An gano ginin farko da Ingila ta riƙa ajiye bayin ƴan Afirka

- Marubuci, Favour Nunoo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Accra
An gano ainihin wurin da ake kyautata zaton shi ne wajen ajiye bayi na Ingilishi na farko a Afirka , BBC ta jima tana bincike kan mahimmancin gano wurin a Ghana.
Cikin kulawa, masanin ilimin kimiya na kayan tarihi, Christopher DeCorse, ya baje kayan tarihin da ba kasafai ake yin su ba a kan teburi kusa da wurin tono.
A hankali ya riƙa fito da tsoffin bindigu, bututun shan taba, fasassun tukwane da ƙashin akuya a hankali.
Waɗannan abubuwan da aka tono a cikin ƙasa, na ƙarin haske kan ainihin abin da ya faru a wajen.
"Duk wani masanin ilimin kimiya na kayan tarihi dole ya ji daɗi idan ya sami wani abu irin wannan,"in ji wani farfesa daga Jami'ar Syracuse da ke Amurka ya faɗaɗa murmushi.
Ya ce , waɗanan abubuwan na nuna farkon samuwar wajen aje bayi a Afrika."
Masanin ilimin kimiya na kayan tarihi yana tsaye a kango na farko da aka riƙa aje bayi a Afrika wato , Fort Amsterdam, ya ci gaba da magana cikin ɗaga murya.
A cikin wannan wajen ajiye bayin, akwai wata katanga da ake tunanin tafi komai jimawa a wajen, wanda tawagar farfesa ke bincike a kan hakan.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohuwar taswirar na nuni zuwa ga Fort Kormantine a wannan yanki, misali sunan garin da ke kusa, Kormantse, yana da alaƙa a fili.
Bugu da ƙari, an ba da wani nau'in sunan, Coromantee, ga wasu daga cikin bayin da ke cikin ƙasashen Caribbean da ake tunanin an ɗauke su ne daga wannan wuri kuma daga baya an san su da taka rawa wajen yin tawayen, tare da neman samun ƴanci.
Amma inda ainihin wajen ajiye bayin ya kasance abin hasashe ne, wanda wataƙila yanzu an kawo karshensa.
Tun daga karni na 17, Fort Kormantine yana a gaɓar tekun Atlantika a daidai lokacin da Turawa suka fara sauya ra'ayin su daga cinikin zinari zuwa cinikin mutane.
Ya kasance wani muhimmin lokaci a tarihin shigarsu a Afirka wanda zai yi tasiri sosai a nahiyar.
Binciken da ƙungiyar masu binciken kayan tarihi suka gano na ƙarin haske kan rayuwar waɗannan ƴan kasuwa na farko da abin da suka yi, da kuma waɗanda aka sayar da tasirin al'ummar da ke kewaye da su.
Garuruwan kamun kifi da ke gaɓar tekun Ghana, da suka shahara da kyawawan jiragen ruwa da kuma waƙe-waƙen da masunta ke rerawa, sun kasance cikin firgita da cin zarafin da Turawa suka yi a baya da kuma zaluncin da suka yi.
Dubban ɗaruruwan mutane sun ratsa ta cikin waɗanan ɗakuna kafin a yi jigilar su cikin mummunan yanayi ta tekun.
An gina wajen ajiye bayin na farko wanda aka yi wa laƙabi da Fort Kormantine a turancin ingilishi a shekarar 1631.
Da farko wurin ana cinikayyar zinari ne sai daga bisani suka sauya ra'ayi suka fara cinikin mutane.
An fara cinikin bayi ne a 1663 lokacin da Sarki Charles II ya ba da izini ga Kamfanin Royal Adventurers Trading na Ingila wanda daga bisani ya koma Kamfanin Royal African.
Wannan kamfanin shi ne aka ba izinin shiga da bayi Ingila.
Sai dai bayan shekaru biyu , ƙasar Netherlands ta ƙwace wurin daga hannun Turawan Ingila.
Fort Kormantine, ya taka muhimmiyar rawa a matakin farko na cinikin bayi.
Ya zama ma'ajiyar kayan da ake sayen bayi. Har ila yau, ya kasance ɗan taƙaitaccen wuri ga waɗanda aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na Afirka ta Yamma kafin a tura su zuwa yankin Caribbean don yin aikin gonaki da bunkasa tattalin arziƙin sukarin yankin.
"Ba mu da cikakkun bayanai game da ainihin yadda waɗannan wuraren da aka fara cinikin bayi suke a baya,"in ji Farfesa DeCorse.
Bayan sun ƙwace wajen ne , ƴan Netherlands, suka gina Fort Amsterdam, duk a wurin, dalilin da ya sa kenan ba za a iya gane ainaahin wurin ba ko kuma a iya banbance kowane ba, musamman ma bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wajen a matsayin wurin tarihi na duniya, hakan ya sa kuma ake shan baƙar wahala wajen haƙo wurin.
Masu binciken kayan tarihi sun dawo a farkon wannan shekarar kuma sun fara bincike.

Asalin hoton, OMOKOLADE OMIGBULE
Da farko an samu abubuwan da basu da alaƙa da binciken da ake da suka haɗa da robobi, waɗanda dole a jefar da su nan take. Sai kuma daga bisani wani ɗalibi wanda ya kammala jami'a, kuma ɗan Najeriya, Omokolade Omigbule, ya haƙo wani dutsi da Farfesa DeCorse ya bayyana da wani ɓangare na katangar ginin da ake nema.
"Abin mamaki ne matuka da ɗaure kai, ganin sawun wani gini na ainahi da aka rufe ƙarƙashin wani katafaren gini," in ji ɗalibin Jami'ar Virginia.
"Ganin shatin sawun waɗannan dakaru a Afrika, da kuma kasancewa cikin masu wannan bincike, ya sanya na riƙa jin kamar ina wajen lokacin da lamarin ya faru shekaru ɗari da suka gabata.
A yayin da aka ci gaba da binciken, an gano katangar ginin wajen mai tsawon mita shida, tsawon ƙafa 20, an ga ƙofa, da tubalin ginin da kuma ginin magudanan ruwa da akayi da jan bulo.
Dukkan waɗannan kayan tarihin da aka gano suna da alaƙa ne da turawan ingilishi, wato an samar da su tun kafin ƴan Netherlands su ƙwace wurin.

Farfesa DeCorse, ya ci gaba da fitar da kayan tarihin, inda ya fitar da wata ruɓaɓɓar bindiga mai tsatsa, wadda ya ce ana amfani da ita a Ingila a farkon ƙarni na 17.
Game da ƙananan bututun shan taba da aka gani kuwa, Farfesan ya ce " Waɗannan abubuwan suna da alaƙa da lokacin da muke magana akai, saboda a wancan lokacin taba sigari bata da wahalar samu saboda arharta."
Farfesa DeCorse ya ƙarƙare tattaunawar da cewa " Ƙashin Akuya da aka gano kuwa, na nuna yadda turawan suka riƙa cin naman dabbobi a matsayin hanyar samun sinadarin protein, duk da wajen yana kusa da teku da zasu iya samun kifi cikin sauƙi."
Binciken irin wannan abun sha'awa ne da burgewa. Kowane ɓangare yana buƙatar bincike da tambayoyi da ƙarin bayani.
A wani ɓangaren kuma, za a iya cewa, masu binciken yanzu suka soma, saboda za su kwashe shekaru uku masu zuwa kafin su iya fitar da ainahin gaba ɗaya ginin wajen mai ɗinbin tarihi na Fort Kormantine, wanda zai ƙara fitar da haƙiƙanin mahimmancin wajen.











