Abin da ke sa matasa yin furfura da wuri da yadda za a kiyaye

Ashley Sukru ta ce samun furfura tun tana da shekara 14 ya ɗaga mata hankali, amma yanzu ta fara bayar da labarin ne domin ta samu kwanciyar hankali

Asalin hoton, Ashley Sukru

Bayanan hoto, Ashley Sukru ta ce samun furfura tun tana da shekara 14 ya ɗaga mata hankali, amma yanzu ta amincewa da yanayi da take
    • Marubuci, Esther Kahumbi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ashley Sukru tana ƴar shekara 14 ne lokacin da wata ƙawarta ta hango farin gashi a kanta, wanda tun daga ranar tunaninta ya sauya kan yadda take ganin kanta.

"Kawai sai na ji wani iri, ina mamaki ta yaya zan samu furfura, ni da shekarata 14 kawai."

"Na tuna a lokacin sai na koma gida ina ta sake duba gashina, ina jin kunya da damuwa."

Ashley ƴar asalin Canada ce wadda yanzu shekarunta 28, ta ce a lokacin sai ta roƙi iyayenta su ba ta damar amfani da dayis wajen mayar da gashin baƙi.

Shin ana fara furfura tun ana yara?

Masana sun ce ƙwayoyin halitta na gado ne suke da alhakin mayar da gashi fari, kuma su ɗin ne suka nuna yaushe mutun zai fara furfura.

Bincike ya nuna ita ma Ashley gado ta yi, domin mahaifiyarta ta fara furfura ne tun tana da shekara 14, sannan kakarta ta yi furfura a shekara 17.

Likitoci sun ce yanzu ana samun ƙaruwar ƙananan yara da suke fara furfura, kuma suna shiga damuwa - yawanci masu tsakankanin shekara 20 zuwa 30.

Idan mutum na cikin ƙoshin lafiya sosai babu wata matsala, ya kamata ne mutanen yankin Caucasia wato yankin ƙasashen Rasha da Georgia da Azerbaijan da Armenia da Turkiya da Iran su fara furfura a tsakankanin shekara 35, amma ƴan Afirka da Asia, sukan haura haka da kusan shekara 10.

Duk wata furfura da ta fito kafin wannan lokacin, to ta yi saurin fitowa - wato idan mutanen yankin Caucasia suka fara furfura kafin shekara 20, ko kuma ƴan Afirka da Asiya su fara furfura 25 zuwa 30.

Tantanin halittar melanocytes ce ke kula da tsirowa da ma kalar gashin mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tantanin halittar melanocytes ce ke kula da tsirowa da ma kalar gashin mutum

Yaya ake fara furfura?

Gashi na tsirowa ne daga fata da tantanin halittar jikin ɗanadam da ake kira melanocytes.

Melanocytes na fitar da sinadarin melanin biyu - eumelanin, wanda ke da alaƙa baƙin gashi, sai kuma pheomelanin da ke da alaƙa da jan gashi ko ruwan ɗorawa. Haka kuma tantanin halittar ne ke da alaƙa da yanayin kalar ido da fata.

Wani bincike da masana ƙwayoyin halitta a Jami'ar New York University (NYU) sun gano cewa da zarar gashi ya fara tsufa, melanocyte na ƙaruwa amma yana rage ƙarfe.

Masu binciken sun ce da zarar gashin ya kai wannan matakin, asalin maɓuɓɓugar gashin zai daina walwala, sai ya tsaya cak, wanda zai hana gashin ci gaba da faɗaɗa da ƙarfafa, wanda haken ke janyo gashin ya fara furfura ya fara zama fari ko kalar azurfa.

Yanayin cimaka na da alaƙa da furfura?

Tantanin halitta da ke kula da fata da gashi suna lalacewa ko mutuwa saboda yawan gajiya, kamar yadda masana daga Amurka da Brazil suka gano.

Amma masana sun ce zai yiwu rashin daidaito a cimaka musamman rashin wasu sinadaran abinci masu gina jiki za su iya jawo saurin fara furfura.

Rashin sinadarin vitamin D da B12 da copper da iron da zinc duk suna da alaƙa da saurin fara furfurwa, musamman ma vitamin B12 wanda shi ne kan gaba wajen jawo sauran fara furfura.

"Yawanci ana samun B12 ne daga dabbbi, don haka idan mutum ya fi cin ganyayyaki, to idan ya fara furfura da sauri ina ganin wannan ne zai zama babban dalili," in ji Dr Mezher.

Sai dai masana sun ce yawan amfani da sinadarin zinc da vitami C na jawo tsaiko wajen sarrafa copper a jikin mutum, wanda ke jawo ƙarancinsa, wanda hakan ma zai iya zama sanadi.

Maria Marlowe ta yi gargaɗin yawaitar amfani da magungunan ƙarin abinci masu gina jiki

Asalin hoton, Maria Marlowe

Bayanan hoto, Maria Marlowe ta yi gargaɗin yawaitar amfani da magungunan ƙarin abinci masu gina jiki

Gyara cimaka zai iya mayar da gashin baƙi?

Wani bincike da masana suka yi a Jami'ar Columbia ya gano kalar gashi zai komawa yadda yake a farko da zarar an rage gajiya da wahalar da jiki.

Likitoci sun ce za kuma a iya mayar da gashin yadda yake idan dama asalin rashin abinci mai gina jiki ya jawo canjin.

"Yawancin masu fara furfura da sauri, idan asali daga canjin ƙwayoyin halitta ne, to gaskiya ba zai iya komawa baƙi ba," in ji Dr Mezher.

"Idan muka gano cewa akwai ƙarancin B12, sai mu nomo magungunan da za su maye gurbinsa, haka ma idan ƙarancin copper ne ko vitamin D, duk nemo magungunan da za su maye su ake yi domin mayar da gashin baƙi," in ji Dr Mezher.

"Ko da kuma gashin bai koma baƙi ba baki ɗaya, furfurar za ta ragu sosai, ko kuma ta daina ci gaba."

Sai dai masanan sun yi gargaɗin cewa babu wani tabbataccen maganin da za a ce shi ne maganin furfura.

A shekarar 2020, lokacin da Ashley Sukru take da shekara 23 sai ta yanke shawarar daina sanya kala a gashinta domin barin furfura

Asalin hoton, Ashley Sukur

Bayanan hoto, A shekarar 2020, lokacin da Ashley Sukru take da shekara 23 sai ta yanke shawarar barin furfurarta

A wajen Ashely, yanayin cimaka ba zai canja mata ƙwayoyin halittar gashinta ba, amma dai tunaninta ya canja, inda yanzu take amfani da kafofin sadarwa wajen ilimantar da matasa game da rayuwa da ado da tsufa.

"Lokacin da na fara fitar da bidiyo a TikTok da Instagram sai na ga ashe akwai mata tsararrakina masu furfurwa," in ji ta.

"Ina fata zan zama abin koyi da zan ƙarfafa gwiwar mata domin su amince da furfurar da suke da ita, sannan maimakon mu riƙa ganin furfura a matsayin alamar tsufa da muni, sai mu riƙa ganin furfura a matsayin abar ado."