Isra'ila za ta bayar da damar shigar da kayan agaji Gaza

Turmutsutsu wajen neman agajin abinci

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 4

Isra'ila ta ce za ta bude hanya domin bayar da dama ga ayarin Majalisar Dinkin Duniya ya shiga Gaza domin raba kayan agaji da magani, bayan makonni na matsin lamba na duniya da gargadin fadawar al'ummar zirin yanayi na bala'in yunwa.

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ranar Asabar, ta ce ta bayar damar komawa jefa kayan agajin ta jiragen sama – abin da aka ce bai wadatar ba, baya ga hadarin da ke tattare da shi.

Isra'ila ta yi wannan sanarwa ne bayan matsin lamba da take sha daga hukumomi da kasashen duniya – cewa al'ummar Falasdinawa da ke yankin za su fada cikin mummunan bala'in yunwa – bayan da Isra'ilar ta takaita shigar da kayan agajin da magunguna tsawon watanni ga al'ummar yankin su miliyan biyu.

Isra'ilar dai ta musanta abin da ta kira ikirarin haddasa yunwa ga al'ummar ta Gaza da gangan.

Rundunar sojin Isra'ilar ta ce ta fara aiwatar da wasu jerin matakai na inganta kai agajin a yankunan da ke da tarin jama'a.

Haka kuma ta ce ta koma samar da wutar lantarki a yankin – da ta ce za ta amfani mutum dubu dari tara.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kafofin Falasdinawa suna tabbatar da ci gaba da aikin jefa kayan agajin ta sama, a yankin arewacin Gaza.

Tun daga farkon watan Maris ne Isra'ila ta dakatar da bayar da dukkanin kayan agajin, amma ta bayar da damar bayarwa amma da sababbin sharuda a watan Mayu.

Isra'ilar tare da Amurka, ta bar kungiyar da suka samar ta Gaza Humanitarin Foundation ta yi aikin rabon a yankin.

A yayin aikin wannan kungiya kusan kullum an rika bayar da rahoton harbe Falasdinawa a yayin da suke turmutsutsun karbar kayan.

Shedu sun tabbatar wa da BBC cewa sojojin Isra'ila ne ke bude wa Falasdinawan wuta a yayin rabon.

Amma kuma Isra'ila ta ce sojojinta na harbin gargadi ne kawai tare da karyata yawan jama'ar da ke mutuwa a lokacin.

Ta kuma zargi Hamas da haddasa hatsaniya a kusa da inda ake rabon kayan.

Kungiyoyin agaji da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kawayen Isra'ila sun dora alhaki a kan Isra'ilar kan bala'in karancin abincin a Gaza, inda suke kira da a bayar da damar shigar da kayan da raba su ba tare da wani tarnaki ba.

Ita kwa ma'aikatar lafiya da Hamas ke tafiyarwa ta ce gomman mutane ne ke mutuwa saboda rashin abinci.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ranar Asabar ma'aikatar lafiyar ta ce a cikin 'yan kwanakin da suka gabata mutum 125 da suka hada da kananan yara 85 suka mutu.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana lamarin da cewa mutum ne ya haddasa shi.

Rundunar sojin Isra'ila a wata sanarwa da ta fitar ta ce Majalisar Dinkin Duniya ce da kungiyoyin agaji na duniya ke da alhakin aikin rabon kayan agaji tare da kira, su tabbatar bai kai ga 'yan Hamas ba.

Sassaucin da Isra'ilar ta yi a ranar Asabar ya biyo bayan amincewar da ta yi ga shirin kasar Jordan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, shirin da ya samu goyon bayan Birtaniya – na jefa kayan agajin daga jiragen sama.

To amma kuma hukumomin agaji sun ce , hakan ba zai wadatar ba ko alama wajen kawar da yunwar da al'ummar ta Gaza ke ciki.

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai taimaka wa Falasdinawa 'yan gudun hijira Philippe Lazzarini, ya ce aikin jefa kayan ta sama na da tsada kuma ba zai wadatar ba.

Bugu da kari ya ce lamarin zai iya hallaka fararen hula da ke cikin bala'in yunwa, idan ba a bari sun yi yadda ya kamata a yi shi ba.

Lazzarini ya ce hukumarsa tana da abin da ya kai manyan motoci dubu shida, da ke dauke da kayan agaji a Jordan da Masar wadanda suke jira su shiga Gaza.

Ya kuma yi kira ga Isra'ila da ta dage haramcin shigar da ta yi tare da bayar da tabbacin shigarsu ba tare da wani hadari ba, da kuma bari sur aba kayan ga mutanen da ke cikin matukar bukata.

Isra'ila ta kaddamar da yakin na Gaza ne bayan da harin ba-zata da Hamas ta kai kudancinta ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 – wanda a lokacin aka kashe kusan mutum 1,200 da kuma garkuwa da 251.

Tun daga sannan Isra'ilar ta kashe sama da Falasdinawa dubu 59 a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta yankin ta sanar.