Abu uku da gwamnonin Arewa suka cimma kan tsaro

Asalin hoton, BBC GRAB
Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 sun fitar da wasu abubuwa guda 6 da suka ce za su mayar da hankali a kai domin tunkarar matsalar tsaron da ta dabaibaye yankin.
Wannan ya biyo bayan taron da ƙungiyar gwamnonin 19 ta yi a Kaduna wanda aka kammala shi ranar Litinin.
Taron ya samu halartar gwamnoni da sarakunan yankin.
Ƴansandan jiha
Ƙungiyar gwamnonin ba tare da ragin ɗaka ba ta amince da kafa ƴansandan jiha, inda gwamnonin suka shawarci ƴan Majalisar Dokokin Najeriya da ta jihohi na yankin na Arewa da su gaggauta aikin da zai tabbatar da samun ƴansandan jiha.
Haƙar ma'adanai
Ƙungiyar gwamnonin ta ce za ta sharwarci shugaban ƙasa domin ya bai wa ministan albarkatun ƙasa umarnin dakatar da dukkannin ayyukan haƙar ma'adanai a yankin arewacin ƙasar har na tsawon watanni shida domin samun damar tantance aikin.
Hakan zai bai wa gwamnonin jihohin da ake haƙar ma'adan damar tuntuɓa da gano masu ayyukan haƙar ma'adanai da ke yi ba bisa ƙa'ida ba.
Gidauniyar Tsaro
Gwamnonin kuma a tsakaninsu sun amince su samar da wata gidauniya da suka kira Gidauniyar Tsaro ta Arewa domin tunkarar matsalar da yankin ke fuskanta.
Ƙungiyar ta ce kowace jiha ta amince za ta rinƙa zuba naira biliyan guda a asusun, inda za a rinƙa cire kuɗin tun kafin ma ya kai ga asusun jiha.
Sai dai gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su riƙa kashe kuɗin.
Dama dai masana tsaro sun jima suna bayar da shawarar aiki tare tsakanin duka jihohin arewa domin magance matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.
Me ya sa gwamnoni ke son kafa ƴansandan jiha?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yadda gwamnonin Najeriya ke ta nanata buƙatar samar da 'yansandan jiha domin magance matsalolin da suke fuskanta a jihohinsu ya sa wasu na tambayar me ya sa suka haƙiƙance.
Bugu da ƙari, batun ƙirƙiro ƴansandan jiha na daga cikin abubuwan da ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta cimma a ƙarshen taronta kan matsalar tsaro, a Kaduna.
Ana ganin wannan ne dai a yanzu haka ya karfafa wa gwamnatin jihar Nassarawa sanar da kafa rundunar ƴansanda ta jiha.
Masana na ganin cewa babban dalilin da ke sa gwamnoni buƙatar ƴansandan jiha ita ce neman amfani da manyan makamai.
Captain Sadiq Garba mai ritaya wanda masanin tsaro ne dokokin Najeriya ba su yarda mutumin da ba jami'in tsaro ba ya riƙe babban makami ba kamar AK-47.
"Shi ya sa (dokar) samar da ƴansandan na jihohi zai ba su dama su riƙe makamai irin su AK47. Doka ba ta bai wa ƴan sa-kai damar riƙe manyan makamai ba, kuma idan ka ga irin makaman da ƴanta'addan suke riƙewa akwai matsala," a cewarsa.
Captain Sadiq Garba ya shaida wa BBC cewa su kansu ƴan sa-kai ɗin da suke amfani da bindiga babu wata dokar da ta ba su dama.
"Idan aka duba, za a ga suma ƴan sa-kai ɗin babu wani takamamaiman lokacin da aka ba su izini. Kuma in ka zagaya wasu jihohi za ka ga suna amfani da bindigar farauta, wasu kuma da sanda ko gora.
"A jihar Borno aka fara maganar ƴan sa-kai ɗin. Da farko a hankali suka fara, lokacin ba su da bindiga, daga baya suka fara amfani da bindiga. Kuma gaskiya da wahala ka iya gano lokacin da gwamnati ta ce su yi hakan."
Ya ƙara da cewa su ma ƴan sa-kai ɗin an samu wuraren da aka zarge su da cin mutuncin mutane, da zargin kisan gilla a wasu jihohin.
"A maganar bindiga kuma, akwai dokar amfani da manyan bindigogi da ta ce dole sojoji ko ƴansanda na tarayya ne kaɗai za su yi amfani da su. Gaskiya idan aka sakar musu mara akwai matsala," in ji shi.










