Ɗan Isra'ila da ya kuɓuta daga Hamas na fargabar kasa dakatar da yaƙin Gaza

Eli Sharabi na fargaba game da sabon daftarin zaman lafiya da shugaban Amurka ya gabatar- amma yana da ƙwarin gwiwa game da kwanaki masu zuwa
Bayanan hoto, Eli Sharabi na fargaba game da sabon daftarin zaman lafiya da shugaban Amurka ya gabatar- amma yana da ƙwarin gwiwa game da kwanaki masu zuwa
    • Marubuci, Lucy Manning
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wani ɗan Isra'ila da Hamas da taɓa garkuwa da shi, wanda kuma ƙungiyar ta kashe mata da 'ya'yansa a harin ranar 7 ga watan Oktoba, ya ce "yana fargaba" rushewar daftarin tsagaita wuta tsakanin Hamas ɗin da Isra'ila.

Cikin wata hira da bai saba yi ba, Eli Sharabi, wanda Hamas ta sace yayin harin na 2023, ya ce rayukan sauran mutum 20 da suka rage a raye a hannun Hamas na cikin haɗari saboda hare-haren Isra'ila.

Ya nemi shugaban Amurka Donald Trump ya "kammala aikinsa" wajen tabbatar da sauran mutanen sun kuɓuta daga hannun masu garkuwar.

Ya nemi Hamas ta amince da daftarin "domin jama'arsu...da kuma Gabas ta Tsakiya...saboda yaƙi bala'i ne ga duka ɓangarorin biyu".

"Ya kamata mu ci gaba da fata na gari" cewa za a cimma matsaya," in ji shi.

Daftarin mai ayoyi 20 wanda Trump da Netanyahu suka amince da shi, ya nemi dakatar da yaƙin nan take da kuma sakin dukkan Isra'ilawan da ake tsare da su cikin awa 72, inda Isra'ilar za ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa.

Zuwa yanzu mahukuntan Hamas sun nuna cewa ba za su amince da tayin ba.

Har yanzu Hamas na riƙe da gawar ɗan'uwan Sharabi mai suna Yossi, da kuma abokinsa Alon Ohel mai shekara 24, waɗanda suke tsare a cikin hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke Gaza.

Mista Sharabi na neman shugaban Amurka ya tabbata an kuɓutar da sauran Isra'ilawan da ke hannun Hamas
Bayanan hoto, Mista Sharabi na neman shugaban Amurka ya tabbata an kuɓutar da sauran Isra'ilawan da ke hannun Hamas

Kuɓuta daga hannun Hamas

Bayan shafe kwana 491 a hannun Hamas, sai a ranar da za a saki Mista Sharabi (a watan Fabrairun 2025) sannan ya san cewa an harbe matarsa Lianne da 'ya'yansa mata Noiya da Yahel bayan sun ɗauke shi.

Kusan mutum 1,200 mayaƙan Hamas suka kashe yayin harin bayan sun tsallaka iyaka, sannan suka yi garkuwa da wasu 251.

Yayin da ake shirin bikin cika shekara biyu da aukuwar harin, Mista Sharabi mai shekara 53 ya faɗa wa BBC irin halin da ya shiga da kuma ƙoƙarin sake gina rayuwarsa.

Lokacin da aka kawo harin, Sharabi da iyalinsa sun ɓuya na tsawon sa'o'i a cikin ɗaki a gidansu da ke kusa da Zirin Gaza. An kashe mazauna unguwar tasu ta Kibbutz Be'eri da yawa yayin harin.

Yayin da aka fara harbe-harbe, shi da matarsa Lianne sun lulluɓe 'ya'yan nasu.

Ɓaraguzan wani gida kenan bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a unguwar Kibbutz Be'eri

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

Bayanan hoto, Ɓaraguzan wani gida kenan bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a unguwar Kibbutz Be'eri
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce sun faɗa wa maharan cewa Lianne da yaran 'yan Birtaniya ne, amma duk da haka suka fito da shi daga gidan.

"Na fahimci cewa garkuwa ake son yi da ni a lokacin. Sai kawai na juya na faɗa wa iyalina cewa 'zan dawo' - kuma wannan ne lokaci na ƙarshe da na gan su."

Mista Sharabi ya bayyana yadda aka kai shi wani masallaci da farko.

"An rufe min ido, amma ina jin manya da yara na ƙoƙarin kashe ni da hannunsu, suna jifa na da takalmi lokacin da nake kwance a ƙasa."

Ya ce kusan duka watannin 16 da ya yi a hannun Hamas, hannaye da ƙafafuwansa a ɗaure suke da igiya, kafin a sauya su da ankwa. Raɗaɗin hakan sai da ya sa shi ya suma.

Wata shida na ƙarshe kafin a sake shi, Sharabi ya ce ana ba su abinci sau ɗaya a rana, da kuma rabin burodi.

Sai da ya rage ƙiba da kilogiram 25 zuwa ranar da Hamas ta nuna shi a dandamali kafin sakinsa.

Mako ɗaya kafin lokacin aka faɗa masa cewa za a sake shi. A lokacin aka faɗa masa cewa an kama ƙaninsa ma amma ya mutu saboda harin Isra'ila. Jim kaɗan kafin sakin nasa, ya fara mafarkin zai koma Ingila tare da matarsa da 'ya'yansa kusa da 'yan'uwanta.

Mayaƙan Hamas kenan suke yin holen Mista Sharabi a kan dandamali kafin miƙa shi ga masu shiga tsakani yayin musayar fursunoni

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Mayaƙan Hamas kenan suke yin holen Mista Sharabi a kan dandamali kafin miƙa shi ga masu shiga tsakani yayin musayar fursunoni

Da ranar da za a sake shi ta ƙaraso, Hamas ta gabatar da shi a kan dandamali yayin bikin da aka yaɗa kai-tsaye a talabijin.

Jim kaɗan bayan haka ne kuma murnarsa ta koma ciki.

"Wata jami'ar aikin walwala ta zo ta ce min: 'Mahaifiyarka da 'yar'uwarka na jiran ka. Na ce mata 'Ki kawo min Lianne da 'ya'yana mata'. Sai ta ce min 'Mahaifiyarka da 'yar'uwarka za su yi maka bayani'.

"Na yi kuka na ɗan lokaci, kuma na faɗa wa kai na cewa 'Zan iya ci gaba da kuka, amma ba zai dawo min da Lianne, da Noiya, da Yahel ba."

Iyalin Sharabi kenan a wani hoto - Yahel, Eli, Noiya, da kuma Lianne
Bayanan hoto, Iyalin Sharabi kenan a wani hoto - Yahel, Eli, Noiya, da kuma Lianne

Jana'izar iyali

An gudanar da jana'izar iyalinsa a Isra'ila lokacin da yake hannun Hamas ba tare da sanin halin da suke ciki ba.

Mista Saharabi ya ci gaba da gwagwarmaya tun daga lokacin ta neman a sako sauran mutanen da ya baro a Gaza. Ya gana da Shugaba Trump, inda ya ce ya nemi "ya kammala aikin da ya fara na taimakawa wajen ceto sauran su ma".

Yana ganin Trump ya taimaka sosai wajen sakin sa a musayar fursunoni a watan Fabrairu.

Da BBC ta tambaye shi ko yana da wata fargabar daftarin tsagaita wuta na yanzu zai yi aiki, Sharabi ya ce: "Tabbas ina da fargaba sosai. Kwana biyu da suka muna da ƙwarin gwiwa sosai cewa an kusa nasara, amma kuma ashe ba haka abin yake ba. Ba mamaki akwai abubuwan da ban sani ba, amma zan ji daɗi idan muka ji abin mamaki."

Ya ce daftarin ya zo musu a matsayin "labari mai daɗi", yana mai cewa "kada mutane su cire rai da samun labarin ƙulla yarjejeniya".

A cewarsa: "Kowa ya san idan aka ci gaba da yaƙi za a jefa rayuwar mutanen cikin haɗari. Ni dai ina son duka tsararrun 48 su dawo gida yau ko gobe...Yaƙi bala'i ne, amma bai kamata mu manta wanda ya haddasa shi ba, da mutumin kirki da kuma maras kirki".