Zaluntar makiyaya na daga abubuwan da suka ta'azzara matsalar tsaron Arewa - Gwamna Yahaya

Asalin hoton, Gombe state government
Shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin arewacin Najeriya, kuma gwamnan jihar Gombe, ya ce gano dalilan da suka tunzura 'yan fashin daji suka ɗauki makamai, ginshiƙin abu ne a yunƙurin kawo ƙarshen rikicinsu a sassan Najeriyar.
A hirarsa da BBC Gwamna Muhammad Inuwa Yahya ya ce ƙungiyarsu ta amince da kafa wata hukumar haɗin gwiwa kan sha'anin tsaron jihohin arewa, tare da ba da gudunmawar naira miliyan dubu daya duk wata ga duk jihohin arewa 19.
Matakan na cikin ƙudurorin da taron ƙungiyar jihohin arewa ya cimma a farkon wannan mako, sanadin ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga da suka janyo sace ɗalibai da rufe makarantu a jihohi da dama.
Gwamnan na yi bayani kan abin da suke ganin ya janyo ta'azzarar rashin tsaron:
''Akwai talauci da yawa da rigingimu na zamantakewa sannan kuma akwai rashin kiyaye doka, wanda duk sun taru sun haɗu shi ne abin ya ta'azzara ya lalace, yanzu.''
Ya ce, ''Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka farraka yanzu ake shiga daji mutane ne da suka san daji. Kiwo suke yi akasari a daji amma saboda rashin bin doka ya sa babu burtali babu labi babu gandun daji babu gandun kiwo a guraren da suka saba.
''Kuma za ka ga har gefen hanya mutane sun yi shuka to ka ga a garin suna kiwo sun zo sun yi ta'adi suka rasa dukiyoyinsu saboda an dai zaluntar da su suma a wannan lokacin ko daga jami'an tsaro ko daga hukumomin shari'a ko daga mutanen gwamnati, sun cutu.
''To amma kuma wannan bai kamata su kuma ya sa su ɗau doka a hannunsu ba,'' in ji gwamnan.
Ya yi nuni da yadda 'yan bindigan suka ɗanɗana suka ji daɗin satar mutane da suke yi domin karɓar kuɗin fansa, inda suke samun miliyoyin kuɗi ta wannan hanya.
Kuma kasancewar sun kasance babu ilimi da sauran abubuwa na jin daɗin rayuwa da suka sani, ya ce to dole ne sai an tashi tsaye a dawo da su hanya su yi watsi da wannan abin da suke yi.
''Idan yanzu misali mutum ya rasa garkensa sai ya koma daji inda zai yi tafiyar kilomita 50 ko 60 a dare guda, ya zo ya ɗauki mutum ɗaya daga gari ya ja shi ya kai daji, nan kuka yi irin wannan maganar suka gane aka ba su miliyan 5 ko 10.
''Nan kusa ma a wasu guraren har ana cewa miliyan maganar miliyan 50 ko 100 kuma ba a daɗi ba, ba ka tarbiyyantar da su ba ba ka ilmantar da su ba.
''To yanzu ai dole sai an nemi dalilin da za a zauna a gane wane ne mai laifi? Ta yaya za a yi a kyautata don a gyara, in ya so gobe kar haka ta kuma faruwa.'' A cewar Gwamnan na Gombe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yayin taron na ƙungiyar gwamnonin na Arewa, shugaban na su ya ce sun lura kusancin jihohin da rashin ɗaukan matakai na bai ɗaya na daga cikin abin da ke ta'azzara matsalar tsaron ta yadda mutum zai aikata laifi daga wannan jihar ya gudu ya shiga wata.
''Saboda haka muka yanzke shawarar haɗa kai mu ɗauki matakai na bai ɗaya tare da hukuma guda wadda ke da sahalewar gwamnatin tarayya.
''In mun haɗa kuɗi muka sayi kayan aiki muka nemi sahalaewar gwamnati ta tarayya, wadda ita aikinta ne, ba gwamna ko shugaban ƙasar da zai yi farin ciki yana kallo a ɗebe 'ya'ya ka bar shi da tashin hankali.
''Ko kuma mutanensa su shiga cikin tagayyara kuma ya kasance yana cikin annashuwa shi kuma yana jin daɗi. Babu ba wanda yake buƙatar wannan. To amma idan ka samo dalilan aka zo aka ɗauki matakai na baiɗaya to za a samu sauƙi cikin ikon Allah,'' in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa: ''To don haka shi ya sa muka yi shawarar mu ga yadda za mu yi dabaru, mu yi gamayya mu yi hukuma wadda za ta kula da tsaron nan a kowane mataki duk da muna da su a jiha, ya kasance a haɗe gamayyarmu a arewaci muna da hukuma kamar wannan muna aiki tare.''











