Ko ya dace Amurka ta kora masu laifi 'yan wasu ƙasashen zuwa Afirka?

Wani jirgin sojin saman Amurka a titin jirgi. Ana iya ganin gaban jirgin mai launin toka da injina biyu ta fukafukinsa na hagu da wasu ma'aikatan jirgin sanye da kaya launin lemo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi amfani da jiragen soji wajen mayar da yan ci-rani daga Amurka har da Honduras a Janairu
    • Marubuci, Priya Sippy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gwamnatin Amurka ta mayar da nahiyar Afirka a matsayin masaukin yan ci-ranin da aka tuso keyarsu wadanda ta ce an same su da aikata laifi.

Yayin da aka kwashi da dama zuwa kasashen tsakiya da kudancin Amurka a Yuli, maza 12 daga kasashe har da Mexico da Mynamar da Yemen an tura su Eswatini da Sudan ta Kudu. An mayar da wani dan Sudan ta Kudu zuwa kasarsa ta asali.

Rahotanni na cewa Amurka na kokarin shawo kan sauran kasashen Afirka su karbi mutanen, wadanda kasashensu na asali ba za su karbe su ba, a cewar hukumomin Amurka.

Shirin korar baki na Shugaba Donald Trump ya samu goyon baya a lokacin da yake yakin neman zabe bara. Sai dai masu kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniyta da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun kadu da abin da ya faru inda suka ce tura mutanen zuwa kasashen da ba sune asalinsu ba na iya zama take dokokin kasa da kasa.

Shin ya halatta a tasa keyar baki zuwa ƙasashen da ba nasu ba a dokar ƙasa da ƙasa?

Ana iya kallon mayar da yan ci-rani zuwa kasashen da ba nasu ba a matsayin yana bisa doka - amma hakan tana kasancewa ne karkashin wasu sharudda.

"Ya kamata a kalli gaba daya batun mayar da baki zuwa wasu kasashen ta fuskar samun mafaka," in ji Farfesa Ray Brescia daga makarantar nazarin karatun lauya ta Albany da ke Amurka,

"Akwai wani tsari a dokokin duniya na kin tura mutum kasarsa ta asali idan hakan zai zama barazana a gare shi, a don haka sai a zabi wata kasar ta kasance zabi," in ji shi.

Tsarin ba wai kawai ya shafi kasashen baki na asali bane amma har da kasashen da za a iya tura su.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan zuwa kasar ba zai tabbatar da tsaron mutum ba, korar na iya cin karo da dokokin kasa da kasa - kamar yadda Kotun Kolin Birtaniya ta hana yunkurin gwamnatin kasar na tura masu neman mafaka zuwa Rwanda a 2023.

Dole yan ci-rani su samu damar kalubalantar korarsu idan wajen da za a tura su zam kasance mai hadari a gare su, duba da hujjoji daga majiyoyi masu tushe kamar rahotanni daga Majalisar Dinkin Duniya ko binciken ma'aikatar harkokin wajen Amurka. Ana sa ran kotuna su yi nazari na tsanaki kan hadarin.

"Ya kamata wadannan kotunan su duba matsayin da bakin suke da shi a shari'ance, idan za a tsare su da kuma irin masaukin da za a samar masu," in ji Dr Alice Edwards, manzo ta musamman ga Majalisar Dinkin Duniya kan azabratrwa da sauran matsaloli na cin zarafi.

Amma galibin baki suna fama wajen samun goyon bayan shari'a kan lokaci.

"Sai an yi namijin kokari wajen samun lauyan da zai dauki mataki da hanzari," in ji Farfesa Brescia.

"Ba kowane zai samu wannan dama ta sharia ba."

Shin korar baƙi zuwa Eswatini da Sudan ta Kudu ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa?

"Tabbas sun saba ta fuska biyu," in ji Farfesa David Super daga jami'ar Georgetown.

"Babu wata hujja da ke nuna Amurka ta bai wa mutane dama ta biyu ta kalubalantar korarsu, kuma ba su da izinin tura mutane kasashen da za su iya fuskantar muzgunawa."

"Akwai shakku game da tsarin kare hakkin bil adama a Sudan ta Kudu da Eswatini," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Lokacin da aka fara tura baki zuwa Sudan ta kudu a Mayu, an shigar da kara a wata kotun Amurka bayan da ma jirginsu ya tashi.

Alkalin ya yanke cewa kokarin tusa keyar mutanen ya saba umarninsa cewa dole ne a bai wa baki damar kalubalantar kai su wasu kasashen da ba nasu na asali ba.

An sauye akalar jirgin zuwa Djibouti da ke gabar gabashin Afirka inda rahotanni suka ce ake tsare da mutanen cikin wata kwantenar jirgi yayin da ake sauraromn shari'ar.

An tura karar zuwa Kotun Koli wadda ta ba da damar a ci gaba da korarsu amma ba ta bayyana ko Sudan ta Kudu wuri ne mai aminci ga bakin ba.

"Abin da muka gani a irin wadannan kararrakin shi ne ana yawan dakile masu damar shari'a a lokacin da suke bukata sannan ana zaman shari'a a lokaci kurarre," in ji Dr Edwards.

"A wannan karar, suna ma kan hanyarsu ta zuwa wani sansanin sojin Amurka kuma hakan babbar matsala ce."

Ta kara da cewa dole kotu ta tsame kanta daga siyasa musamman idan hakkokin bil adama na cikin hadari.

Farfesa Brescia ya yi gargadi cewa hukuncin Kotun Koli na iya kafa misali mai hadari.

"Akwai damuwa sosai cewa hakan zai karfafawa gwamnati gwiwa ta hanzarta kafin mutane su samu damar zuwa kotuna," in ji shi.

Shin Eswatini da Sudan ta Kudu na da tsaro?

Baya ga kin yi masu adalci, ana tura baki zuwa wasu kasashen da ba su da aminci a gare su - lamarin da ya saba da dokokin kasa da kasa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka a yanzu tana ankarar da mutane game da tafiya zuwa Sudan ta Kudu, inda ta ba da misali da laifuka da garkuwa da mutane da rikicin masu rike da makamai. A farkon wannan shekarar, an bayyana kasar, daya daga cikin mafiya talauci a duniya, a matsayin wadda tgake gab da komawa yakin basasa.

"Akwai abubuwan damuwa game da doka da oda a Sudan ta Kudu - kan tashin hankali da rikici da kuma yakin da ake gwabzawa," in ji Dr Edwards.

Wadanda aka tura Sudan ta Kudu, rahotanni sun ce ana tsare da su ne a wata cibiya da ke Juba, babban birnin kasar wadda ta yi kaurin suna kan rashin yanayi mai kyau, a cewar wani dan faftuka Agel Rich Machar.Gwamnati ba ta tabbatar da inda suke ba ko kuma tsawon lokacin da za su kasance a wajen.

A Eswatini da ke kudancin Afirka, jami'ai sun ce bakin na tsare a gidan gyaran hali kuma za a tusa keyarsu tare da taimakon hukumar kula da yangudun hijira ta duniya IOM.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce gidajen yarin Eswatini na fuskantar matsaloli na cunkoso da rashin kewayawar iska da rashin abinci mai gina jiki da kuma cibiyoyin kula da lafiya.

"Ba ma hangen za su tsaya na tsawon lokaci kafin su shiga cikin al'umma ba," in ji kakakin gwamnatin Eswatini Thabile Mdluli kamar yadda ya shaida wa BBC, ba tare da bayar da haske kan tsawon kwanakin da za su yi a kasar ba ko kuma za su fara karasa zaman hukuncin da aka yanke masu.

Gwamnatin Amurka ta ce wadanda aka kora zuwa Eswatini sun aikata miyagun laifuka har da yi wa yara kananan fyade da kisa da kuma cin zarafi ta hanyar lalata.

Ana samun karuwar masu yin suka a Eswatini.

Babbar jam'iyyar adawa mafi girma a kasar, Pudemo ta ce yarjejeniyar da aka yi tsakanin kasashen biyu ta safarar mutane ce da aka yi ta da sunan yarjejeniyar korar mutane".

Dan fafutukar kare dimokradiyya Lucky Lukhele ya ce bai kamata kasar ta zama wajen watsar da masu laifi ba".

Ko da an saba dokokin kasa da kasa, Farfesa Super ya ce ba lalle bane Amurka ta fuskanci hukunci saboda ba ta amince da kotunan duniya da dama ba.

"Da alama wannan ya shafi hani, aika sako cewa idan ka zo Amurka, za ka fuskanci tsangwama," in ji shi.

Ba tare da la'akari da tsarin doka ba, korar baki zuwa wasu kasashen da ba nasu na asali ba na jefa masu rauni cikin wani yanayi mara dadi bisa karancin goyon baya ko kuma matsayin shari'a, in ji Dr Edwards.

Ta jaddada cewa masu kare hakkin bil adama ba wai suna kokarin hana korar baki ba ne - suna yin haka ne a wuraren da suka lura ana take hakkokin bil adama.

A 2017, Isra'ila ta tura dubban baki daga Afirka zuwa Rwanda da Uganda a karkashin wani tsari. Wani binciken BBC daga bisani ya gano cewa an wulakanta da yawa a cikinsu bayan da suka isa kasashen.

Wane tagomashi ƙasashen da ke karɓar korarrun ke samu?

Bayanan yarjejeniyar korar baki har yanzu batu ne na sirri.

Ms Mdluli ta shaida wa BBC cewa dalilan Eswatini na karbar bakin da aka kora abu ne da ba a da bayanansu zuwa yanzu."

Sai dai, gwamnatocin Eswatini da Sudan ta Kudu sun bayyana alakarsu mai karfi tsakaninsu da Amurka a matsayin dalilin karbar bakin.

Farfesa Brescia ta nuna wasu kasashen na iya jin tsoron mataki daga Amurka idan suka ki amincewa kamar tsaurara dokokin bayar da biza ko lafta masu haraji.

A Afrilu, Amurka ta ce za ta janye dukkan takardun biza da ta bai wa yan Sudan ta Kudu idan ta ki amincewa da korarrun mutane.

Babu bayani kan ko hakan ya sauya a yanzu da ta karbi korarrun daga Amurka.

Danfafutuka Machar ya ce Sudan ta Kudu ta amince da yarjejeniyar saboda tana son Amurka ta janye takunkuman da ta kakaba wa mataimakin shugaban kasa, Benjamin Bol Mel.

Gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumi kan Bol Mel a 2021 saboda zargin rashawa kuma ta sabunta su a wannan shekarar.

A Yuli, Semaya K.Kumba, ministan harkokin waje na Sudan ta Kudu ya gana da tawagar kakaba takunkumi da kare yancin bil adama a ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Sai dai kasashe kamar Najeriya sun nuna ja.

"Muna da matsalolin kanmu da dama," in ji ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar a watan Yuli, inda ya yi fatali da bukatar karbar tsararru yan Venezuela.

Dr Edwards ta bayyana cewa wadannan yarjeniyoyi na zuwa ne da tagomashi.

"A baya, tsare-tsaren tura mutanen kasashen da ba nasu ba, ana bayar da makudan kudade da hadin kan soji da tsaro cikin tsarin," in ji ta.

A watan Maris, rahotanni sun ce gwamnatin Trump za ta biya El Salvador dala milioyan 6 domin ta karbi yan Venezuela da aka kora.