanen da aka gano na ɗauke da cutar sun kai shekara 55 zuwa sama.

Kira ga likitoci

Dr Alexandre Jácome wears a black suit with a white shirt. He has short dark hair and is looking serious.

Asalin hoton, Brazilian Society of Clinical Oncology

Bayanan hoto, Dakta Alexandre Jácome

Sai dai wannan lamarin ya janyo manyan ƙungiyoyi kamar ta masu yaƙi da cutar daji ƙara wayar da kan likitoci game da cutar daji a tsakanin matasa.

"Idan wanda shekarunsa suka haura 60 ya bayyana yana kashi da ƙyar, yana fama da gajiya da kumburin ciki, ya kamata likitoci su ɗauki lamarin da gaske sannan su bayar da shawarar yin gwaji. Sai dai ga wanda yake ɗan shekara 30, za a iya watsi da waɗannan alamomin," in ji Dakta Alexandre Jácome, masani kan cutar daji.

Dakta Dunlop ya kuma bayyana damuwa game da tasirin daji na tsawon lokaci.

"Matasa da ke fama da cutar daji na iya zama da haɗarin har shekarunsu su ja," a cewar shi.

Cutar daji na tattare da darasi

Photo illustration of a cancer cell

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cutar daji ta fi kama mutanen da shekarunsu suka ja saboda dalilai da dama

Luisa ta ce babban darasin da ta koya shi ne zama a yanayin da take ciki - da daɗi ba daɗi. Idan ɓacin rai ya zo, ina rungumar shi. Idan na samu ƙwarin jiki, sai na ji daɗin waɗannan lokutan, sanin cewa suma za su wuce.

Shawararta ga wasu ita ce: A bi a sannu. Ku kula da jikinku - wasu ranakun, abin da ya fi dacewa ka yi shi ne ka huta.