Me ke jawo yawan hatsarin kwale-kwale a Najeriya?

Akan samu asarar rayuka a lokuta da dama na hatsarin kwale-kwale

Asalin hoton, NEMA

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ana ci gaba da aikin ceto mutanen da suka nutse sakamakon hatsarin kwale-kwale a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke yankin ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.

Cikin wata sanarwa da babban darektan hukumar agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ya ce kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da kwale-kwalen ke ɗauke da fasinjoji fiye da 300 ya kife.

Kawo yanzu dai an ceto kusan mutum 150, kuma hukumomi sun ce an ƙara gano gawarwaki 30 bayan18 da aka gano tun da farko yayin da ake ci gaba lalabe.

Hatsarin kwale-kwale dai na neman zama wata babbar barazana a Najeriya, kasancewar a duk lokutan da aka samu hatsarin yakan zo da asarar rayuka masu yawa.

Lamarin da ya sa 'yan ƙasar da dama ke aza ayar tambayar dalilin yawaitar samun hatsarin kwale-kwale a faɗin ƙasar.

Kan haka ne muka duba wasu dalilai da ke haddasa aukuwar hatsarin kwale-kwale a Najeriya.

Abu huɗu da ke kawo hatsarin kwale-kwale

Galibi akan samu asarar rai

Asalin hoton, Getty Images

Bashir Idris Garga daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) mai lura da shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, ya ce dalilan da ke haddasa yawaitar haɗuran kwale-kwale a Najeriya suna da yawa, sai dai ya ce wasu daga cikinsu sun haɗa da:

  • Lodin mutane fiye da ƙima
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jami'in hukumar ta NEMA ya ce babban dalilin da ke haddasa yawaitar hatsarin kwale-kwale a Najeriya ba ya rasa nasaba da irin ƙazamin lodin da ake yi wa jiragen.

''Sannan kuma za ka ga galibi mutane sun zauna an yi balbela a kan wannan kwale-kwale ba tare da sanya rigunan kariya da za su iya hana nutsewa ko da jirgin ya kife ba'', in ji shi.

Masana da dama dai na kokawa kan rashin bin ƙa'ida a lokacin yi wa jiragen ruwan lodi, wanda kuma hakan ne ke haddasa shigar mutanen fiye da ƙima a lokacin lodin.

  • Lodin kaya fiye da ƙima

Bashir Garga ya kuma ce wani abu da ke haddasa yawaitar hatsuran kwale-kwalen shi ne yadda ake maƙare jiragen da lodin kayayyaki.

''Ana labta wa waɗannan jiragen ruwa lodin kayayyakin da suka wuce kima'', in ji Bashir Garga.

A lokuta da dama an ga yadda ake samun hatsuran kwale-kwalen da ke ɗauke da kayayyaki kamar buhuna musamman na 'yan kasuwar da ke zuwa cin kasuwa.

  • Rashin ingancin kwale-kwale

Haka kuma akwai matsalar rashin ingancin kwale-kwalen waɗanda galibinsu ba a bin ƙa'idar ingancin wajen ƙera ƙwale-kwalen.

''Galibi waɗannan jiragen da ake amfani da su ba su da inji, in ma masu injin ne to za ta tarar da cewa sun tsufa'', kamar yadda Bashir Garga ya yi ƙarin haske.

  • Rashin ƙwarewar masu tuƙa kwale-kwalen

Shi ma wannan batu na daga cikin manyan matsalolin da ke haifar da hatsarin jiragen ruwa a Najeriya.

''Yawanci waɗannan matuƙa kwale-kwale ba su da ƙwarewar da za su tuƙa kwale-kwale a rafukan ƙasarmu'', in ji jami'in na hukumar NEMA.

Galibi dai dama ana zargin cewa masu tuƙa kwale-kwalen ba sa halartar wata makarantar koyar da aikin tuƙa kwale-kwalen, yawancinsu kawai tashi suka yi suka koya kuma suke aikin, ba tare da samun amincewar hukumomi ba.

Wasu dabbobi

Asalin hoton, Getty Images

Lokuta biyar na hatsarin kwale-kwale a Najeriya

..

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jama'a ke cika kwale-kwale a lokutan tafiya

An samu lokutan da aka fuskanci mummunan hatsarin kwale-kwale a Najeriya da ya tayar da hankala a ƙasar.

Mun kuma yi bitar wasu daga cikinsu.

Satumban 2024: Nutsewar mutum fiye da 40 a Zamfara

A ranar 14 ga watan Satumban 2024 ne aka samun mummunan hatsarin kwale-kwale, wanda ya yi sanadin nutsewar fiye da mutum 40 a garin Gummi na jihar Zamfara.

Ya ƙara da cewa galibi waɗanda ke cikin jirgin manoma ne da ke ƙoƙarin tsallaka kogin domin zuwa gonakinsu.

Daga baya hukumomin jihar sun tabbatar da mutuwar da dama daga cikin fasinjojin.

Satumban 2024: Kifewar kwale-kwale a Bukkuyum

A dai cikin watan na Satumban 2023 aka sake samun wani hatsarin kwale-kwalen a ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar ta Zamfara.

Kwale-kwalen dai na ɗauke da fasinjoji aƙalla 20 yayin da a lokacin aka bayar da rahoton mutuwar aƙalla mutum huɗu.

Mutanen da ke cikin jirgin dai galibinsu manoma ne da ke kan hanyar zuwa gonakinsu.

Agustan 2024: Nutsewar fiye da mutum 20 a Jigawa

A watan Agustan 2024 wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji fiye da 20 ya kife yayin da yake ƙoƙarin tsallake kogin Gamoda a kusa da ƙauyen Nahuce a yankin ƙaramar hukumar Taura.

A lokacin hatsarin, kakakin rundunar 'yansandan jihar DSP Lawan Shiisu ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda a lokacin ya ce an gano gawarwakin mutum biyar.

Yunin 2023: Sama da mutum 100 sun mutu a Kwara

A watan Yunin 2023 ne kuma aka samu wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 106 a jihar Kwara.

Mutum 300 ne ke cikin jirgin wanda ya taso daga jihar Neja zuwa Kwara bayan wani bikin aure, lokacin da hatsarin ya faru.

Galibin waɗanda suka mutu a lokacin hatsarin 'yan'uwan juna ne.

Oktoba 2023: Mutuwar mutum 23 a Kebbi

A farkon watan Oktoban 2023 ne aka samu wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Yauri ta jihar Kebbi, da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 23.

A lokacin hatsarin an ruwaito cewa mutane da dama ne kuma suka ɓata.

Waɗanda lamarin ya shafa sun kasance ƴan kasuwa da suka fito daga jihar Neja zuwa Yauri domin cin kasuwa, ta mako-mako.

Mece ce mafita?

Ma'aikatan NEMA

Asalin hoton, NEMA

Jami'an na hukumar NEMA ya kuma zayyana wasu matakai da yake ganin idan an bi su to za a rage ko ma a kawo ƙarshen matsalar.

Makatan sun haɗa da:

  • Samar da hukumar kula da sufurin kwale-kwale: ''Yana da kyau a samar da wata hukuma ta musamman da za ta riƙa lura da irin jigilar mutane da ake yi a kwale-kwale'', in ji shi. Yana mai cewa ta hanyar hakan hukumar za ta riƙa sanya idanu tare da lura da irin tarin matsalolin da ke haifar da hatsarin tare da ɗaukar matakai.
  • Tabbatar da ingancin kwale-kwale: ''Yana kuma da kyau a riƙa tabbatar da ingancin kwale-kwalen da ke jigilar mutane a cikin rafukan ƙasar nan'', in ji Bashir Garga. Ya ƙara da cewa yin hakan zai sa a kauce wa amfani da jiragen da suka tsufa ko aka gano suna da wata matsala.
  • Jami'ai su tabbatar da bin doka da oda: Bashir Garga ya ce akwai 'yansanda da ke lura da kai komon da ake samu a rafukan ƙasar, don haka akwai buƙatar waɗanan jami'an su matsa ƙaimi wajen tabbatar da bin dokoki. ''Yana dai kyau su yi tsayin daka wajen tabbatar da cewa ana bin doka da oda'', in ji shi.
  • Shirya tarukan bita: Jami'in na NEMA ya kuma ce akwai tarukan bita da hukumarsu ke shiryawa da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi don duba yadda za a ɓullo wa wannan matsala.
  • Gina tituna a yankunan karkara: To sai dai masana na ƙara mafita ta biyar da gina tituna a yankunan karkara wanda alhaki ne da ke wuyan gwamnatocin tarayya da jihohi da ma na ƙananan hukumomi.