Abin da ya sa Sarkin Ingila ba zai nemi afuwa kan cinikin bayi ba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sean Coughlan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Royal correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
''Abu mafi ciwo a tarihinmu na ci gaba da tasowa", in ji Sarki Charles III a lokacin da yake jawabi ga shugabannin ƙungiyar Commonwealth a Samoa, yayin da muhawara kan batun biyan diyya da neman afuwa a kan cinikin bayi ya ƙara tasowa.
Wannan batun ya kasance ɗawainiya da kuma alhakin ya rataya a wuyan Iyalan Gidan Sarautar Ingila, saboda ba ta yadda za su iya raba kansu da duk wani ƙorafi a kan abin da ya faru na bauta saboda alaƙar da gidan ya kasance da ita da cinikin bayi.
Hatta a lokacin taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth, wasu daga cikin shugabannin ƙasashen da cinikin bayin da mulkin mallaka ya fi shafa sun taso da maganar.
To amma ko da Sarkin shi kansa ya yi amanna cewa ya kamata a nemi afuwa ko kuma a biya diyya, ba zai iya yin hakan ba.
Sarakai suna magana ne kan shawarar ministoci- da kuma batun siyasar da ke tattare da wannan magana, dole ne kalamansa su kasance daidai da manufofin gwamnati.
Mako daya da ya wuce fadar gwamnatin Birtaniya ( Downing Street ) ta nuna alamun cewa babu wata afuwa da za a nema ko ƙulla wata yarjejeniya ta biyan diyya daga Birtaniya a wajen taron na Samoa.
"Ba wanda a cikinmu zai iya sauya abin da ya riga ya faru," in ji Sarkin a lokacin da yake jawabi ga shugabannin ƙungiyar Commonwealth, wanda wannan maganar tasa ta yi daidai da kalaman Firaminista Keir Starmer, da ke cewa, '' ba za mu iya sauya tarihinmu ba.''

Asalin hoton, Reuters
A shekarar da ta wuce Sarkin ya nuna takaicinsa da kuma nadama kan abubuwan da aka yi na rashin kyautatawa a lokacin mulkin mallaka.
A cikin kalamai masu ƙarfi fiye da yadda ya yi a lokacin taron Samoa, Sarkin ya yi magana kan abubuwa na rashin kyautatawa da aka yi wa mutanen Kenya a lokacin gwagwarmayarsu ta neman 'yancin kai.
To amma kamar yadda tsarin yake na taƙaita kalamansa ga manufofin gwamnati, babu wata afuwa da ya fito ya nema ƙarara.
Kalaman nasa a iya cewa sun zo kusan daidai da waɗanda tsohon Firaminista Tony Blair ya yi a 2007, inda ya nuna nadama a kan rawar da Birtaniya ta taka a cinikin bayi.
A lokacin an yi ta kira ga Blair da ya nemi afuwa, to amma ya toge, daga baya dai ya ce a iya haƙuri.
Duk da cewa an nuna nadama kan abin da ya faru a bayan to amma hakan ba yana nufin a sa rai da biyan diyya ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A matsayin Sarkin na shugaban ƙasa, shi ne kusan nauyi ya rataya a wuyansa kan bayar da amsa game da wadannan kiraye-kiraye na neman afuwa da kuma maganar biyan diyya ko kuma wasu hanyoyi na magance abubuwan da aka yi na rashin kyautawa a baya. Wannan magana ba za ta kau ba.
Wannan dai abu ne mai wahalar gaske a gareshi to amma zai san yadda zai ɓullo masa, amma duk da haka batu ne na siyasa da ba zai iya sauya ba, kuma maganar biyan diyya kusan abu ne mai wuyar gaske idan aka yi la'akari da kasafin tattalin kuɗin Birtaniya da ke cikin matsi a yanzu.
Wani abu kuma shi ne idan ana batun cewa Birtaniya ce kan gaba wajen ganin an soke bauta, a farkon ƙarni na 19, binciken da malamar tarihi, Farfesa Suzanne Schwarz ta yi ya nuna cewa hatta su kansu iyalan gidan sarautar Birtaniyar kansu ya rabu a kan batun.
Ɗan
Ɗan wan Sarki George III, Yariman Gloucester, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi fafutukar neman hana bauta, inda ya kasance mai gwagwarmayar ganin an daina cinikin bayi har ta kai yana goyon bayan yadda sojojin ruwa na Birtaniya ke tare jiragen ruwa da ke ɗauke da bayi.
To amma kuma ta wani ɓangaren kafin a kai ga cimma wannan muraɗi, ɗan Sarki George III, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi ƙaunar ci gaba da da bautar.

Asalin hoton, Reuters
Akwai yunƙuri a wasu ƙasashe na neman nesanta kai ko bayar da haƙuri kan wannan batu na bauta.
Sarkin Netherlands ya bayar da haƙuri a wani yunƙuri na haɗin gwiwa da Firaministan ƙasar.
To amma ga Sarki Charles da sauran manyan 'yan Gidan Sarautar - batu ne da yake ci gaba da zamar musu alaƙaƙai, musamman ma idan suka ziyarci wata tsohuwar ƙasa da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, ko kuma wani wuri da cinikin bayi ya yi tasiri sosai.
Duk wasu masu tsara tafiye-tafiyen iyalan Gidan Sarautar dole ne su duba yadda za a shirya bikin kaɗe-kaɗe da raye-raye na tarbar sarakin idan sun kai ziyara, kuma hakan na damunsu domin fargabar abin da zai iya faruwa, a ziyarar.
To amma Sarkin wanda ya daɗe yana fuskantar wannan dambarwa ta siyasa tsawon gomman shekaru, ya yi taka-tsan-tsan kamar kullum, a wajen taron Samoa, inda a jawabinsa ya ce:
"Ba wanda a cikinmu zai iya sauya abin da ya faru a baya. Amma za mu iya ƙudurcewa da zuciya ɗaya, aniyar koyar darasi daga abin da ya faru tare da nemo hanyoyi masu kyau na magance rashin daidaiton da lamarin ya haifar."
To amma kuma a jawabin da yawanci ake kallo a kan abin da bauta ta haifar ne - ko da sau ɗaya sarkin bai yi maganar bauta ba sam-sam.











