Ɓarnar da sauyin yanayi ke haifarwa a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
A yayin da duniya baki ɗaya ke fama da matsalolin sauyi da ɗumamar yanayi, ƙasashe masu tasowa a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka ma na ta fama da illolin da wannan sauyi ke jawo musu.
Bala’o’i kamar ambaliyar ruwa da fari da mahaukaciyar guguwa da girgizar kasa da kuma gobarar daji na ci gaba da afkuwa sakamakon sauyin yanayi, inda kasashen da sauyin yafi shafa ke son a biya su diyya na tsawon shekaru don ganin an rage musu raɗaɗi.
Manyan matsaloli biyu da Najeriya ba ta fuskanta zuwa yanzu su ne mahaukaciyar guguwa da girgizar ƙasa gobarar daji.
A makon da ya gabata ne aka yi taron sauyin yanayi karo na 27 a Masar wato COP27, don gano bakin zaren yadda za a shawo kan lamarin.
Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka shaida ɓarnar sauyin yanayi a baya-bayan nan. Sai dai ƙwararru na kukan cewa akwai buƙatar faɗaɗa wayar da kai don daƙile irin bala’o’in da hakan ka iya haifarwa.
Mutum miliyan ɗaya da rabi sun tsere daga gidajensu

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu wasu na ganin maganar sauyin yanayi ba gaskiya ba ce, duk da yadda hasashen masana da ƙwararru kan kimiyya ke ƙara zama gaskiya game da bala'in da ke tattare da hakan.
Alƙaluma na baya-bayan na da hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta fitar sun nuna cewa mutum aƙalla miliyan 3.2 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya.
Kazalika, 612 sun rasa rayukansu yayin da miliyan 1.4 suka rasa muhallansu a jihohin ƙasar 34 cikin 36.
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce miliyan 4.1 daga cikin mutanen da lamarin ya shafa na fuskantar ƙarancin abinci, da kuma yara 'yan ƙasa da shekara biyar miliyan 1.74 da aka yi hasashen za su fuskanci tsananin yunwar abinci mai gina jiki.
"Mutum 14,000 ne suka kamu da cutar kwalara a jihohin Borno da Adamawa da Yobe tun daga watan Janairu, inda ta kashe mutum 443," a cewar rahoton da MDD ta fitar ranar Juma'a 11 ga watan Nuwamba.
Wani sabon rahoto da haɗakar masu bincike 100 da kuma masu ruwa da tsaki a a duniya suka fitar kan asara da kuma illolin sauyin yanayi, ya nuna cewa ƙasashe kusan 55 sun samu asara ko ko-ma baya na tattalin arziki da ya kai sama da dala biliyan 500 tsakanin shekarar 2000 da 2020.
Kuma hakan zai iya ƙaruwa zuwa wata biliyan 500 a shekara 10 masu zuwa.
Ƙafewar koguna da ke jawo ƙaura, rikicin manoma da makiyaya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wani hannun kuma, sauyin yanayin da ke sa koguna su yi ambaliya, shi ne dai ke jawo ƙafewarsu, abin da ke haifar da ƙarancin ruwa na sha da kuma noma.
Shekara kamar 40 da suka gabata, Tafikin Chadi na da tsawon fiye da murabba'in kilomita 40,000, sai dai ya zuwa 2016 yana da abin da bai wuce 1,300 ba, kamar yadda wata maƙala ta bayyana a shafin Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta Najeriya ta bayyana.
Yayin da lamarin ke ƙara ta'azzara sakamakon ɗumamar duniya da kuma ƙaruwar Sahara ta gefe kudancin tafkin, gonaki da kuma ƙauyukan da ke kusa da shi na kasancewa kufai sakamakon yawan hamadar da ke lulluɓe su.
Hakan ya jawo mutane da dama na yin ƙaura don neman ƙasar da za su yi noma daga arewa maso gabashin Najeriya zuwa tsakiyar ƙasar - kamar jihohin Filato da Taraba.
Kazalika, yawaitar hamada na tilasta wa Fulani da sauran makiyaya yin ƙaura zuwa jihohin na tsakiyar Najeriya da suka haɗa da Binuwai da Filato da Kogi da Kwara da Neja da Nasarawa.
An yi imanin cewa hakan na jawo ƙaruwar rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Ga mazauna birane a arewacin Najeriya kamar Kano, suna sane da yadda rijiyoyi ke daina kawo ruwa a 'yan shekarun nan da zarar damuna ta ɗauke. Duk da cewa wasu na alaƙanta hakan da yawan haƙa rijiyar burtsatse ko borehole a turance, yana dai da alaƙa da raguwar ruwan da aka saba samu.
Raguwar wutar lantarki

Asalin hoton, Nigeria Ministry of Water Resources
Najeriya ce ƙasa mafi girman tattalin arziki da kuma yawan jama'a a Afirka, wadda kuma ke da ma'adanai daban-daban musamman a ɓangaren mai da iskar gas.
Tashoshin samar da wutar lantarki uku cikin shida da Najeriya ke amfani da su na amfani da ruwa, inda sauran ukun ke amfani da makamashin fetur ko iskar gas.
Tashoshin uku da ke amfani da ruwa su ne na Jebba, da Kainji, da Shiroro - dukkansu a Jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.
Fari da ƙarancin ruwan sama da ake fuskanta a wasu lokuta, haɗi da ɗumamar yanayi, na cikin abubuwan da ke haifar wa ɓangaren lantarki cikas
Hakan na nufin duk lokacin da aka samu raguwar ruwa a kogunan da ke juya injin samar da lantarki a Neja, ita ma lantarkin da Najeriya ke samu za ta ragu - musamman a yankin arewaci.
"Ɓangaren makamashi da lalata dazuka da kuma sauyi wajen amfani da albarkatun ƙasa na cikin manyan abubuwan da sa Najeriya na fitar da iskar da ke gurɓata muhalli," a cewar hukumar agaji ta gwamnatin Amurka (USAID) cikin wani rahoto.
Babban ƙudiri na 20230
A 2013 gwamnatin Najeriya ta amince da wani shiri mai taken National Policy on Climate Change don daƙile fitar da hayaƙi mai gurɓata muhalli.
Haka nan, a 2015 Shugaba Muhammdu Buhari ya saka hannu kan Yarjejeniyar Paris kuma ya ƙaddamar da shirin ƙasa da zimmar rage gurɓataccen hayaƙi da kashi 45 cikin 100 zuwa 2030.
Kafin haka, a 2012 Najeriya ta shiga yarjejeniyar raɗin-kai ta MDD mai taken UN Environment’s Climate and Clean Air Coalition don rage gurɓatacciyar iska a manyan ɓangarori 10.
"Sai dai kuma, tana fuskantar ƙalubale wajen aiwatar da ƙudire-ƙudire kan sauyin yanayi da suka shafi ƙona iskar gas, da amfani da gas wajen samar da lanatarki, da sufuri, da yin noma na zamani da kuma sake farfaɗo da dazuka," in ji USAID.
Ƙasashen Turai munafukai ne game da sauyin yanayi - Buhari

Asalin hoton, State Hosue
Duk da cewa bai halarci taron COP7 ba, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tura wakilci ta hannun Ministan Muhalli Mohammed H. Abdullahi.
Sai dai da alama ba duka saƙon da yake son isarwa a wurin taron wakilin nasa ya bayyana ba domin kuwa cikin wata maƙala da ya rubuta wa jaridar Washington Post, Buhari ya siffanta ƙasashen Yamma 'munafukai" saboda gazawarsu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi.
"Da yawa daga cikin takwarorina [shugabannin ƙasa] na nuna damuwa game da munafurcin ƙasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa ɗaukar matakin da ya dace," a cewarsa.
Shugaban ya jaddada cewa shugabannin Turai sun sha nuna gazawa wajen cika alƙawarin samar da dala biliyan 100 don shawo kan "matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu" ga ƙasashe masu tasowa.
Ya ƙara da cewa daga yanzu ba zai yiwu ƙasashen Turai su dinga tsara yadda ya kamata ƙasashen Afirka za su yi amfani da ma'adanan da suke da su ba.
"Kar ku faɗa wa 'yan Afirka yadda ya kamata su yi amfani da arzikinsu. Da a ce Afirka za ta yi amfani da dukkan arzikin iskar gas da take da shi a rumbuna, wanda shi ne mafi inganci ga muhalli, hayaƙin da ke gurɓata yanayin duniya zai tashi daga kashi 3 cikin 100 zuwa 3.5."
Afirka na fitar da kashi kusan uku ne kacal na hayaƙi mai gurɓata muhalli a duniya baki ɗaya amma tana cikin nahiyoyin da suka fi kowace fuskantar bala'in sauyin yanayin.











