'Shekara biyu bayan harin Hamas, babu tabbacin ɗana yana raye'

- Marubuci, Alice Cuddy
- Aiko rahoto daga, Tel Aviv
- Lokacin karatu: Minti 4
Mahaifiyar wani mutum da Hamas ta yi garkuwa da shi a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ta ce ba ta da tabbacin ko har yanzu ɗan ta yana raye, amma tana da yaƙinin cewa daftarin zaman lafiya na shugaba Trump zai kai ga nasarar sako dukkan mutanen daHamas ta yi garkuwa da su..
Herut Nimrodi ta shaidawa BBC cewa tana fargabar ɗanta Tamir ya mutu, amma tana ci gaba da jiran abin da zai faru shekara biyu bayanyin garkuwa da shi.
Ta ce shi kaɗai ne har yanzu hukumomi ba su bai wa danginsa bayanin ko yana da rai ko kuma ya mutu ba.
An fara tattauna wani daftarin zaman lafiya da shugaba Trump ya gabatar, wanda ya bayar da damar ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, daga ranar Talata domin cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da kuma sako waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su.
"Suna ƙoƙarin ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya, amma an daɗe ana wannan ƙoƙari. Sai dai wannan karon akwia banbancin yanayi,'' in ji Ms Nimrodi. "muna fatan wannan karon za a kaiga nasara., wannan ya zamo sasanci na ƙarshe."
Ta ƙara da cewa ''yana da muhimmanci sosai yadda aka gindaya sharaɗin saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, masu rai da kuma gawar waɗanda suka mutu," she said.
"Mun ƙosa a sako mutanen da Hamas ke tsare da su, yana da muhimmanci sosai mu gane halin da suke ciki. A haka dai babu wani tabbacin ko suna raye."
Tamir na cikin mutane 47 da har yanzu suke a hannun Hamas, daga cikin waɗanda ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma ana sa ran har yanzu 20 a cikin su suna raye.

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT
Ganin ƙarshe da ta yiwa ɗan nata, wani bidiyo ne aka wallafa a shafukan sada zumunta a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ke nuna mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Ta ce "A lokacin ƙaramar ɗiyata mai shekara 14 ta garzayo tana ihu, tana cewa ta ga an yi garkuwa da ɗan uwanta, a wani bidiyo a da ta gani a Instagram,''
"Na ga Tamir sanye da doguwar riga. Ko takalmi babu a ƙafarsa, kuma babu gilashinsa duk da cewa baya iya gani sosai idan babu su. Yana cikin ɗimuwa sosai.''
"Daga bidiyo da na gani, shi kaɗai ne bai ma san abin da ke faruwa ba. Ya tsinci kansa ne kawai a cikin mummunan hali.''
Kamar sauran iyalan da aka kashe ƴan uwansu, ko aka yi garkuwa da su, Ms Nimbrodi ta shaida wa BBC cewa rayuwarta ta shiga mawuyacin hali cikin shekaru biyun nan.
"Mutane na tambaya ta, shekara biyu kenan... ya kike ji, ya kike samun natsuwa? Ni kuwa ina ce masu rayuwa ta matuƙar canzawa, komai ya canza mani.'' in ji Ms Nimbrodi.
Isra'ila na ganin ranar da wannan hari ya faru shekaru biyu baya a matsayi rana mafi muni a tarihinta, inda aka kashe mutane 1,200, kuma Hamas ta yi garkuwa da wasu 251.
Harin ya tunzura yaƙin Gaza, inda dakarun Isra'ila suka kashe mutane fiye da 67,000. Haka nan kuma yaƙin ya tilastawa kusan dukkan jama'ar Gaza barin muhallin su.

Asalin hoton, Family handout
Ms Nimrodi ta ce tana gidanta a kusa da Tel Aviv a ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da Tamir ya tura mata sako cewa Tamir ya tura mata saƙo cewa ana luguden rokoki kan gidajen su, a kan iyakar Gaza.
Ms Nimrodi ta bi sahun dubban mutane ciki harda iyalan wadanda Hamas ke tsare da su wajen gudanar da taruka da addu'oi da kuma alhinin halin da yan uwan nasu ke ciki.










