Manyan bala'o'i shida da suka faru a Najeriya a 2024

Asalin hoton, FRSC
Kowace shekara da yadda take zuwa dangane da abubuwa na alkairi da kuma na sharri.
Kamar yadda aka samu abubuwa na alkairi a shekara mai ƙarewa, an kuma samu abubuwan bala'i da za a jima ba a manta da su ba a Najeriya.
An samu bala'o'in da suka fi razanar da al'umma da waɗanda suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi a sassan daban-daban na Najeriya.
Wasu daga ciin waɗannan bala'o'i ƙaddara ce daga Ubangiji yayin da wasu kuma ayyukanmu ne ya janyo su.
Mun yi waiwaiye kan wasu da suka fi ɗaukar hankali a ƙasar cikin shekarar 2024.
Sace ɗaliban Kuriga

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 7 ga watan Maris ɗin shekarar ne wasu 'yanbindiga ɗauke da muggan makamai suka auka garin Kuriga da safiyar ranar wata Alhamis, inda suka yi wa makarantar furamare da ƙaramar sakandire ta garin ƙawanya.
Maharan sun kwashe ɗalibai masu yawan gaske a lokacin harin da suka kai garin da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun.
Lamarin ya jafe iyalai da dama a garin - waɗanda suka ce a suna gani lokacin da ake kora ƙanana yaran zuwa cikin daji - cikin halin damuwa da ƙunci.
A lokacin, mutanen garin sun bayyana wa BBC cewa lamarin ya shafi kusan ilahirin gidajen da ke garin.
Wani malamin makarantar da BBC ta yi hira da shi a lokacin ya ce kimanin ɗalibai 287 maharan suka ɗauke a makarantar.
Gabanin wannan hari, wasu maharan sun shiga ƙauyen na Kuriga cikin watan Janairu, inda suka kashe shugaban makaranta tare da sace matarsa.
Ɗaliban sun kwashe fiye da mako biyu a hannun masu garkuwar.
Inda a ranar 24 ga watan shalƙwatar tsaron Najeriya ta sanar da kuɓutar da ɗaliban suu 187.

Asalin hoton, Nigerian Army
Hotunan ɗaliban da aka wallafa bayan kuɓutar da su, ya nuna su cikin galabaita da duk jikinsu ya yi ƙura, tufafin su duka sun yi datti, alamun dai tun da aka sace su ba su ga ruwa ba.
Ruftawar gini ta kashe ɗalibai 22 a Plateau

Asalin hoton, AFP
A ranar Juma'a 12 ga watan Yuli ne aka samu wani wani mummunan bala'in ruftawar ginin wata makaranta a jihar Plateau a daidai lokacin da ɗaliban makarantar ke tsaka da rubuta jarrabawa.
Bayanan da hukumomi suka fitar a lokacin sun ce akwai kimanin ɗalibai 154 a makarantar mai suna Saints Academy da ke birnin Jos.
Bayanai daga jami'an gwamnatin Najeriya na cewa ɗalibai 22 suka mutu a lamarin, kodayake mazauna yankin sun ce yawan waɗanda suka mutu ya kusa 50.
Iyayen yara dai sun ta yin ƙoƙarin ceton yaran nasu ta hanyar amfani da hannayensu da shebir wajen kawar da ɓaraguzan da suka danne su.
Makarantar dai na kusa da wata ƙorama da ta yi ƙasa saboda da zaizayar ƙasa.
Mazauna yankin sun ce masu haƙar ma'adinai sun jima suna sana'arsu a yankin tun kafin kafa makarantar.
'Yan sanda sun ce an samu nasarar kuɓutar da ɗalibai 132 waɗanda aka garzaya da su asibitocin jihar domin samun kulawar likitoci.
Ƙona mutane a masallaci a Kano

A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne aka zargi wani mutum da watsa fetur a cikin wani masallaci sannan ya cinna wuta ya kuma rufe ƙofofin masallacin, a daidai lokacin da kimanin mutume 40 ke gudanar da jam'in sallar asuba.
Mutanen da ke cikin masallacin sun samu ƙuna mai yawa a jikinsu, lamarin da ya sa fiye da mutum 20 suka mutu, bayan kwantar da dama a cikinsu.
Tuni ƴansanda suka kama mutumin da ake zargi da cinna wutar, mai shekara 38 inda ake ci gaba da yi masa shari'a har yanzu a gaban kotu.
Ƴansanda sun ce wanda ake zargin ya tabbatar musu da cewa ya ɗauki matakin ne a wani ɓangare na turka-turkar rabon gado, inda ya ce ya cinna wutar ne kasancewar akwai wasu da yake tunanin sun danne masa hakki a cikin masallacin.
'Fiye da mutum miliyan guda ne suka rasa gidajensu a ambaliyar Maiduguri'

Asalin hoton, Weather monitor
A shekarar 2024 an fuskancin munanan ambaliya ruwa jihohin Najeriya da dama, waɗanda suka zo da asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.
Sai dai ambaliyar da ta shafi birnin Maiduguri a farkon watan Satumba, ta shafe kowane saboda irin muninta.
lamarin ya faru ne sakamakon fashewar babbar madatsar ruwa ta Alau Dam da ke birnin Maiduguri.
Cikin wata hira da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi da BBC, ya ce ambaliyar ta shafi aƙalla mutum miliya biyu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar, NEMA ta ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 37.
A lokacin da lamarin ya faru, hukumomi a jihar sun sanar da rufe dukkan makarantun jihar na tsawon makonni biyu.
Tituna da dama dai sun cika da ruwa wanda hakan ya janyo wahala wajen zirga-zirgar ababen hawa.

Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Facebook da X sun nuna yadda ambaliyar ta mamaye titunan Maiduguri a yayin da jama'a suka hau gadoji domin neman mafaka.
Ambaliyar ta shafi gidan adana namun daji, lamarin da ya sa dabbobi suka fita kan titunan suna gararamba.
Haka kuma ta shafin gidan yarin birnin, lamarin da ya sa gomman fursunoni suka tsare.
Gwamnatin jihar ta buɗe sansanonin 'yangudun hijira aƙalla huɗu domin kula da mutanen.
Mutuwar fiye da mutum 180 a hatsarin tankar a jigawa

Asalin hoton, FRSC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin Oktoba ne kuma aka samu wani mummunan bala'in na hatsarin tankar man fetur a garin Majia da ke jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya.
Gwamnan jihar, Mallam Uma Namadi ya ce adadin mutanen da suka rasu sakamakon hatsarin ya kai mutum 181.
"Tankar man ta taso ne daga Kano za ta tafi Nguru a jihar Yobe lokacin da ta kwace wa direban," in ji Kakakin 'yansandan, DSP Lawan Adam Shiisu.
Babbar jami'ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa'ad ta shaida wa BBC cewa ibtila'in ya faru ne bayan direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.
Hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.
DSP Shiisu, ya ce bayan tankar ta faɗi sai mutane suka yi dafifi a wurin domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami'an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.
Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.
Hatsarin kwale-kwale a Kogi da Neja

Asalin hoton, NEMA
A ƙarshen watan Nuwamabn shekarar ne aka samu wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Hukumomi a Najeriya sun ce kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji fiye da 200.
Cikin wata sanarwa da ofishin gwamnan jihar Kogi ya fitar, ya tabbatar da ceto aƙalla mutum 24, waɗanda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Kwale-kwalen - wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha da ke ci mako-mako a jihar Neja - ɗauke da fasinjoji waɗanda galibi 'yan kasuwa ne da manoma ya nutse a yankin Dambo-Ebuchi na Kogin Neja.
Haka ma a cikin watan Oktoban shekarar aka samu wani mummunan hatsarin kwale-kwale a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke yankin ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja mai makwaɓtaka.
Cikin wata sanarwa da babban darektan hukumar agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ya ce kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.
Lamarin ya faru ne lokacin da kwale-kwalen ke ɗauke da fasinjoji fiye da 300 ya kife, inda kusan 100 daga ciki suka mutu.











