Har yanzu ambaliyar Maiduguri na hana ni barci - Ma'aikacin BBC

Asalin hoton, BBC/Imam
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Maiduguri
- Lokacin karatu: Minti 12
Ma'aikacin BBC Imam Saleh ya samu shiga can cikin wuraren da ambaliyar Maiduguri ta fi shafa.
A cikin wannan muƙala ya bayar da labarin irin uƙuba da tashin hankalin da mutane suka shiga, sai dai wataƙila wasu abubuwan da za ku iya karantawa a wannan labari na iya tayar maku da hankali.
A yayin da nake rubuta wannan labari a cikin jirgin sama kan hanyata ta komawa Abuja daga Maiduguri, cike nake da tausayi da alhini da jimamin abubuwan da har abada ba zan manta da su ba.
Mutanen Maiduguri sun fuskanci uƙubar da a tarihi ba su taɓa ganin irinta ba, domin rabon da a samu ambaliya gama-gari irin wannan tun 1994, waccan din ma ba ta ko kama kafar wannan ba.
Ƙaddara kanka zaune a saman rufin gida tsawon kwana uku kwana huɗu babu ci babu sha saboda kana fargabar sakkowa saboda ruwa ya mamaye gidanka gabas da yamma kudu da arewa, kana tsoron kada ka sakko ruwa ya cinye ka.
Ƙaddara kanki a matsayin mahaifiyar da ta saka jaririyarta a roba ta ɗora a ka kamar mai talla, domin tana tsoron kada ruwa ya tafi da jaririyarta.
Ƙaddara kanka, ko kanki, a matsayin wadda dole ta tursasawa barin tafiya ta bar mijinta a gida sabili da ba za ta iya cetonsa ba, don haka sai ta zabi ta ceci ƴaƴansu masu ƙarancin shekaru.
Ƙaddara kanka a matsayin ɗan uwan waɗanda rashin tsira da ransu ya sa yunwa ko rashin lafiya ya kashe a cikin gidajensu, gawarwakinsu suka kumbura suka fashe har suna wari a cikin gari.
Da idona na ga mahaifiyar da bayan mun ceto ta daga cikin ruwan da ya kusa cinyeta, da ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka, aka tambayeta dalili, ta ce ta mance jaririyarta ƴar wata daya da take shayarwa a baya, haka aka barta ta sake komawa cikin wannan ruwa tana tafiya har ta ɓace, ba mu sake ganinta ba.
Watau a zahirin gaskiya abun ya wuce intaha, ban taɓa ganin wani bala'i makamancin wannan ba.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da farko dai na bar Abuja ranar Laraba 11 ga watan Satumban 2024, domin in je in aiko wa Sashen Hausa na BBC rahoton bala'in da ya faru, kwana guda bayan dam din Allo ya ɓalle, ruwa ya shiga gari ya mamaye gidajen jama'a.
Ina zuwa Maiduguri, tun daga sararin Subhana nake hango ruwa ya mamaye ƙasa, na leko ta tagar jirgi domin tabbatar da abun da idona ke gani, Maidugurin da na sani a baya ta tafi, tun daga sama mutum na iya ganin rabinta ruwa ya cinye, ba ka iya hango komai sai ɗaiɗaikun gidajen da, da alama na bene ne da ba su wuce ka ƙirga da yatsun hannunka ba, tun daga sama, a raina nake faɗi lallai bala’in ya kai ya kawo.
Ina sauka a filin jirgin sama na tarar babu sadarwar Intanet, don haka ba za ka iya yin kira ko aika saƙo ba. Ga shi kuma babu motocin da za su wuce da mu irin wuraren da ambaliyar ta shafa.
Tsit kake ji a filin jirgin saman, in banda ni da sauran fasinjojin da muka sauka, sai kuma ma’aikatan filin jirgin na Maiduguri da ke ta zirga-zirga, don haka shiga gari zai zama ƙalubale a garemu, ga shi filin jirgin babu mota kowa ya kama gabansa.

Da ƙyar da siɗin goshi dai na samu wata mota da ta kai ni unguwar Gwange, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa, inda nan na tarar da ikon Allah, na kalli gabas da yamma, kudu da arewa, ruwa kawai kake gani babu ƙarshensa.
Yawancin gidaje sun nutse, kana iya ganin ruwan ya karya ƙofofin gidaje, wani gidan taga ta faɗo, kai ka ce an yi shekaru aru-aru ba a rayuwa a waɗannan gidaje, domin sun zama kufai.
A gefe guda kuma ga mata da ƙananan yara na ta ƙoƙarin ganin sun ceci rayukansu.
Wasu sun ɗauko kayansu a ka, wasu sun ɗauro ƴaƴansu a wuya, saboda idan a ƙasa suke ruwan zai shanye su, ga motoci da dama sun nutse.
Za ka ga tsaleleliyar mota ta gani ta faɗa, amma ruwa ya shanye ta, mai ita ya haƙura ya tafi ya barta a wajen, tun da kamar yadda Hausawa kan ce abun duniya nan ake barinsa.
Akwai wata mata da na yi kiciɓis da ita tana tafiya tana kiran sunan ɗanta da ta nema ta rasa, alhalin sun baro gida tare, suna ƙoƙarin zuwa sansanin masu neman mafaka.
Mutane da dama suka rika fada wa kwalbatocin kan titi suna nutsewa saboda ruwa ya shafe hanyar gaba ɗaya ba ma ka iya gane inda ramuka, ko kwalbatoci suke.
Ko da naga ruwan ba mai shiguwa ba ne, sai na ciro kyamara na riƙa ɗaukar hotuna da bidiyon yadda lamura suke a wurin, inda daga nan na kama hanyar isa sansanin ƴan gudun hijira na Bakassi, wanda shi ne mafi girma, da aka tara sama da masu neman mafaka dubu 200 a iya nan kaɗai.
Rayuwa a sansanin masu neman mafaka na Bakassi

Tun kafin isa ƙofar shiga sansanin masu neman mafaka na Bakassi na hango mutane na daka wawa ana turmushe wasu, mata da yara tsaye a gefe, yayin da su kuwa maza ƙarfafa ke ta kokawa.
Ban fahimici abun da ya sa ba har sai da na ƙarasa wurin, ashe abinci ne wata mata ta kawo na jinƙai, don taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa. Wasu da na yi magana da su a wajen sun shaida ma ni cewa duk lokacin da aka kawo abinci tun daga bakin ƙofar shiga yake ƙarewa, domin duk da akwai jami’an tsaro a wajen haka mutane za su daka masa wawa kowa ya kwashi nasa.
Shigata ke da wuya mutane da dama suka yunƙuro kaina suna roƙon in ba su abinci.
Wata dattijuwa mai sama da shekara saba’in ta tunkaro ni ta ce: ‘’Babana yau kwana na biyu, ban ci abinci ba, yunwa nake ji, zan mutu, don Allah ka taimaka mani’’
Wasu daga cikin matan da suka kewaye ni, na riƙe da jarirai a hannunsu suna ta kukan yunwa, iyayensu ko da hawaye sharaf-sharaf a fuska - yara na kukan yunwa iyaye na kukan yunwa, amma ga iyayen, nasu kukan ko shakka babu har da na baƙin cikin ganin sun kasa ciyar da waɗannan jarirai da ƴaƴan nasu.
Ni da na je a matsayin ɗan jarida sai zuciyata ta karaya, ganin irin wahalar da mutane ke ciki.
Wasu sun shaida mani cewa babu ruwa babu abinci a wannan wuri, haka suke zaune kwana da kwanaki babu ci babu sha, kuma ƴan uwansu da suke wasu wuraren ba su san inda suke ba ballantana su zo su same su, su kawo musu agajin abnci, ga shi kuma wasunsu da dama ba su ma san inda wayoyinsu suke ba, sun fadi lokacin da suke ƙoƙarin ceton ransu.
Wata uwar ƴaƴa uku da na tarar tana shayar da ɗaya daga cikin ƴaƴanta, ta shaida mani cewa kwananta uku ba ta ci abinci a sansanin ba, kuma haka take shayar da ɗan, inda a cikin raina na ce to idan ba ta ci abinci har tsawon wannan kwanaki ba to me take shayar da shi ?
Na yi magana da da yawa daga cikinsu, amma kalma ɗaya dukkansu ke fitowa daga bakinsu, abinci..abinci...abinci.
Tun daga ƙarfe shida har zuwa takwas da rabi na dare ina wannan sansani inda na bayar da rahoto kai tsaye a shirinmu na rediyo, kafin daga bisani na bar wurin, na koma masaukina.
Sai dai kash, yadda na ga rana haka na ga dare domin ban iya barci ba, abubuwan da na gani su suka yi ta dawo mani har gari ya waye, ashe ban ma ga komai ba tukunna.

Asalin hoton, BBC/Imam
Kashegari ƙarfe biyar da rabi na safe na saɓi jakata na kama hanyar gidan gwamnatin jihar Borno, inda aka tsara zan bi gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ta tawagar shugabannin tsaro domin shiga wuraren da ambaliyar ta shafa ƙafa da ƙafa mu ga halin da ake ciki.
Ko da na isa gidan gwamnati da duku-dukun safiya, sai na tarar da Gwamna Zulum zaune da jami'an gwamnati ana haramar tafiya, ga kayan abinci an ƙuƙƙulla a leda ana zubawa a wasu dogayen motocin sojoji waɗanda ruwa ba ya iya yi masu lahani.
Misalin ƙarfe bakwai da kwata muka kama hanyar shiga unguwannin Abbaganaram, da Kwastam (Custom), da 505, da Goni Kachallari, da Muna, wuraren da lamarin ya fi ta'adi.
A wannan rana na ga musibu iri-iri da ban taɓa gani ba a rayuwata - gawarwaki ne kawai kake gani a saman ruwa suna yawo, wasu kuwa mutane ne ke ɗakko su a wuya domin a fitar da su, to amma fitarwar ma wani babban akiki ne domin ruwa ne da ba ka hango ƙarshensa.
Na ga wata uwa da ta sako jaririyarta a roba ta ɗora a kanta kamar mai talla, domin kada ruwa ya janye ta, wa ma yake batun dabbobi, irinsu awaki da shanu waɗanda kana tafiya ma za ka ci karo da su a gabanka suna yawo.
Ko da muka isa unguwar 505 sai muka ji wari ya cika hanya, ashe na gawarwakin waɗanda suka mutu ne har sun ruɓe, sun kumbura sun fashe - akwai wani gida da aka nuna min a tsakiyar ruwa aka ce akwai marar lafiyar da aka tafi aka bari saboda ba za a iya cetonsa ba, don haka ya mutu har gawarsa ta lalace.
Wani mutumi da muka ci karo da shi ya keto ruwan tun daga unguwar Muna, ya tare tawagarmu ya fashe da kuka, yana faɗin mutane na can suna mutuwa, saboda yunwa.
Duk inda muka ratsa mutane ne cirko-cirko sun fice daga gidajensu, wasu suna cikin ruwa tsamo-tsamo.
Mun wuce kasuwanni da makarantu da hukumomin gwamnati waɗanda ruwa ya shafe su baki ɗaya.
Na ga babban gidan ajiyar namun dajin Maiduguri wanda shi ma ruwa ya mamaye shi, wani jami'in gwamnati da muke tare da shi a wannan tawaga yake shaida mani cewa kusan kashi 90 cikin ɗari na namun dajin da ke wannan gida sun fice sun shiga gari, kuma ana kyautata zaton kadoji na nan kwance a ƙarƙashin ruwa, don haka masu ƙoƙarin tsira a kafa na cikin haɗari.
Gaba kaɗan muka ci karo da babban kurkukun Maiduguri, wanda kwana guda kafin na isa ruwa ya shiga ya rusa wata katangarsa, har ta kai sama da fursunoni 200 sun arce.
Daga cikin waɗanda suka tsere kamar yadda mahukuntan jihar suka shaida mani har da mayaƙan Boko Haram da ke ajiye a wannan gidan yari.

Asalin hoton, BBC/Imam
Wani abun sosa zuciya da na yi ta gani shi ne mutanen da har kawo wannan lokaci suna ci gaba da kasancewa a irin waɗannan wurare domin ba a kai ga ceto su ba, don haka babu yadda za su yi sai dai su zauna su rayu cikin yunwa da ƙishirwa, domin babu ma wuraren sayar da abinci ko shaguna ko kasuwanni ko wani wuri da za ka ga ana sayar da abinci ma, don haka sai dai su zauna haka nan da yunwa.
Kamar yadda na faɗa tun da farko mun taho da abinci cikin tawagar gwamnatin jihar Borno, sai dai zancen gaskiya shi ne ko kadan wannan abinci bai isa ba.
Tun ma kafin mu nausa sosai cikin waɗannan unguwanni abincin ya ƙare.
Mutane suka yi ta tare motocinmu duk da na sojoji ne suna daka masu wawa suna kwashe abinci, ba su ma bari an raba shi bisa tsari ba, don haka ko da muka ƙarasa sosai cikin unguwannin da abun ya shafa sai ya zamana babu abincin da za a ba su, don haka sai motocin da muka shiga da su suka zama na ceton rai, inda muka rika ceto mata da ƙananan yara muna zuba su a motocin, domin ceton rayukansu.

Sai dai hatta a wannan yanayi, na ga gwarzantakar maza da dama, musamman waɗanda suka duƙufa wajen jefa rayukansu cikin haɗari domin ceton na matansu da ƴaƴansu.
Za ka ga namiji ya riƙo hannun matansa da ƴaƴansa ya kawo su gaban motocinmu ya ce a taimaka a cece su, shi zai haƙura ya zauna har sai ya ga abun da hali ya yi.
Kwasar mutane kawai muke yi, babu ɗaukar suna ko bayanai, ballantana a sanar da su inda za su je su samu yan uwansu - haka nan ido rufe kowa ke son ganin an ɗauki wanda ya kawo, ya yi imanin cewa da zarar an fita daga cikin wannan ruwa, to a wajensa babu sauran matsala, domin zai tsira da ransa.
Sai da muka cika motocinmu maƙil da mutane, duk da dama akwai mutane da muka shigo da su, haka muka kama hanya motarmu na tangaɗi muka fita.
Muna kokarin fita ruwa mai ƙarfi ya tsuge, haka ya jikamu jagaf, kasancewar rufi a saman motar, muna kyarma dai muka gagganɗa muka kama hanya.
Sai dai tsallakawarmu ke da wuya aka ji ɗaya daga cikin matan nan da muka ceto ta fashe da kuka, wani daga cikin jami'an tsaron da muke tare da su ya tambaye ta dalilinta na kuka, sai ta ce ta mance jaririyarta ƴar wata ɗaya da take shayarwa ne a baya, ka ji fa!, a lokacin ne ta dawo hayyacinta, ta tuna cewa ta bar ƴarta a baya.
Lamarin ya shafi mutane miliyan biyu - Zulum

Bayan mun fita daga wuraren da matsalar ta shafa kai tsaye muka wuce fadar gwamnatin jihar Borno, inda aka tsara zan yi hira da gwamnan jihar Babagana Umara Zulum.
Na gan shi a yanayin da ban taɓa ganinshi ba, cike da ɓacin rai da kuma jimamin abun da ya faru, da babban birnin jiharsa - haka aka kafa kyamara muka fara tattauanwa.
Tambayar da na fara masa ita ce ''Mai girma gwamna me za ka ce kan wannan abun da ya faru'?'
Ya shaida mani cewa duk abun da ya faru iko ne na Ubangiji, don haka sun karɓa da hannu bibbiyu sun ɗauki ƙaddara, sannan gwamnatinsa za ta tunkari matsalar iya ƙarfinta.
Wani abu da ya fito daga hirar da na yi da shi da ya zama babban labari shi ne na adadin waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamna Zulum ya shaida mani cewa akalla mutane miliyan biyu ambaliyar ta shafa, yana fadin haka na sake tambayarsa, ''Mutane miliyan biyu?'' cikin jinjina maganr, ya kada baki ya sake jaddada abun da ya fada.
Ya shaida mani cewa bayan komai ya wuce, gwamnatinsa za ta kafa kwamiti domin duba irin ɓarnar da ta auku da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin sake inganta rayuwar jama'ar da abun ya shafa.
Hakazalika ya shaida mani cewa gwamnatinsa na yin iya ƙoƙarinta wajen ganin ta sama wa waɗanda ke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira abinci da dukkan abun da suke buƙata.

A yanzu haka na koma Abuja, munanan abubuwan da na gani har yanzu sun tsaya mani a rai, bacci ya zama wani abu mai wahala a gareni, duk sa'ad da na kwanta sai in riƙa ganin gawarwaki na yawo a saman ruwa, sai in rika tuno da matar da ta mance jaririyarta da irin yadda gawarwakin mutanen da suka mutu ke wari cikin unguwanni da sauran munanan abubuwuan da na gani.
To amma babban abun da ke cikin raina shi ne me ya sa aka gaza ɗaukar mataki tun da farko, duk da cewa an sanar da gwamnatin jihar Borno, lokacin da aka lura dam din Allo zai iya yin ambaliya?
Gwamna Babagana Zulum ya ce lokacin da ya samu wannan labari ya tura tawaga ta musamman, kuma ta je ta duba wannan kogi, masu kula da shi sun tabbatar masu cewa babu wata matsala.
Matsala dai ta riga ta faru, sai dai akwai babban jan aiki a gaba, ko shakka babu ruwa kam zai wuce, sai dai maganar ita ce yadda za a sake gina Maiduguri ta koma kamar yadda take a baya, kasuwanni da makarantu da asibitoci su farfado su dawo kamar yadda suke.
Akwai kuma babban ƙalubale na kiyaye bazuwar cututtuka musamman na kwalara wadda tuni masana lafiya sun fara gargaɗin za a iya samun ɓarkewarta musamman a sansanonin masu neman mafaka.
Bayan komai ya wuce, mutane za su je su tarar da gidajensu wasu sun lalace, hanyoyi da titunan sun farfashe, kuma dagwalon wannan ambaliya zai iya zama babban sanadin haifar da yaduwar cututtuka a tsakanin jama'a.
Akwai buƙatar gwamnatin jihar Borno da kuma gwamnatin Najeriya su yi wani tsari na musamman da za su tunkari waɗannan matsaloli don magance su.











